← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 52

Sashe 29

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya wara idanu ya ce, “Wai Hajjan nan wacece tawa? Uwata ce ko kakata?. Babu dangi uwa da uba ki dinga saka ni zuwa wajan ta?.” Didi ta ce, “babu ɗaya, amma ta wani ɓangaren tafi dangin uwa da uban, saboda tayi mana abinda si basu yi mana ba a lokacin da muke buƙatar taimako. Bani da wacce nake kallon matsayin uwa da Kaka sai ita, in kai baka kallonta a haka ni a haka nake kallonta.”
“Ke ki ka ga zaki iya” ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba.

Didi tayi dariya tana girgiza kai ta ce, “oh halin ka dai na zafin kai yana nan, Allah ya sauke maka shi ka huta.” Bai ce komai ba sai leda da ya ɗauko a gefen sa yana fito da takalma daga ciki. Didi ta ce, “kai ma sha Allah! Omaar wannan design ɗinku ne?.” Bai yi magana ba ta sake duba takalmin, daga can ƙarshen takalmin wajan dunduniya akwai wani ƙaramin sign da aka rubuta tiger cikin wani rubutu da yake a kwance sai ka kula zaka fahimta.

Didi tayi murmushi ta ce, “kai amma yayi kyau takalmin nan Omar, kamar ba hannu ne yayi shi ba.” Ya kalle ta ya ce, “na ki ne, gana mijinki. Ban san size ɗinsa ba ban sani ba ko zai masa” ya faɗa yana bata. Iri ɗaya ne takalmin banbancin design na maza da mata, amma iri ɗaya ne sak komai da komai. Didi ta ce, “kai amma mun gode. Kuma kaga zaku iya fara siyar da wannan couple design ɗin wallahi za a yi ciniki.”

“Ana yi sosai ma, sai dai ki cigaba da taya mu addu’a” ya faɗa tana kallon ta.
“In sha Allah Omar, addu’a kullum cikin yi maka ita nake. Yanzu ma tunanin sadakar azumi nake yi, ban san ya za a yi ba. Can unguwar mu babu wasu jama’a sosai sannan ban san kowa ba tukunna, nan kuma kai kaɗai ne da ace kayi aure ne sai matarka cigaba da yi, amma zan san abinda zan yi. Yadda Allah ya dafa mana ana cinikin nan dole mu dage da sadaka, Allah ya cigaba da riƙo da hannun mu ya gafartawa iyayen mu.”

Ya amsa da amin kana ya ce, “Ki dai faɗa min in za’ayi kar naji kin bayar da kuɗin da kanki, sadakata ce daman ai.” Tayi dariya ta ce, “tamu dai, ai tare muke yi ba kai kaɗai ba.”

Omar dai bai tanka mata ba ta sake juya takalmin da yayi kyau sosai ta ce, “Amma kuna ɗora a social media ko?.” Omar ya ce, “eh to bana ce ba, ana yi amma ba’a mayar da hankali sosai a kai ba, amma za’ayi.”
“Ya dai kamata wallahi, daman kai alhajin danne-danne in baka ɗora kana talla ba ai danna wayarka bai yi rana ba. Nima a turo min hotuna zan saka a status da kuma Instagram page ɗina. Customers dina na abinci in sun gani zasu siya sosai ma kuwa.”

“To. Bashir ne mai yin hotuna ya iya ɗaukar hoto sosai. Zan tura miki.”
“Wanne suna za a sakawa company?.”
“Ni wallahi ban sani ba, zaɓi.”
“Ga tiger na gani a rubuce, mai zai hana ba za a sakawa company suna Exclusive Footwear by Tiger ba, sannan sai ya zama logo ɗin takalman da hoton Tiger a jiki, amma a canja wannan na jiki.”

Kai ya ɗaga ya ce, “za a yi hakan.”
“Ai gwara, ta yadda duk inda aka ga takalman a san na mu ne. Tunda dai wannan suna na Tiger ya shiga jininka, gwara ma a saka shi yadda kowa zai san naka ne yanzu ka bar rayuwar baya.”

Kai ya ɗaga mata kafin ya ce, “za a yi, amma fa sabon kashe kuɗk ne ni duk na talauce” ya ƙarasa faɗa yana murmushi. Dariya tayi ta ce, “da rarrafe yaro yake fara tafiya, wata ran sai kuɗin sunzo ka rasa me ma zaka yi dasu. Allah ya taimaka ya bada nasara ƙanina.” Murmushi yayi ya ce, “Amin Didi. In sha Allah sai na saka ki farin cikin da baki taɓa yi ba a rayuwarki, zan cika miki dukkan burinki na duniya indai ina da rai.”

Daɗi ya mamaye zuciyar Didi ta ce, “Allah Amin. Ya rabbil alamin ka cikawa ƙanina burinsa, ka bashi ikon neman halak ta hanyar halak.” Murmushi ya sake yi ya amsa da amin bai ce komai ba amma a zuciyarsa yaji daɗin ganinta ya kuma ji daɗin addu’ar da take yi masa.

Kallon falon tayi ta ce, “ɗaɗi da kai baka da lalata waje, sannan kana da ƙoƙarin gyara. Babu laifi dai kawai zance, amma gidan da ƴar ƙura kaɗan, kalli fa tv can.” Omar ya kalli inda ta nuna ya ce, “tunda ki ka bar gidan nan ban taɓa ta ba, kin san bana ƙura ko wajan ma bana kallo.”

