Sashe 51
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana nan zaune taji kiran sallar i'sha ta tashi a sanyaye tayi sallah ko shafa'i da wutir bata yi ba tana zaune tana jiransa. Wayar Didi ce tayi ƙara ta ga sunan Salma ta ɗauka da sallama, Salma ta amsa ta ce, "Didi su Daddy ne suka ce na faɗa miki suna hanya, ku shigo gidan Hajja yanzu zasu ƙaraso." Daƙyar ta iya amsawa sannan ta kashe wayar cike da tsoro.
Babu jimawa taji an dafa kafaɗarta, ta ɗago kai ta kalle shi kamar yadda yake binta da kallo cikin son gano damuwarta. Kamar ta buƙata ya yi wanka ya canja kaya zuwa manyan kaya riga da wando na shadda ash colour. Ya yi mata kyau sosai a idanunta, ta zuba amsa ido tana kallo kafin ta miƙe tsaye ta ce, "ka yi kyau." Kallon fuskarta ya yi ya ce, "kuka ki ka yi?." Kai ta girgiza alamun a'a ya ce, "gashi nan na gani a idanunki, kuka ki ka yi Didi? Ban san wanne abu ne wannan da ki ka kasa sanar dani ba, kodan kin yi aure ne yanzu kina ganim ban kai na san damuwarki ba ban sani ba."
Didi ta ce, "yanzu zaka ji."
"Mu je to, na shirya ko?." Ta kalle shi ta ce, "shiyasa na ce ka yi kyau, dama zaka saka babbar riga."
"Taɓ bazan iya ba, ni bani da babbar riga ma a duniya. Ban sani ba ko sai nan gaba." Didi ta yi murmsushi kawai bata ce komai ba sai ya kalle ta ya ce, "wataƙila sai aurena zan ɗinka." Gabanta ya faɗi sosai a haka ta yafa mayafi ta ɗauki jakarta da wayarta ta ce, "ka kashe hasken gidan sai mu je."
Ya kalle ta da mamaki ya ce, "Kashe hasken na meye kuma? Abinda dai zan dawo." Ta kalle shi ta ce, "Don Allah ka kashe, in ka kashe ka kulle gidan." Zai yi magana ta ce, "Allah na ce." Bai ce komai ba ya yi abinda ta ce suka fito ƙofar gidan ya kulle sannan ya kalleta ya ce, "Sai ina....?."
[25/09, 11:34 am] +234 810 686 6659: KRB2P028
Arewabooks@nanahaleema11.
Kallon ƙofar gidan Hajja tayi ta ga manyan motoci da alama su Daddy ɗin sun iso. Ta kalli Omar dsa yake kallonta yana jira yaji inda zasu jw ta ce, "Zo mu je." Gaba tayi yana binta a baya har ƙofar gidan Hajja. Da mamaki yake kallon ta ganin ta tura gate ɗin ta shiga sai ya ce, "na jira ki?."
"Ka shigo dai."
"A'a ban yi niya ba gaskiya, ko na shiga babu lada, kedai ki je ki gaishe ta."
"Ka shigo Omar, don girman Allah." Mamakin wannan magiyar da take yawan yi masa yake yi ta san kuma baya so, babu yadda iya haka ya shiga kamar yadda ta ce.
Sallamarta da shigar falon ya saka suka mutanen falon suka san sun iso aka amsa mata tana bin kowa da kallo. Gaisawa suka yi da kowa da yake zaune, Omar da yake bayanta ya gaishe su cikin gaisuwarsa ta ko yaushe taƙaitacciya. Kallon Didi yayi ya ce, "ina jiranki a waje." Hannunsa ta riƙe ta ce, "ka shigo ka zauna." Kallon mutanen falon ya yi da suke kallonsa ya kalle ta ya ce, "na zauna nayi me kenan? Zan dai jira ki." Didi ta ce, "ka zauna don Allah."
Juya idanu ya yi cikin gajiya ya ce, "wai magiyar nan ta meye? Kin fara isata wallahi." Didi ta yi ƙasa da murya ta ce, "Mutane suna jinka, don darajar annabin Allah ka zauna." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya ƙaraso ya zauna akan carpet kamar yadda ta zauna.
Daddy ya kalli Abba da yake kallonsa shima suka ɗauke kai a tare. Nayla tun da ya shigo da maganarsa ƙirjinta yake bugawa, tana jin gardama da yake yi akan ya zauna, a nan ta tabbatar da har lokacin bai san abinda yake faruwa ba. Hawaye ta ji na sakko mata cikin tausayin kanta.
Daddy ne ya fara magana bayan an buɗe taro da addu'a ya ce, "kowa ya san abinda ya tara mu a nan,magana ce akan abinda ya faru da kuma wanda zai faru yanzu. Nayla dai an ɗaura mata aure a wani bahagon yanayi wanda mahaifinta ne kaɗai ya san dalilinsa na yin hakan. Amma ya ba mu ragamar kula da komai a yanzu, ya ce mu gyara inda aka ɓata shiyasa mu ka zo aka zauna gabaɗaya domin a tattauna a kai."
Omar jin kalaman Daddy ya saka shi ya kalli Didi zai yi magana ta yi masa alamun don Allah ya yi shiru. Dole ya yi shiru amma shi bai ga amfanin zamansa ba, har ita Didin bai ga amfanin zamanta ba tunda taro ne na familynsu to su me zai kawo su ciki?.
"Omar!." Daddy ya katse masa tunani hakan ya saka ya ɗago yana kallonsa ba tare da ya amsa ba. Daddy ya ce, "ka san wannan?." Ya faɗa yana nuna masa Nayla da take zaune kai a ƙasa. Kallon inda aka nuna masa ya yi ya sake kallon Daddy ya girgiza kai alamun bai santa ba.
