Sashe 31
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta ce, "har yanzu bakya jin zaki iya zama da mutum ɗaya a cikin su?." Nayla ta ɗaga kai ta ce, "bana ji Mama, wallahi bana ji gabaɗaya." Mama tayi ajiyar zuciya ta ce, "Kawai zan faɗa masa akwai wanda ki ke so." Nayla ta wara idanu waje tana kallon Mama da firgici ta ce, "don Allah Mama kar ki faɗa masa, in kika faɗa masa ya nemi sanin waye shi fa?."
"Sai mu faɗa masa waye, in ya kuma kira ki ya tambaye ki ki tabbatar masa da kina sona kuma aurensa kike so ki yi."
Nayla ta fara girgiza kai cikin tsoro ta ce, "bazan iya ba Mama, bazan iya ba wallahi." Mama ta dafata ta ce, "ni zan iya yi miki faɗan Nayla, abinda nake so in ya kira ki ya tambaye ki ki tabbatar masa dake shi kike so kuma shi ki ke son aura. Zaki iya ko baza ki iya ba?."
Nayla ta kalli Mama cikin rauni ta ce, "Mama bazan iya ba, bazan iya kallon Abiy na tabbatar masa Ina son Omar ba, bazan iya ba gaskiya." Mama ta ce, "zaki iya, zuciyarki zaki saurara da zarar ya kiraki, kar ki bar harshen ki ya sarrafa kalaman zuciyarki, kai tsaye ki bari su fito daga cikinta ki faɗa masa gaskiya, in ba haka ba in ya gano da kansa ransa ne zai ɓaci sosai."
Nayla ta ce, "Mama gwara ya gano da kansa da ace nice na tabbatar masa." Mama ta dafata cikin rarrashi ta ce, "Nayla bazan taɓa bari naga kina son abu ina da damar baki shi ban baki shi ba, sannan bazan taɓa bari naga kina shan wahala akan abinda bai fi ƙarfin ki ba kuma na zuba miki idanu. Zan iya yin ko meye wajan ganin na samar miki da farin ciki koda ni zai zama silar baƙin cikina. Dan haka ki bani haɗin kai Nayla, na tabbatar miki zanyi abinda mahaifinki zai baki abinda kike so ba tare da tashin hankali ba ko wani abun."
Nayla ta kalli Mama cikin gamsuwa da kalamanta ta ce, "Na sani Mama, amma bakya ganin Abiy zai yi fushi dani?."
"Babu fushin da zai yi dake, ki bar komai a hannuna ina tabbatar miki da babu abinda zai faru sai alkhairi." Nayla ta sauke numfashi ta ce, "To Mama" ta faɗa a sanyaye tana wasa da hannunta. Mama tayi murmushi ta ce, matar Omar." Kunya ta bata sai ta rufe fuska da hannunta kafin ta buɗe ta ce, "Mama shi fa bai san Ina sonsa ba, taya zan aure shi?." Mama ta yi murmushi cikin shigar kwantar da hankali ta ce, "ke dai ki jira mu gama da Abiy zamu koma kansa." Kai ta ɗaga kawai bata ce komai ba Mama ta fita ta barta a zaune tana tunani.
Washe gari a ɗarare ta shirya ta tafi aiki, ko a can ma haka take yin komai babu kuzari har lokacin dawowar ta gida yayi ƙarfe biyar na yamma. Tana ajjiye motarta taga motar Abiy sai da gabanta ya faɗi tayi saurin wucewa ciki ta shige ɗakin ta harda kulle ƙofar da makulli.
Bayan sallar i'sha kamar yadda Abiy ya saba yana zaune shida Mama bayan ya gama dinner ya kalli Mama ya ce, "ya kuka yi da Nayla? yau ne kwana biyun da na bata." Mama ta fuskance shi sosai ta ce, "maganar gaskiya Nayla bata son samarin nan guda huɗu." Abiy ya kalleta cikin mamaki ya ce, "kamar ya bata sonsu? Duka mutane huɗun babu wanda take ji zata iya aure?. Wannan ai shirmen ne da rainin hankali, na bata iya lokacin da zan bata kuma tazo min da wannan iskancin?." Mama ta ce, "hmm wani daban zuciyarta take so ba su ba."
Abiy da mamaki ya ce, "wani daban kuma take so? Waye shi?." Tayi ajiyar zuciya ta ce, "Wani ne daban a Kano, babban abin haushi da tashin hankalin ma data buɗe baki ta faɗa min waye yafi komai ɗaga min hankali. Kuma wai bai ma san tana sonsa ba, duk wannan rashin lafiyar da take fama da ita cikin kwanakin nan duk saboda shi ne, wannan ramar da tayi da rashin nutsuwa duk akansa ne. In da ace mutumin kirki ne na gari dan tayi haka a kansa ba laifi bane, amma ni har kunyar faɗa maka waye nake yi wallahi" Mama ta faɗa cikin zallar nuna takaicinta.
Abiy da yake so Mama ta kai ƙarshen maganar a ƙagauce ya ce, "wa take so? Waye shi ki faɗa min bana son zagaye-zagaye." Mama ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "wannan ɗan daban yaron nan da ka yiwa hanya aka fito dashi har suka zo gidan nan godiya. Shi Nayla take mutuwar so, ta tabbatar min da in baka amince ta aure shi ba zata iya barin gidan nan, ta ce min zata iya barin kowa na gidan nan taje ta tare dashi kaɗai. Wannan kalma ta tayar min da hankali, nayi rarrashin na nuna mata hakan kuskure ne amma Nayla sam ta kasa amincewa."
