Sashe 10
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajja ta ce, “nima nayi kewarki Nayla. Amma me yake damunki haka?.” Nayla ta ce, “Hajja na fara aiki fa, in na fita tun safe sai yamma nake dawowa, kin san ba wani abincin kirki na iya ci a waje ba shiyasa na koma haka.” Hajja ta tace, “Mahaifinki ya faɗa min ai zancen aurenki ake yi, yanzu haka ya baki lokaci ki fitar da gwani. Ni na san a cikin gwanayen naki babu Abbas ko?.” Gabanta ya faɗi sosai ta kalli Hajja bayan ta ɓoye damuwarta ta ce, “Hajja ni na barwa Allah zaɓi, duk wanda ya zaɓa min shine daidai da rayuwata. In Yaya Abbas ne Ina maraba dashi.”
Hajja ta ce, “Gaskiya ne. Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi. Ni daman so nake ki yi auren ai, an gama karatu aikin me za a tsaya yi? Me kika nema kika rasa?.” Nayla tayi murmushi kawai kafin ta kalli Didi da take kallon ta. Didi ta ce, “Ashe ƙanwar tawa ta kusa aure babu labari.” Murmushi tayi kawai bata ce komai ba kafin ta ce, “Yau baki yi abincin sadaka bane?.” Didi ta ce, “bani da lafiyar yi ne, da Omar ma yana nan sai ya yi ni bani da wannan ƙarfin gabaɗaya” tana faɗar haka sai hawaye ya sakko mata.
Nayla daman zancen Omar ɗin take so ayi sai ta ce, “Didi meye na kuka?.” Didi ta ce, “Nayla baki san an kama Omar ba?.” Nayla tayi ajiyar zuciya ta kalli Salma kafin ta kalli Didi ta ce, “Salma ta bani labari.”
“To na je har Abuja naga halin da yake ciki Nayla, Omar yana cikin wahala da azabtarwa, dauriya da rashin son sani a damuwa ne ya saka shi ya dake har yake yi min magana kamar ko yaushe. Suna cutar min da Omar kawai dan suna taƙama da mulki baza a iya ja dasu ba, in ba dan haka ba meye laifin Omar? Me ya yi da za a kama shi a ɗaure ba tare da ya yi laifin komai ba?. Laifin Omar ɗaya da yaje gidan, amma da ya je ai ba kisan kai ya je yi ba, ba kuma wani laifi ya aikata musu ba. Kawai saboda bai kai matsayin da suke kai ba, a gare su ƙasƙanci ne ƴarsu ta so Omar. Yanzu zancen asiri suke yi, sun ce asiri ya yi mata take sonsa, ko nazo na karya asirin ko kuma bazan sake ganinsa ba har abada!…..Kashe Omar suke son yi, kashe shi suke son yi kawai!” Ta faɗa da rauni tana hawaye mai taɓa zuciya.
Nayla kuka take yi sosai wanda ya bawa kowa mamaki, sun santa da tausayi sosai kuma tsaf labarin zai iya saka ta kuka. Amma yadda take kuka da zuciyarta da gangar jikinta zaka tabbatar da ba iya kukan tausayi take yi ba akwai wani abun a cikin zuciyarta. Hajja a sanyaye ta ce, “Aisha na ce ki yi haƙuri komai zai zo ƙarshe in sha Allah.” Didi ta ce, “Hajja wallahi mahaifiyar Narma so take a kashe Omaar, yanayin kalamanta kashe shi suke son yi kawai. Sun san in sun kashe shi sun kashe banza tunda bashi da gata, bashi da wani gatan da za a neme shi shiyasa.”
Hajja ta ce, “su Baba Adamu dasu Kawu duk babu wanda zai samu hanyar magana da Sanata?.” Didi ta ce, “Tunda har Daddyn Salma bai samu ba bana tunanin zasu samu. Kuma ni ko faɗa musu ma ban yi ba, ban saba kai damuwata gare su ba na saba ni da Omaar mu ke warware ko meye in ya tunkaro mu. Ban sani ba ko sun ji a gari amma ni ban sanar musu da komai ba.” Hajja ta ce, “ai ya kamata ace sun sani Aisha, iyayen Omar ne fa, ya kamata a sanar dasu ko da addu’a su taya mu.”
Didi ta ce, “Hajja yanzu bana cikin wannan nutsuwar, hankalina baya jikina wallahi.”
Nayla dai kuka take yi har sautin nata kukan yafi na Didi fita, Didi ta kalle ta cikin rauni tace, “ki bar Kuka Nayla, ni ban faɗa miki dan ki yi kuka ba. Ki share hawayenki.” Nayla ta kalli Didi cikin muryar kuka ta ce, “Didi ki yi haƙuri in sha Allah zan yi ko meye ganin na dawo dashi, zan yi duk abinda zanyi dan ganin ya bar hannunsu.”
Didi ta murmusa cikin tsokana da son kawar da damuwa ta ce, “na ɗauka zaki barshi a can kawai, kin manta tsorataki yake yi?.” Nayla bata yi murmushi ba sai ma hawayen da ya sake sakkowa daga idonta ta ce, “Didi ba maganar wasa nake yi ba, zan yi ko meye ganin na dawo da shi.”
