Sashe 49
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yau zaki tare a gidan mijinki wanda kika zaɓa matsayin wanda kike so ki ke ganin zaki iya rayuwa dashi. Duk da auren yazo a bazata a wani yanayi wanda bai miki daɗi ba ina so ki san aure dai sunan sa aure, duk inda akace kalmar miji to mijinki ne biyayya ta zama dole a gareki. Kar ki yi tunanin komai akan auren, kawai ki yi masa biyayya ki nemi aljannaki a gare shi. Ki yi zaman ki a Kano ki yi bautar aure da biyayya ga mijin da ki ka zaɓa matsayin abokin rayuwarki. Bana so na ganki a Kaduna har sai lokacin da nace kizo, ba dan bana son ganinki ko dan kin yi min laifi ba, sai dan inaso ki nutsu ki yi zaman aure. Dan haka babu ke babu zuwa gidan nan matuƙar bani na buƙaci hakan ba. Kin san meye aure, kin san me ake nufi da aure, kin san haƙƙin miji a kanki, kin san naki a kansa. Ki yi biyayya ga mijinki, ban da rashin kunya, ki yi ko yi da halin mahaifiyarki wajan biyayya da kyakykyawan zama. Allah ya bada zaman lafiya. Abinda zan ce miki kenan, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya kai ku lafiya, Allah yasa haka shine alkhairi a gareki."
Kuka Nayla take yi sosai jin kalaman Abiy na kar tazo gida, ta ƙaraso inda yake, ta miƙe akan guiwarta, ta matsa kusa dashi sosai ta ce, "Abiy ban san meyasa ka yanke wannan hukuncin a kaina ba, ban sani me nayi maka ba, ban san meyasa kayi fushi dani har haka ba. Abiy ban san laifin da nayi har kace kar nazo gidan nan sai ka neme ni ba, Abiy gidan da aka haifeni ka yi min iyaka dashi.....!"
Ta kasa ƙarasa maganar saboda kukan da yaci ƙarfinta. Ta sassauta kukan ta ce, "Abiy nidai burina ka yafe min, ka daina fushi dani, kuma ko meye ya faru har ka yanke wannan hukuncin a kaina wallahi ban sani ba, bani da hannu akai dan ban aikata komai ba." Kuka take yi sosai tana durƙushe a gabansa.
Ta kuma cewa, "Bani da mahaifiyar da zata fahimce ni, inda Ummana tana da rai ita zata iya fahimtar abinda nake so ka fahimta Abiy. Abiy tunda nake ban taɓa jin kewar mahaifiyata kamar wannan lokacin ba, ban taɓa jin zafin rashin uwa ba sai a wannan lokacin.....! Ka cike min gurbin uwa da uba, amma a yau ina kewarta, ina tsananin kewarta. Gashi ko fuskarta ban sani ba, a hoto kaɗai nake ganinta, amma kewarta nake ji har cikin rai Abiy.....!" Kuka ya ci ƙarfinta ta kifa kanta a guiwar Abiy tana kuka sosai.
Dukkan su ta basu tausayi, Jalila da take tsaye kuka take yi haka Jidda da Salma da suka fito. Nayla ta ɗago ido yayi kaca-kaca da hawaye ta ce, "Na ɗauki wannan auren a matsayin ƙaddarata kuma jarabawata, jarabawar mahaliccin mu tana zuwa a lokacin da baka yi tunani ba kuma baka yi zato ba. Na ɗauki wannan abun a matsayin haka amma ba dan ina so ba Abiy. Na san na furta maka ina sonsa amma tunda akace na bari na haƙura gabaɗaya, ka tambayi Mama itace take bani ƙarfin guiwa amma na ce mata tunda baka so na haƙura. Ka yi haƙuri Abiy, wallahi ko me ka ke zargina dashi ban yi ba, ko tafiyata Kano ban je dan na ɓata maka rai ko dan ka kasa bani abinda nake so ba" ta faɗa da kuka sosai.
Abiy yayi shiru yana kallon ta, gabadaya kalamanta sun gama sanyaye masa jiki, zuciyarsa tayi rauni tausayin Naylan ya mamaye masa zuciya. Nayla ta kalli su Yaya ta ce, "Yaya da Yaya J wallahi ban yi komai ba, ku daina fushi dani. Kun ji Abiy yace kar nazo gidan nan, ya ce baya so na zo, na zauna a Kano...!" Ta faɗa tana ƙara ƙarfin kukanta wanda yake nuni da kalaman sun dake ta sosai.
Nayla ta gama raunana zuciyar Jawad, ji yake kamar ya zubar mata da hawaye. Ya ta so da hanzari ya ƙaraso inda take ya miƙar da ita sai ta kwanta a jikinsa tana kuka. Shi kansa sai da yayi hawayen tausayinta, ya ɗagota daga jikinsa ya zaunar da ita akan kujera ya kawo mata ruwa da kansa ya bata ta sha tana sauke ajiyar zuciya. Jawad ya ce, "ki daina kuka, ni bana fushi da ke Nayla, ina tare da ke a ko yaushe. Duk abinda ki ke so a ko yaushe ki kira ni ki faɗa min, kuma ko meye ya faru wanda ki ke neman taimako ki sanar dani zan yi miki."
Kai ta ɗaga tana kallonsa ta kalli Abiy da yake kallonta. Kafin tayi magana ya rigata dan in ya bari ta cigaba da magana bai san abinda zai yi ba saboda tausayi da rauni da ƙaunarta da yake ji a zuciyarsa, hakan ya saka ya katseta ya ce, "Ku tashi ku wuce lokaci yana tafiya" ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Nayla ta ce, "Abiy!." Ya kalle ta ba tare da ya amsa ba, sai ta dawo ƙasa ta durƙusa ta ce, "ka yafe min, wataƙila bazan isa Kano da rai ba, wataƙila kuma bazan sake ganinka ba. Ina ji a jikina kamar mutuwa zanyi, don Allah ka yafe min."
