← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 52

Sashe 38

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Meyasa mahaifinku ya yanke wannan hukunci? Me Nayla tayi masa haka?. Ko dan ta tafi Kano ne ya saka ya yanke wannan hukuncin?." Jawad ya ce, "itama bata da mutunci ai Mama, ban da rashin hankali da shirme meye na barin gida a akan wannan maganar? Na rantse da Allah in ta dawo sai na zaɓa mata kamanni."

Mama ta ce, "bara naje na samu Abiy ɗin naku naji dalilin sa na aikata wannan ɗanyen aiki." Yaya ya ce, "Yauwa Mama, in da hali a kira yaron kawai ya sake ta tunda daman bai san anyi auren ba. In yaso ni a bani Nayla mu koma Lagos ta koma zama a gidana, nayi alqawari zan kula da ita babu wata damuwa irin wannan da zata sake kunno kai." Mama ta girgiza kai ta hau sama da sauri wajan Abiy. Sallar magriba ta samu yana yi sai ta zauna tana zaman jiran ya idar suyi magana.

Koda ya idar lazimi ya fara ta san kuma baya gamawa sai za a yi i'sha gashi ita ta ƙagu tayi magana dashi. Mama ta ce, "Don Allah Abiy ka katse lazumin nan muyi magana. Ta ya za a aurawa Nayla wancan yaron?. Bai kamata a biye mata a aikata abinda take so ba." Ko motsi bai yi ba balle ta saka ran zai bata amsa. Mama ta ce, "Abiy don Allah kace wani abu, ka dakatar da lazumin nan muyi magana don Allah."

Ban ma bai kula ta ba Mama ta zauna tayi tagumi tana kallonsa. Gajiya tayi da zaman ta tashi ta fita shi kam bai ma kalle ta ba. Sai da ya kammala yaji ana kiran sallar i'sha sannan ya tashi ya fito dan zuwa masallaci.

Koda ya dawo a falo ya tarar dasu gabaɗaya da alama zaman jiran sa suke yi. Wucewa yayi ba tare da ya zauna ba suka bishi da kallo ganin ya shiga ciki. Jawad ya ce, "Mama don Allah kije kuyi magana ya bar mu cikin tunani." Mama ta ce, "maganar ce baya so shiyasa ya wuce bai kula mu ba, amma bara na sake zuwa naji" ta faɗa tana hawa saman ta barsu a ƙasa.

Tana zuwa ta same shi ya zauna akan kujera yana kallon tv, ta zauna a kusa dashi ta ce, "abinci fa?." Ya girgiza kai kawai alamun baya ci. Mama ta ce, "maganar dai da baka so ita zanyi Abiy. Meya faru ka yanke wannan hukunci akan Nayla?. Naji bata kyauta ba amma da ka sani baka yi haka ba." Bai ce mata komai ba itama sai tayi shiru bata sake magana ba.

Katse shirun tayi da cewa, "bata kyauta ba abinda tayi na barin gıda, bata kyauta ba maganar da tayi ta ce zata kashe kanta akansa amma Abiy bai kamata ka biye mata ba, Nayla yarinya ce ƙarama bata da hankali har yanzu." Abiy ya kulle ido ya buɗe ya kalli Mama ya ce, "gobe ku shiga kasuwa, duk abinda ake siyawa amarya ku siya mata. Duk abinda za ayi ayi shi a gama ba sai ance za ayi order daga wata ƙasa ba. A siyi komai gobe zuwa ranar Sunday nake so tafi gidan mijinta" yana faɗar hakan ya tashi ya bata waje.

Mama ta ce, "meyasa haka...." Katse ta yayi ta hanyar cewa, "kar ki shigo ki dame ni" yana faɗa ya wuce ɗaki. Mama tayi wani mayaudarin murmushi ta ce, "an gama." Canja yanayinta tayi ta sakko ƙasa wajan su Yaya da Jawad suka bita da kallo ganin yanayinta ya nuna musu alamun rashin nasara. Ta kalle su ta ce, "yace gobe na shiga kasuwa na siyawa Nayla duk abinda ake siya na aure, wai zuwa jibi zata tare." Yaya ya ce, "Mama sai kika ce masa me?" Ya faɗa kamar zai yi kuka.

Mama ta ce, "bai bani damar magana ba, ya kuma kalle ni yace kar na dame shi ya shiga ɗaki ya bar ni a falo." Jawad ya ce, "wai me yake damun Abiy ne har haka? Me Nayla tayi masa da ya canja lokaci guda don Allah?."
"Bata kyauta ba Jawad, abinda tayi ba tarbiyyar da ya baku bace gabaɗaya. Amma shima yayi gagagwar yanke hukunci, Nayla yarinya ce ƴar ƙarama ba babba ba."

Yaya ya ce, "kome tayi ai bata cancanci haka ba, irin wannan aure kamar bata da gata kawai an ɗauketa an bashi ba tare da yana so ba? Babu kuɗin aure, babu komai hatta sadaki biya masa aka yi. Ko da yake bai ma sani ba." Mama ta ce, "ka wuce gida dare yayi, in yaso gobe zai kuzo mu ji in zai yi mana magana." Jawad ya ce, "ai wallahi gobe in bata dawo ba da kaina sai naje na dawo da ita, shashasha mara hankali da tunani" ya faɗa yana fita daga falon shima ya bi bayan sa.

Mama shiga ɗaki ta ɗauki waya ta saka a kunne kafin ta ce, "Yauwa, in zaka iya ka sake hacking account ɗinta na WhatsApp ka sake turawa Abiy saƙo. In zai yu zan turo maka irin abinda da zaka tura masa yanzun nan." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta ce, "karka damu, na tura maka kuɗin ka harda na data ka ƙara." Yanke wayar tayi tana kallon wani wajan daban tana ɗan dukan wayar da hannunta.