Didi tayi murmushi ta ce, “to Nayla. Na gode sosai Allah ya bar zumunci.” Idanu Nayla ta goge ta kulle idanun nata, ita kaɗai ta san raɗaɗin da take ji akan rashin Omar, ita kaɗai ta san azabar da zuciyarta take mata akan Omar. Dole ta san abinda zata yi ta fito da Omar, ko meye shi kuwa zata aikata in dai zai dawo. Zata iya sadaukar da komai dan Omar ya dawo, zata iya rasa komai indai Omar zai fito ta amince.
Ganin tayi shiru sai kowa ya yi shiru Salma da Jidda dai kallon Nayla kawai suke yi cikin tuhuma. Nayla sai ta miƙe ta shiga ɗaki tayi alwala tayi sallar azahar kafin ta dawo falon. Abinci ta tarar suna ci, Hajja ta kalle ta tace, “baza ki ci abincin ba?.” Nayla ta ce, “bana jin yunwa, kaina ciwo yake yi.” Jidda ta ce, “dole kan ki ya yi ciwo, kin zo daga Kaduna ko hutawa baki yi ba kina taho nan, ga kukan da ki ka yi gashi ko abinci baki ci ba, ai dole ki yi ciwon kai.” Hajja ta ce, “Hauwa’u me yasa haka?.”
Kallon Jidda ta yi tace, “Twiny mu je gida” ta faɗa tana ɗaukar mayafinta da yake wajan. Jidda ta ce, “ki ka ce sai anjima zamu tafi.”
“Na fasa, mu tafi yanzu. Salma zaki je bikin ko baza ki ba?.”
“Zan je mana.” Nayla ta ce, “ku zo mu tafi, Hajja sai gobe” abinda ta ce kenan ta fita da hanzari bayan ta ɗauki key ɗin motar Jidda ta fita dashi.
A mazaunin driver ta zauna ganin haka sai suka shiga motar ta ja motar da ƙarfin gaske suka tafi. Gudu take yi sosai ga yanayin gari na juma’a a cushe garin yake da mutane amma haka take gudu kamar zasu bar gari burinta kawai ta je gida. Jidda da take a zaune a gaba ta kalle ta ta ce, “Twiny wai lafiyar ki kuwa? Wannan gudun da ki ke yi na meye?.”
Bata yi magana ba Salma da take baya ta ce, “malama magana ake miki ki rage gudu Ina zamu je? Sai gudu ki ke yi kamar zaki tashi sama.” Daidai nan suka ƙaraso gate ɗin gidan ta dinga danna horn dashi ƙarfi, mai gadi ya buɗe da gaggawa ta shiga da motar ganin motar Abiy tana nan ko parking daidai bata yi ba ta fita daga motar da sauri.
Jidda ta kalli Salma ta ce, “lafiyar ta kuwa?.” Salma tayi tsaki ta ce, “ƙiris ya rage bata saka mun baƙunci lahira ba, ko aure ban yi ba zata kashe ni.” Jidda tayi dariya suka shiga cikin gidan.
A zaune suka same ta a gaban Abiy da yake waya suma suka zauna saboda ya kammala. Kashe wayar ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Mamana lafiya ki ke kuwa? Meye ya same ki haka fuskarki tayi ja haka?." Nayla ta ce, "Abiy ai ka san Didi ko?." Abiy ya ce, "Wacece Didi kuma?."
"Maƙociyar Hajja Yayar...." Kafin ta ƙarasa ya ce, "Oh Yayar ɗan daban nan ko? Na gane ta, da Aisha na santa ni ba wani Didi ba. Mutuwa tayi?."
Nayla gaban taya buga dum jin da sunan da Abiy ya kira Omar dashi, amma bata nuna ba ta ce, "da ranta." Abiy ya ce, "to lafiya ki ka shigo a firgice haka?." Jidda ta ce, "Haka ta dinga gudu damu a titi Abiy, gari ya cushe mutane an dawo daga masallacin juma'a amma bata daina ba, ƙiris ya rage bamu yi hatsari ba." Abiy ya kalli Jidda ya ce, "Wai daman ba Jawad ne ya shigo da mota a guje ba itace?."
"Wallahi itace" ta bashi amsa tana kallon Nayla.
Ya kalli Nayla a nutse ya ce, "Me ya faru haka?." Nayla ta ce, "Tausayin Didi nake ji Abiy, an kama mata ƙaninta sai kuka take yi har da zazzaɓi. Don Allah Abiy ka taimaka a fito dashi don Allah." Abiy ya bita da kallo cikim mamaki ya ce, "akan wannan ne kika kusa kashe kanki da ƴan uwanki?."
"Na kasa sarrafa kaina ne kawai Abiy, bana jin daɗi a zuciyata, Didi tana sona, nima ina son abinda take so." Abiy ya kalle ta a nutse ya ce, "mun yi maganar da Hajja jiya sai dai ba a bani labari duka ba aka kira ni a waya. Waye ya saka aka kama shi ɗin sannan me ya yi?."
Shiru tayi bata amsa ba ya ce, "ke nake saurare, me ya yi aka kama shi har kike so na fito dashi?. Ko wani ya kashe?." Ta girgiza kai alamun a’a ya ce, "to faɗi." Nayla ta ce, "Dama ya je gidan Sen Sagir Sani ne, shine ya saka aka kama shi."
"Me ya je yi gidan? Sata ko kuma kisan kai?." Salma ce ta bawa Abiy labarin abinda ya faru kaf har zuwan Didi wajansa. Abiy ya girgiza kai cikin mamakin ƙarfin halin Omar ya ce, "Barr Narma ya je yace yana so? Kuma yana da hankali?." Salma ta ce, "gashi nan dai akwai Abiy."