Ajiyar zuciya yayi ya kalleta ya ce, "baki yi min laifin komai ba, kuma ni ba fushi nake da ke ba. Zaki je Kano lafiya in sha Allah." Nayla ta ce, "Abiy in na mutu ka yarda a kawo gawata gidan nan? Kar ka ce za a binne ni a Kano don Allah, ina so a kawo maka ni ka yi min wankan gawa da kanka."
"Ya salam!" Abiy ya furta saboda yadda kalamanta suka daki zuciyarsa, kusan irin kalaman da mahaifiyarta ta dinga amfani dasu ne a lokacin da take gab da barin duniya shiyasa kalaman suka dake shi har cikin jininsa. Hannunsa ta riƙe ta ce, "Abiy ka yafe min, ban yi komai ba wallahi. Ina sonka Abiy, bazan iya ɓata maka rai ba, duk abinda ka ce na bari ina barinsa da zuciyata da gangar jikina. Wallahi na bari tunda ka furta baka so, ka daina kallona da wannan laifin don Allah." Abiy da yake kallonta ya yi ajiyar zuciya, ya lura bata cikin hankalinta hakan ya saka ya kalli Yaya da Jawad ya ce, "Ku tashi ku wuce" yana faɗa yana zare hannunsa daga cikin nata ya shige ciki ya barsu a wajan.
Mama ta riƙe Nayla suka fito tana kuka zuwa motar Yaya, duk jikinsu ya yi sanyi har Maman zuciyarta tayi rawa sosai musamman kalaman Nayla na mutuwa. Jalila da su Salma kuwa kuka suke yi sosai, Yaya ma ya kasa magana sai kallon Nayla da yake yi cikin rauni da tsananin ƙauna da tausayinta. A haka aka saka kayanta a booth ɗin motar, Jawad ma ya shiga ta sa motar, Salma da Jidda da Jalila suka shiga mota kuka aka ja mota suka fita daga cikin gidan.
[25/09, 11:34 am] +234 810 686 6659: KRB2P027
ArewaBooks@nanahaleema11
Abiy yana tsaye a balcony yana kallon lokacin da motarsu ta fita daga gidan. Wani irin yanayi yake ji a zuciyarsa mai wahalar fassarawa, sai yanzu yake tuhumar kansa akan meyasa ya yiwa gudun jininsa haka? Meyasa bai sake bata lokaci ba? Shin Nayla ta cancanci wannan hukunci daga gare shi kuwa? Anya bai cutar sa marainiyar Allah ba? Haƙƙinta bazai kama shi ba. Ajiyar zuciya yayi ya kulle ido yana tunani.
_Abiy ni na san wannan ciwo ba na tashi ba ne, ga amanar ƴata Nayla nan na bar maka, ka kula da ita yadda ya kamata. Na san za ka yi koda ban ce ba, amma ina sake maimaitawa ne matsayina na mahaifiyarta. Na san zaka bata tarbiyayya mai kyau, na san Zeenatu zata riƙe min ita hannu biyu ta yi mata tarbiyya tare da su Jidda. Abiy! don Allah kar ka bari Nayla ta yi kukan rashina a tare da ita, kar ka bari ta zubar da hawayen maraici, ka zame mata uwa, ka zamar mata uba, ka zamar mata jigo a rayuwarta._
Ido ya buɗe tunawa da wasiyyar mahaifiyar Nayla, ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Allah ya ba ky zaman lafiya Nayla, Allah ya sa wannan auren ya zama alkhairi a gareki." Barin wajan yayi jikin sa a sanyaye ya rufe balcony ɗin ya dawo falo ya zauna zuciyarsa cike da tunani akan abinda ya faru.
••••••••
Dad kallon Mum yake yi tunda ta dawo daga America bai ji ta ce masa komai akan batun Narma ba, hakan ya saka shi tambayarta a wannan lokaci ya ce, "My dear Ina jiranki, me yake faruwa da Narma a can? Ina fatan komai lafiya dai ko?." Mum ta kalle shi ta ce, "babu lafiya, Narma ta canja kamar ba ita ba, ta rame sosai kamar bata cikin farin ciki."
Da mamaki Dad ya ce, "rashin Lafiya ta yi ta rame?." Mum ta ce, "lafiyarta qalau, kawai ni na ga alama bata jin daɗin zama da Ashraf gabaɗaya. Har yanzu da wannan yaron a zuciyarta, babu Ashraf a rayuwarta yanzu gabaɗaya." Dad ya ce, "wannan masifa har ina? A can ɗin ma bata huta ba?." Mum ta ce, "sannan ka san Narma bata son wahala ko kaɗan, shi kuma Ashraf ya kasa haƙuri da yanayin da take ciki yana raping ɗinta ko yaushe."
Dad ya ce, "wanne irin raping kuma? Mijita ne fa."
"Mijin ta fa, ta ya zai dinga zuwa wajanta ba tare da izini ba? Ai dan yana mijinta ba hakan yana nufin ya dinga amfani da ita duk sanda ya so ba, akwai lokacin da zata ji bata ra'ayi ko da yana ra'ayi sai ya ƙyale ta tunda bata so. Kuma a wannan yanayin da take ciki ni ban ɗauka ma Ashraf zai kai wannan waje ba, na ɗauka zai bata time ya rarrashe ta har ta dawo nutsuwarta sannan sai su yi honeymoon ɗinsu. Amma yanzu ga damuwa, ga wannan tsinannen yaro, ga damuwarsa da me zata ji?."