Sashe 5
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nayla hawaye ya gama wanke mata fuska, hawaye na tausayin masoyinta, hawaye na tausayin abin ƙaunarta, hawaye na tausayin halin da yake ciki a wannan lokaci. Hango fuskarsa take yi tana tunanin yadda ya koma a yanzu. Gabaɗaya nutsuwarta ta bar gangar jikinta.
Daƙyar ta iya buɗe baki ta ce, "Allah ya kyauta" daga haka ta yanke wayar ta toshe bakinta da hannunta fashe da kuka mai sauti. Mama tana tsaye daga bakin ƙofar duk hirarta da Salma taji, girgiza kai take yi domin wannan soyayyar da Nayla ta fara babban makami ne a gareta, tunda gashi har taji tana cewa mahaifinta bazai amince ba, lallai tsuntsu ya faɗo daga sama gashashshe.
Shigowa ɗakin tayi tana kallon Nayla, Nayla tana ganin ta manta halin da take ciki ta miƙe a guje ta faɗa jikinta tana kuka. Mama tana shafa bayanta a hankali cikin rarrashi ta ce, "yi shiru kar ki damu, kwantar da hankalinki."
Kuka Nayla take sosai na tausayi Omar da Didi, jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali da tsananin bugawar zuciya. Mama ta ɗago ta daga jikinta ta kalle ta ta ce, "Nayla ko baki faɗa min ba idanunki sun faɗa min soyayya ce ta saka ki a wannan yanayi, kar ki damu kar kuma ki tsorata ni uwa ce a gare ki, zan shige miki gaba wajan samun duk abinda ki ke so a wajan mahaifinki. Haka ne hasashena?."
Nayla ta yi shiru ta sunkuyar da kai sai hawaye da yake zarya a kan fuskarta. Mama ta sake janta jikinta ta ce, "kar ki damu ki nutsu, Ina tare dake a ko yaushe. Na kuma yi miki alqawari zaki auri wanda ki ke so ko waye shi, kar ki damu da faɗa min waye shi a yanzu, ki bari sai lokacin da zuciyarki ta aminta da ki faɗa min. Ni kuma a lokacin zan jajirce kamar ko wacce uwa na samar miki da farin ciki. Zan sadaukar da komai wajan ganin mallaki wanda ki ke so, zan iya yin komai dan tabbatar da cikar burin ki Nayla."
Nayla kwanciya tayi a jikin Mama tana kuka tana ji wani ɓangare na zuciyarta na tabbatar mata da abinda Maman ta faɗa. Ido ta a kulle cikin tausayi da soyayyar Omar..
[20/09, 8:29 am] +234 906 075 3382: KRB2P003
Arewabooks@nanahaleema11.
Mama sai da ta bar Nayla tayi kukan ta sosai sannan ta ɗago ta daga jikinta ta ƙarasa da ita kan gado ta zaunar da ita, ta tashi ta kawo mata ruwa a glass cup ta sha ta zauna a gefenta tare da riƙe hannunta tana kallon ta. Nayla sai sauke ajiyar zuciya take yi irin ta wacce ta sha kuka ta gaji. A tausashe Mama ta ce, "ki nutsu, Ina tare da ke a akan duk abinda ki ke so. Mahaifiyarki ni ta barwa amanarki, bazan taɓa bari wani abun ya cutar dake ba."
Nayla ƙarfin guiwa maganar Mama take ƙara mata hakan ya saka ta ɗaga kai Mama ta ce, "Sanar dani yaushe kika fara sonsa? Sannan a Ina yake?." Nayla ta rausayar da kai ta ce, "Mama don Allah bana so Abiy ya sani."
"Bazan sanar dashi ba Nayla, ai wannan sirrin uwa da ƴarta ne." Nayla ta sauke numfashi ta ce, "A Kano yake da zama Mama, kuma ni ma ban san lokacin da na fara sonsa ba."
Mama ta ce, "ya sunansa?." Nayla ta kalli Mama sai bata ce komai ba. Mama ta ce, "shikenan ba sai kin faɗa min waye ba, amma meyasa ki ke cewa Abiy bazai amince ki auren shi ba? Yana da wani hali mara kyau ne ko kuwa ba musulmi bane ba?." Nayla a sanyaye ta ce, "Musulmi ne Mama, kawai dai...." Sai tayi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce, "Ina jinki, kawai dai me?."
Nayla ta kalli Mama ta ce, "don Allah Mama mu bar maganar nan kawai." Mama tayi murmushi ta ce, "shikenan Nayla. Ki daina saka damuwarsa a zuciyarki komai zai zama labari kin ji ko?." Nayla ta ɗaga kai Mama ta ce, "Dama nazo na sanar dake Abiy ya ce zaki yi baƙo yau, sai ki shirya tarbar zuwansa."
Nayla ta amsa a sanyaye Mama ta dafata ta ce, "kar ki damu, zaki auri wanda ki ke so in sha Allah." Murmushin yaƙe kawai tayi dan ko amin din ma bata ce ba. To in ta ce amin ta wacce hanya auren zai zo? Na farko dai Omar bai ma san tana sonsa ba, na biyu yanzu haka Omar yana kulle babu ranar fitowarsa, na uku koda yana nan ita dai baza ta ce tana sonsa ba, na huɗu Abiy bazai amince ta auren shi ba. Duk da Abiy baya damuwa da lallai sai mai kuɗi za a aura, amma yana son good background da kuma good manners wanda ta tabbatar da Omar ya rasa. To akan me zata ce amin? Gwara tayi shiru kawai kar ta faɗa da bakin mala'iku.