Mutuwar zaune Abiy yayi jin kalaman Mama ya zuba mata ido ya kasa cewa komai, Daƙyar ya iya tattaro kalaman bakinsa ya ce, "Omar ɗan daban Kano take so? Wai maganar nan gaskiya ce ko wasa kike yi min?."
"Wallahi da gaske nake, ita da kanta ta faɗa min. Da farko na ɗauka wasa ne amma Jidda ta tabbatar min da gaske shi take mutuwar so. Abin haushin ma ko ta ita baya yi, in da na kirki ne ma da sauƙi to na banza ne. Wallahi ji nake kamar na yi kuka."
Abiy ya rasa ma abinda zai ce kawai sai ya miƙe ya shiga zuwa cikin gidan ya hau sama har ɗakin Nayla ya same ta a zaune tana ganinsa ta firgita ta miƙe tsaye. Kallonta yake yi kamar yadda take kallon sa dan in ba rashin lafiya ba babu abinda yake kawo Abiy ɗakinta sai dai in bata da lafiya.
Abiy kallon ta yayi ya ce, "Nayla da gaske ne abinda Maman ki ta faɗa min? Da gaske kina son Omar na Kano?." Gabanta ya yanke ya faɗi ta ɗago ido ta kalli Mama da take gefen ta tayi mata alama da ta amsa ta sake saukar da ido ƙasa tare da zube guiwarta duka biyun a gaban Abiy.
Abiy ya ce, "tambayar ki nake da gaske kina sonsa? Da gaske akan sa kike wannan rashin lafiyar?." Nayla ta sake sunkuyar da kai hawaye na zuba a idonta. Mama ta ce, "Abiy ka yi mata a hankali" ta ƙaraso kusa da Naylar ta ce, "Nayla ki faɗa masa abinda yake ranki. Da gaske kina son Omar?." Nayla zuciyarta bugawa take yi sossai, zuwan Mama kusa da sai ya ƙara mata ƙarfim guiwar da ta amsawa Abiy tana so ɗin.
Dafata Mama tayi hakan ya saka tayi ajiyar zuciya ta sake saukar da ido ƙasa ta ce, "Da.....gas....ke....ne......Abiy....."ta faɗa a rarraebe cikin tashin hankali da tsoro. Abiy ya ce, "da gaske ne me? Da gaske shi kike so?." Ta ɗaga kai alamun eh. Abiy ya ce, "'magana zaki yi min!." Tsawar da ya yi mata sai da ta tsorata, a firgice ta ce, "Eh Abiy, da gaske shi nake so..." ta ƙarasa faɗa cikin muryar tsoro da tashin hankali.
[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P018
“Hauwa!” Abiy ya faɗa cikin tsawa yana kallonta cikin ɓacin ran jin kalamanta masu kama da rashin hankali ko wacce bata cikin hankalinta. Dumm ƙirjin Nayla ya buga, ta wara idanu waje cikin tsantsar tashin hankali da firgici. Tunda take da Abiy bata taɓa ji ya kira asalin sunanta ba, koda wasa bai taɓa kiranta da Hauwa ba sai dai ya ce Mamana ko kuma Nayla, amma yau gashi ya kira sunanta da murya mai amo mai nuni da tsantsar ɓacin ran da yake ciki.
Kasa ɗago kai tayi dan yanayin muryar mahaifin nata da taji bata taɓa jinta a kausahe haka ba, hakan ya saka ta kasa ɗago kai ta amsa kiran da ya yi mata. Abiy ya ce, “kina cikin hankalinki kuwa?.” Nayla ta sake sunkuyar da kai kamar ruwa ya cinyeta ko motsin kirki bata so ta yi.
“Wannan yaron ki ke kallona kina cewa shi kike so Nayla? Me ya shiga kaaki ne?. Wannan dalilin ne ya saka kika tayar da hankalin ki a karɓo shi daga hannun Senator?.” Yadda yake magana cikin murya mai amo ya saka Nayla yin danasanin furta abinda ta ce dan gabaɗayata rasa nutuswarta. Abiy baya taɓa yi musu tsawa tunda suka tashi, yadda yake yi mata a yanzu ya sakata take ganin abun baƙo shiyasa ya tsoratata sosai.
Mama ce ta kalle shi ta ce, “ka yi mana a hankali Abiy.” A fusace ya ce, “bazan yi mata a hankalin ba, yarinya ce ko kuma bata da hankali? Bata san abinda ya dace da wanda bai dace ba ko me?. Duk mazan duniyar nan, duk mazan da suke Kano da wajan Kano ta rasa wanda zata fara so sai riƙaƙƙen ɗan daba wanda aka yi masa shaida mara kyau?. Meye abin so a tare dashi!.” Mama ta kalli Nayla da ta kasa motsi ma balle tayi magana, ta kalli Abi zata yi magana ya dakatar da ita ya kalli Nayla ya ce, “Hauwa!.”
Nayla murya na rawa ta ce, “Na’am Abiy.”
“Tunda ta nan ki ka ɓullo zan yiwa tufkar hanci, zan sake baki dama ki fitar da mijin aure a karo na uku, in kika sake aikata irin abinda kika aikata yanzu bazan sake baki dama ba har abada. Sannan ki cire batun wannan yaron daga zuciyarki, ba mijin aure bane, in ma bakya cikin hankalinki to ina mai baki shawara da ki dawo cikin nutsuwarki ki san waye a gaban ki!” Ya ƙarasa faɗar maganar da tsawa yana nuna ta da yatsa.