Murmushi tayi daman ta san kallo bai dame shi ba, shi dai barshi da ya zauna kawai shi kaɗai hakan yafi masa komai daɗi. Tana ta yabon takalmin kafin tashi ta shiga kitchen tana ji a zuciyarta sana’ar nan da Omaar ya fara zata kai shi inda bai yi tunani ba.
[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P017

Didi tana kitchen tana ta yi amsa mita ya bar ƙwai sun lalace shi dai yana zaune dan shi bai ma duba ba balle ya san akwai wani ƙwai a kitchen ɗin. Gajiya yayi da ya bar wannan, ya lalata wancan da take ta faɗa ya fita. Wayarsa ce tayi ƙara a lokacin ya duba sai ya ga DPO da suka saba dashi ne. Ɗauka yayi suka gaisa yake sanar dashi in yana da dama da lokaci yana son ganinsa, ya amsa masa da zan zo in ya fito daga nan suka yi sallama ya kashe wayar.

Wajan Didi ya koma a lokacin ta fito daga kitchen ta ce, "Komai na kitchen ɗin nan ya la'ance Omar, gas ɗin duk ya yi baƙi saboda baka gyarawa." Ya kalle ta ya ce, "to aikina ne? Ina iya abinda zan iya na bar sauran."
"Yanzu dai ka bayar a siyo kayan miya nayi maka girki."
"To zan aiko dashi, zan fita yanzu amma ba zan jima ba dawo."
"Kar ka manta dai ka bayar a kawo." Da kai ya amsa mata ya fita ita kuma ta koma ciki.

Bashir ya kira a waya yazo ya ɗauke shi a machine suka tafi police station ɗin. Har offfice ɗin dpo suka shiga suka gaisa Omar ya zauna shima Bashir ya zauna yana kallon sa. Dpo ya ce, "Damisa daman na kira ne akan yaran da suka dame mu da faɗace-faɗacen nan na daba da ƙwacen waya da sace-sace. Mutanen gari suna cewa ƴan sanda basa yin komai wajan kama irin waɗanna mutanen, gwamtani ta matsa mana lamba akan mu kawo ire-iren waɗannan ɓata gari da ake nema. Wannan dalilin ya saka na kira ka dan ka taimaka min wajan kama su."

Omar ya ce, "amma kwanaki ka kira ni na tabbatar maka da duk abinda ya shafi wannan ɓangare na fita a ciki, aikin ku ne kama mai laifi ba ni ba, na yi iya abinda zan yi muku a baya amma yanzu babu ruwana a cikin wannan lamari."
"Na sani Damisa, taimako nake so ka yi min wajan bani list na waɗanan ɓata garin da ka sani dan a taimaki al'ummma." Omar ya kalle shi ya ce, "dole sai an haɗa kai da mutanen gari da masu unguwa sannan za a kawo ƙarshen wannan faɗan na cikin unguwa. Ko wacce unguwa a san su waye ɓarayin sun kuma san masu tayar da fitina, wani lokacin masu faɗace-faɗace daban masu sata da ƙwace waya daban, amma da yake su masu faɗan su ake gani da makami duk abinda ya faru kawai su ne. Kowa na unguwa ya san waye ɓarawon unguwa ya san mai faɗan daba, kowa ya san har cikin gidan su amma tsoro sai ya hana a faɗa. Misali kamar ni a baya, kowa ya san ina daga cikin ɓata garin da ku ke nema, amma in zaku kwana kuna tambaya a unguwar babu lallai a faɗa muku saboda ana jin tsoro. Kowa ya san ta inda ɓarna take ɓullowa a unguwanni shiru kawai ake yi, iyayen su kuma in aka zo ana faɗa sai suce su ƙarya ake yiwa yaran su kuma bayan sun san gaskiya. Wannan abinda kake so nayi maka aikin ƴan unguwar da ka ke nema ne, shugaban unguwar zaka je ka samu ya baka list na mutane da ake zargi a wannan ɓangaren."

Dpo ya ce, "Wannan gaskiya ne Damisa, kuma inda ƴan unguwa zasu yi ƙungiya suzo wajan hukuma su faɗi suna da inda waɗannan mutane suke wallahi da sun rage mana aiki. To kowa ya san ɗan iska amma sai a ƙi faɗa, in an faɗa an kama iyaye su shiga radio suna cewa an kama musu yara ba tare da laifin komai ba kuma sun san gaskiya. Yanzu ƙananun yara ake samu da wannan ɗabi'a, wani yaro da aka kama da laifin ƙwacen waya bai fi shekara sha biyar ba. Da aka kama shi mahaifiyarsa zage-zage ta dinga yi mana wai ƙarya ake yiwa ɗanta, da aka tambayi yaron ya amsa a gabanta ya aikata, akace meye dalili ya ce baya cin abinci ya ƙoshi shiyasa yake ƙwacewa ya siyar dan ya ci abinci. Tsakani da Allah wannan ba laifin iyaye bane?."

Omar ya ce, "shiyasa na faɗa maka mafita, kowa ya san na kirki ya san na banza. Manyan unguwa zaka samu a haɗa kai dasu a hukunta duk mai laifi."
Chapter 29 · 0% Book details