Mama ta ce, "ki yi ƙoƙari ki dinga sakewa in ba haka ba Abiy zai takura ki akan rashin da sakewar nan taki." Kai ta ɗaga kawai Mama ta fita ita kuma ta koma da baya tana ajiyar zuciya. _Ko ya Omar yake yanzu? Wanne hali yake ciki?. Allah sarki Omar ya haɗu da sharrin so, son maso wani kenan, ni ina nan ina haukan sonsa shi yana can ya sadaukar da ƙuruciyarsa akan wata. Ko da yake abinda nake ji shima shi yake ji a zuciyarsa akan wata, amma ni bazan iya furta Ina sonsa ba, gwara na mutu....eh gwara na mutu kawai na huta. Bayan a gabana yake yiwa wacce take son sa faɗa a waya...? Hmmm ga wulaƙancin da Didi ta faɗa min ya yi mata a gabanta, me ya kaini cewa ina son Omar?. Gwara nayi shiru kawai na auri wanda suke sona._ tunanin da take yi kawai a zuciyarta kenan ita kaɗai cikin yanayi na damuwa da bugawar zuciya.
Sai bayan sallar i'sha sannan aka turo tazo baƙon ta yazo. Daƙyar ta samu ƙarfin guiwar motsawa daga inda take ta miƙe ta canja kaya zuwa doguwar riga ta slik mai kyau da santsi. Ɗinkin bubu ne, amma wacce ake yayi, wacce ake ɗan ɗaureta daga ciki. Tayi mata kyau sosai ta saka hular kayan sannan ta yaga mayafi ta fito zuwa falon.
Yau ma dai baƙuwar fuska ta gamu da ita, daman Abiy ya ce mata mutum huɗe ne har Abbas, ta zauna da mutum biyu ga na ukun, na huɗun kuma Abbas ne daman ta sani. Kamar sauran bata haɗe rai kuma bata kore shi ba, sun gaisa da girmamawa ya gabatar da kansa itama ta gabatar da kanta, sun ɗan tattauna kafin ya yi mata sallama ya tafi.
Kamar ko yaushe yau ma dai Abiy na zaune a falo ta dawo, shi da Yaya J ne da kuma Mama. Da sallama ta shigo kamar baza ta zauna ba sai kuma Abiy ya kira ta dole ta dawo ta zauna gabanta na faɗuwa matuƙa. Abiy ya kalle ta ya ce, "Mamana kun gaisa da Lamin ɗin?." Nayla ta ɗaga kai ta ce, "Eh Abiy, ya tafi ma."
Abiy ya ce, "To daga kansa zan dakatar da duk mai zuwa neman aurenki. A cikin Omar, Lamin, Abbas da Hashim ki ɗauki guda ɗaya a cikin su. Dukkan su na amince da iyayen su, aikin su, ilimin su, halayen su da sauran su. Sannan ko wanne ɗan babban gida ne sun fito daga gidan mutunci da tarbiyya. Babu ɗaya a cikin su da yake shan koda taba balle a kai ga batun maye ko wani abun. Babu wanda na bawa damar zuwa wajanki a cikin su har sai da nayi bincike a kansu sannan na bari suka zauna dake. Kun tattauna da ko wanne a cikin su, to ki zaɓi guda ɗaya da ki ke jin zaki iya zaman aure dashi. A cikin guda huɗu ai na san baza ki rasa wanda ya kwanta miki a rai ba, In kuma ɗan uwanki Abbas kika ɗauka duk ɗaya ne."
Nayla gabaɗaya kalaman Abiy tarwatsa mata zuciya suke yi, dan gabaɗaya abinda yake lissafowa samarinta suna da shi ita kuma hange ta ke yi Omar bashi da ko ɗaya. Gashi Abiy ya jefa ta a tsaka mai wuya, ta ya ake tunanin zata iya ɗaukar mutum ɗaya a cikin su da sunan tana so? To wa take son ɗin a cikin su...?ita ko kamannin su ma bata tunanin zata iya hange a idanunta balle tayi batun so, ko waya suka kirata bata jimawa take sallama dasu ta kwanta. So ɗaya take yiwa mutum ɗaya tak a duniya kuma shine Omar Tiger, ta kuma tabbatar son bashi da wani amfani tunda ba auren sa zata yi ba.
Abiy ya katse ta ya ce, "kina ji ko?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "in sha Allah Abiy. Ka taya ni da addu'ar neman zaɓin Allah." Abiy ya murmusa ya ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi a rayuwar ku baki ɗaya." Aka amsa da amin ta tashi ta shiga ciki.
Abbas ta gani yana yi mata waya ta taɓe baki dan baza ta ɗauka ba, ita a cikin samarin nata ma zata iya auren kowa amma ban da Abbas, sam tsarin Abbas bai mata ba, ita maza masu gym ɗin nan ba burge ta suke yi ba. Omar ne kawai mai irin wannan jikin da taji ya burgeta amma shi kam Abbas ko kaɗan bata son halittar jikinsa. A cikin samarin na ta ma gwara Omar, zata iya ɗaukarsa ba dan ya cancanta a wajanta ba, sai dan saboda sunan masoyinta da yake dashi kuma yana da sanyi bashi da yanayi saɓanin nata Omar ɗin. Da wannan tunane-tunanen ta shirya ta kwanta tana tunanin halin da masoyin ta yake ciki a Abuja.
Bayan Kwana biyu.
*Abuja.*
Yadda Narma take kuka sai ka ɗauka mutuwa aka yi mata, ta rame sosai ta yi wani iri da ita kamar ba ita ce Narma ƴar gayu mai ji da ƙwalisa ba. Soyayya ta sakata birkicewa, ta koma kamar wata mai taɓin hankali saboda surutan da take yi ita kaɗi. Wannan dalilin ya saka iyayenta suka sake gasgata asiri Omar ya yi mata.