← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 52

Sashe 4

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ta shiga waje mai kyau aka ajjiye ta, inda masu azabtar dashi ɗin suke nan suka bata ta zauna. Bouncers ɗin da suke gidan kaɗai abin tsoro ne, Narma sai kallo su take yi domin kana ganin su ka san basu da imani, in ka shiga hannun su sai sun karya ka. Ita kam ta kasa zama sai zagaye take yi, tana ji an buɗe ƙofa da sauri ta kalli wajan. Ajiyar zuciya ta sauke ganin Omar da kayan jikinsa da suka zo amma kayan sun yi baƙi, duk da ba ɓaki sosai ba amma sun yi duhu. Fuskarsa babu walwala ko kaɗan, sannan wahala ta bayyana ƙarara akan fuskarsa. Da gudu Narma ta taho inda yake zata rungume shi ya motsa ya ɗan ja baya kaɗan sai ta kalle shi tana kuka.

Zubewa tayi a wajan ta ce, "im sorry Faruk! I'm sorry!!" Ta faɗa tana kuka sosai tana durƙushe a gaban sa. Bai ce komai ba bai ma kalle ta ba idanunsa a rufe babu abinda yake addabar zuciyarsa kamar ɓacin rai, babu abinda yake damunsa kamar halin da Didi take ciki. Zaman inda yake da wahalar da ake bashi baya damuwan sa kamar barin Didi da ya yi a gida ita kaɗai. Ya san tana can tana kuka, ya san tana can hankalinta a tashe saboda rashin ganinsa. Wannan tunanin yafi halin da yake ciki ƙuna da raɗaɗi a zuciyar sa.

Narma ta ce, "Na yi maka alqawari zan yi duk yadda zan yi wajan ganin ka bar wajan nan, zan yi iyakar iyawata wajan tabbatar da Dad ya ƙyaleka. Ni lawyer ce, zan yi duk abinda zan yi saboda kai Faruk." Sam kalaman ta basa kwantar masa da hankali dan gabaɗaya ma baya so yaji koda maganarta, ba wai dan ya tsane ta ko dan yana jin haushinta ba, sai da tsantsar baƙin cikin da yake zuciyarsa.

Narma ta sake cewa, "kayi magana Faruk, ka ce wani abun ko zan ji daɗi." Sai a lokacin ya sauke shanyayyun idanunsa a kanta, haɗa ido suka yi ya kalle ta na sakan biyar kafin ya janye idanunsa. Tabbas ta rame kana ganinta ka san tana cikin damuwa. Damuwarta bata dame shi ba, inda zai iya yi mata magana da ya yi magana akan Didi, amma baya tunanin ko waye yazo a wannan lokaci zai iya buɗe bakinsa ya yi magana, shirun shine alkhairi a gare shi.

Omar da kansa ya juya ya koma inda aka ajjiye shi, Narma na kiransa amma ya yi mata banza ko juyowa bai yi ba. Bashi da nutsuwar da zai iya kallon ta har ya yi mata magana shiyasa bai ce komai ba.

Narma da hawaye shaɓe-shaɓe ta fito ta shiga mota ta fizgi ta da ƙarfi zuwa gida. Tana tafiya tana kuka har ta je gida tana shiga falo ta zube a jikin Mum tana kuka mai sauti. Hankalin Mum ya tashi dan ita take nema tun bayan fitarta ta ce, "Narma Ina kika je? Kin san baki da lafiya kika fita ke kaɗai?. Me ya same ki ke kuka haka?."
"Mum naje na ga Faruk, Mum gabaɗaya an canja min Faruk ɗina, Mum Dad ya saka ana azabtar min dashi. Mum abinda nake ji a zuciyata ji nake kamar na kashe kaina. Kinga bouncers ɗin da Dad ya ajjiye suna dukan Omar, kinga irin azabar da ake yi masa? Kashe kaina kawai zan yi!."

Hankalin Mum ya tashi da kalaman Narma, da hanzari ta dannawa Sen waya Allah ya taimaka bai yi nisa ba ya ƙaraso gidan.  A lokacim Narma take cewa, "Mum Ina sonsa, Ina ƙaunarsa. Mum in Dady bai fitar dashi daga gidan da ya saka aka ajjiye ba ni zan yi da kaina, in aka hana ni zan yiwa kaina illa Mum, zan iya kashe kaina akan Faruk Mum...!" Ta ƙarasa faɗa tana jan sunan Mum ɗin tana kuka.