Murmushi tayi ta ce, "kwanciyar hankalina shine auren nan ya tabbata, babu ta yadda za ayi na bari a warware shi tunda an riga da an ɗaura. Yadda ban ji daɗi zaman gidan nan ba, yadda Bilkisu ta wahalar dani a rayuwar gidan nan Nayla ma sai ta ɗanɗana irin abinda na ɗanɗana. Muje dai zuwa" ta faɗa tana yanke wayar ta shiga banɗaki zuciyarta fes take dan ta san ta zama silar aurawa Nayla wanda baza ta taɓa jin daɗin zaman aure dashi ba.

•••••••

      Didi tana barin gidan Kawu gidan su ta wuce ta samu Omar ɗin a zaune ya dawo daga masallaci yana zaune akan kujera ya ɗan zame kansa na bayan kujerar ya ɗora ƙafa kan ɗaya kamar yadda ya saba. Kallon sa take yi ganin yayi mata kyau gashin kansa ya kwanta kamar na jariri, idanunsa a rufe gashin idanunsa sun kwanta a ƙasan idanun.

"Omar Lafiya?" Ta faɗa tana zama daga gefen sa. Buɗe ido yayi ya ce, "Didi! Saukar yaushe?."
"Yanzu na shigo, baka da lafiya ne?."
"Ciwon kai ne yake damuna tun safe."
"Amma ka sha magani?."
"Na sha" ya faɗa yana sake lumshe idanunsa bai ce mata komai ba.

Didi kallonsa take yi tana haɗa kalaman da zatayi amfani dasu wajan sanar dashi abinda ya faru amma ta kasa, ta rasa ta ina zata kamo zaren, ta rasa da wacce kalma zata yi amfani wajan sanar dashi abinda yake zuciyarta akansa. Ajiyar zuciya tayi hakan ya saka ya buɗe ido ya kalleta ya ce "Lafiya dai?." Didi ta kalle shi sai taga idanunsa sun yi ja alamun yana jin ciwon kan sosai ta ce, "ciwon kan ne dai?." Ya ɗaga kai alamun eh.

Lumshe ido tayi ta sake buɗewa tana kallonsa ganin ita yake kallo, ya sauke ƙafa ɗaya ƙasa ya kalleta sosai ya ce, "kar ki damu da kaina na ciwo, ki faɗa min abinda yake faruwa. Naga kin canja alamun damuwa, meye?." Kai ta girgiza ta ce, "Babu komai Omar, Tambayar ka nake so nayi kawai."

"Akan son tambayata kawai kika koma haka?." Kallon sa tayi sai bata amsa ba ya ce, "Ina jinki."
"Omar na isa da kai? Na isa na zaɓa maka abu ka karɓa hannu biyu?." Wani irin kallo yake yi mata na me ya kawo wannan tambayar kafin ya ce, "me ya kawo wannan tambayar? Wani abun ya faru ne?."

"Babu abinda ya faru, ka amsa min tambayata."
"Akwai abinda ya faru, kawai bakya so ki faɗa min ne. Ni kuma Ina so na san meye abinda ya faru kafin na amsa miki."
"Kawai ka amsa min Omar."
"Me zan amsa?" Ya tambaya yana kallonta. Didi ta rausayar da kai ta ce, "na isa da kai? Na isa na zaɓa maka abu ka karɓa?."

Omar ya bita da kallo yana so ya gano dalilin tambayar amma bai gane ba, ya ɗan ɗauke ido yana kallon wani wajan daban kafin ya ce, "kin isa."

Didi ta ce, "Koda matar aure ce? Koda ɗauko mace nayi a yanzu nace maka na saka an ɗaura maka aure da ita zaka karɓa ta?." Omaar ya bita da kallon mamaki ganin ba da wasa take yi kamar yadda ta saba ba, sannan ya ga damuwa a kwance a fuskarta, sannan ya tabbatar da akwai abinda take so ta faɗa masa kafin wannan. Didi ta ce, "ka yi shiru kana kallona." Omar yayi ajiyar zuciya ya ce, "dalilin wannan tambayar nake so naji."

"Ni dai ka amsa min kawai" ta faɗa tana kallon sa. Shiru yayi na wani lokaci yana kallonta kafin ya ce, "eh to, kin isa ki zaɓa min ɗin tunda kece zai karɓa babu yadda zanyi. Amma kin san kin bani ita ne ba dan Inaso ba, kuma zama da wacce bana so bazata taɓa jin daɗin zama dani ba har abada. Kin fi kowa sanin halina, bana son ganin abinda ban saba gani a tare dani ba." Didi gabanta ya yanke ya faɗi tsoro ya mamaye mata zuciya ta ce, "amma zaka iya zama da ita a matsayin matarka dai ko? Babu tsawa, babu tsoratarwa, babu razani, babu harara ko?."

Gyara zama yayi ya shafa kansa zuwa gashin fuskarsa, ya ɗan sosa girar sa da yatsa ɗaya kana ya ce, "gaskiya bazan iya zama da ita matsayin mata ba, zan dai zauna da ita a gida ɗaya matsayin zaɓinki, amma gaskiya ba dai a matata ba."

Kallon sa take yi ta kasa magana dan ya kashe mata baki, ya katse shirun ya ce, "me ya kawo wannan maganar wai? Aure zaki yi min ne?." Jin yana ƙoƙarin gano ta sai ta girgiza kai ta ce, "Kusa hakan, bana son zaman ka kai kaɗai a gidan nan shine nake tunanin zaɓar maka mata na aura maka."
Chapter 38 · 0% Book details