Daddy ya yi murmushi shi kuma Omar ya mayar da kai ƙasa dan baya jure magana da manyan mutane irin su Daddy, Daddy ne mutum na biyu bayan Abiy da ya yi amsa kwarjini a duniya. Daddy ya ce, "Omar ranar juma'a da ta gabata sati ɗaya kenan yau, ƙaddara ta gifta a tsakani har aka yanke hukunci ba tare da ka sani ba. Domin kuwa a wannan ranar aka ɗaura aurenka da ita wacce take zaune yanzu." Omar bai motsa ba dan bai ɗauka shi Omar ɗin ake nufi ba, ya yi tunanin akwai wani Omar ɗin a wajan bayan shi.
Ganin bai nuna firgici ba sai Didi ta ɗan ji sanyi tana cigaba da kallonsa. Daddy ya ce, "Mahaifin Nayla ya yanke hukunci cikin wani yanayi na fushi da wani dalili na sa, ya aurawa ƴarsa kai kamar yadda ake ɗaura ko wanne aure. Wakilanka sun shaida dan sune suka karɓi auren, sannan Yayarka ma ta shaida anyi hakan. To mun zauna a nan ne dan mu ji ta bakinka akan auren, dan yanzu ga amarya ma an kawo ta daga Kaduna zuwa nan. Kana ganin zaka iya zama da ita a matsayin mata?. In baza ka iya ba kar kayi mana kara, ka faɗi abinda yake zuciyarka domin muna so komai ya ƙare a nan wajan."
Shiru kowa ya yi ana jiran amsar Omar, shi kuma bai ce komai ba dan har ga Allah bai ɗauka dashi ake magana ba. Ganin shirun ya yi yawa Hajja ta ce, "Ummaru!." Ɗago kai ya yi ya kalle ta ta ce, "baka ji abinda aka ce ba ne?." Omar ya ce, "na ji mana."
"Baka ce komai ba." Ya kalli Hajja ya ce, "Hajja a ganina kamar maganar ai bata shafe ni ba ko? Zamana a wajan nan ma bashi da amfani tunda maganar da ta shafeku ku ke yi. Ba batun aure naji ana yi ba?."
Hajja ta ce, "shi ake yi mana, kuma in bai shafe ka ba ai ba za a ce kazo ka zauna ba Omar." Ya ce, "nima shine nayi mamaki ai. Yanzu me ya shigo da ni cikin maganar?." Didi ta ce, "Saboda kaine mijin! Kaine Omar ɗin da ake zancen ɗaurawa aure da Nayla jikar Hajja!."
Kallon Didi ya yi ya ɗauke kai dan gani yake ba dashi take ba, sake kallon ta ya yi yaga dai shi take kallo ya ce, "Didi!." Ta ce, "Omar!."
"dawa ki ke maganar nan?."
"Da kai nake, da kai nake Omar Osman Omar!. Kai ne wanda aka ɗaurawa aure tun last week a gidan Kawu, ni kaina shaida ce dan a gabana aka yi."
Kallon ta yake yi dan wallahi ya ɗauka ta ɗan samu matsalar kai ne ya saka take cewa haka. Hakan ya saka ya tausasa murya ya ce, "Didi tun ɗazu na faɗa miki ba a nutse ki ke ba, ki bari ki nutsu sai ki yi magana. Me zai kawo ni cikin batun aure kuma? Wani Omar ɗin ne daban amma ba ni ba. Duk inda akace Omar sai ki ɗauka ni ake nufi? Ki nutsu don Allah" ya faɗa yana kallonta har lokacin bai amince dashi ake ba.
Abba ya ce, "Omar ƙanin Aisha kalle ni." Ba musu ya kalli Abban ya ce, "dakai ake, maganar da ake faɗa akanka take ba wani ba. Kai mijin Nayla ne tun waccan juma'ar, Nayla matarka ce ta sunna." Kallon Abba ya ke yi dan ya san dai bazai masa ƙarya ba, ya kalli Didi da take kallonsa ta ce, "E da gaske ne."
Omar ya ce, "E da gaske ne me?."
"An ɗaura aurenka tun wancan satin a gidan Kawu."
"amma dai a mafarki ko? Mafarki ki ka yi akan hakan ko kuma wannan ma mafarkin ne?." Mama Sa'adatu ta fusata da kalaman Omar na rainin hankali ta ce, "Omar ba mafarki ba ne gaskiya ne, da gaske an ɗaura maka aure da Nayla tun waccan juma'ar da ya wuce. Ka daina yi mana wasa da hankali mana."
Shiru Omar ya yi na wani lokaci bai ce komai ba, ya sake kallon mutane falon ya tabbatar dai ba fa mafarki yake yi ba da gaske ne. Ya ɗan girgiza kai ya ce, "Aure!." Kallon Didi ya yi da take kallonsa dan ta kasa ɗauke ido daga kansa, ta san hali ƙiris yake jira yayi wani abun,shiyasa duk motsinsa a kan idonta yake yi. Omar ya ce, "Ni na kasa fahimta ne Didi, wai auren na wasa ko na gaske?."
"Omar ana aure da wasa ne? In auren wasa ne zaka ganmu a zaune a wajan nan ne?, ai mu ba abokan yin wasan ka bane. Ka nutsu mu yi maganar da ta tara mu a nan. Kamar yadda ka ke jin maganar bazata haka mu ma muka ji ta, In kana ganin ƙarya mu ke yi maka ka kira Kawunka ka tambaye shi sai ka tabbatar" Abba ya faɗa cikin faɗa dan Omar ɗin ya fara fusata shi.