Sen ya ji ta ya ƙaraso ya tasar da ita tsaye ya rungume ta sai kuka take yi yana rarrashinta. Surutai take tayi masa barkatai akan Omar yana ta rarrashi yana shafa bayanta, sai da ya ga ta ɗan yi sanyi sannan ya kalle ta ya ce, "je ki ɗaki ki huta." Zata yi magana ya ce, "kar ki ce komai Daughter, je ki" ba musu ta tafi zuwa ɗaki tana share hawaye.

Mun ta kalli Dad a ƙufule ta ce, "Tunda har ka san zata iya binciko inda yake har taje ta ganshi meye amfanin barinsa nan? Meyasa baka kai shi inda baza ta iya zuwa ba?." Dad ya ce, "shiyasa zan tura ta London."
"Saboda shi sai ta bar Nigeria? Kenan shi ya yi riba akan ta ko me?."
"Saboda ta samu peace of mind. Shi kuma zan ji dashi" ya faɗa yana hawa sama ya bar Mum a wajan. Dole ya san abinda zai yi akan Omar kafin ƴarsa ta rasa hankalinta akansa.

*Kaduna.*

Nayla na zaune sun gama magana da Twiny a waya sai ta kira Salma, tana ɗauka ta ce, "Sis ya ki ke? Ya Hajja?." Salma ta ce, "lafiya lau Nayla, ya Mama da Abiy?."
"Kowa yana nan lafiya lau. Kin ga alert?."
"Eh naga kuɗi ya zo, na ce Nayla kuɗin wa ta saka min." Nayla ta ce, "Kuɗinki ne, first salaryna ya sauka."

Salma tayi dariya ta ce, "godiya nake ma'aikaciya." Murmushin yaƙe Nayla tayi kafin Salma ta ce, "ya ki ke? Ina fatan yanzu babu damuwa ko?." Murmushi ta yi kawai bata ce komai ba dan maganar da suka gama da Jidda kenan. Salma ta ce, "Nayla don Allah ki kwantar da hankalinki, in kina tayar da hankali Abiy bazai ji daɗi  ba. Yanzu kin samu magana dashi ɗin?."

Nayla ta ce, "Salma na faɗa muku ni bana so ya san Ina sonsa, gwara ku taya ni addu'a kawai Allah ya kawo min ƙarshen ko meye. Bana jin zan iya furta masa kalmar so gaskiya."
"Amma Nayla cutar da kan ki ke ke yi. Ni ki faɗa min inda take a faɗin Kano naje na same shi nayi masa magana, sai cutuwa ki ke yi a kansa, ba ke kika sakawa kan ki ba Allah ne, meye aibu dan an faɗa masa?." Nayla ta murmusa ta ce, "Salma sanin waye bashi da wani mahimmaci, koda yana sona ma aure na dashi bazai yu ba. Na tabbatar Abiy bazai aura min shi ba."

Da mamaki Salma ta ce, "kafiri ne?." Nayla ta ce, "musulmi ne yana sallah kamar kowa, kawai dai aurena dashi na san bazai taɓa yuwa ba. Balle kuma ni bazan faɗi suna ba, kuma sannan bazan ce Ina sonsa ba." Salma tayi shiru kafin ta ce, "Nayla kar ki cutar da kan ki, ni na san Abiy indai kina sonsa shima zai so shi Nayla." Nayla bata ce komai ba Salma ta ce, "kin yi shiru."

"To me zan ce miki Salma? Asalin gaskiyata nake faɗa miki Salma, na san Ina sonsa, Ina ƙaunarsa amma bazan iya furta masa ba, kuma bazan iya faɗa muku sunansa ba koda zan mutu. Ƙarƙari in na mutu ku ce soyayya ce ta kashe ni keda Jidda. Tabbas in na bar duniya a yanzu da tasirin soyayyarsa a yin ajalina."

Salma ta sake karya murya zata yi magana Nayla ta katse ta ta ce, "Ya Didi? Tana lafiya?." Salma jin ta kawar da maganar sai ta ce, "Allah ya kawo miki mafita, in alkhairi ne a gare ki Allah ya zaɓa miki shi ƴar uwa."

Ta amsa da amin kafin Salma ta ce, "Didi tana gida, ɗazu dai ta fita daga nan, da yake a nan ta kwana." Nayla ta ce, "ta kwana a gidan Hajja? Lafiya dai ko?."
"Ba ƙalau ba dai. Taƙadirin ƙaninta ne mana, ɗan kuka mai jawa uwarsa jifa." Gaban Nayla ya faɗi matuƙa ta ce, "Me ya faru?."

Salma ta ce, "Wai ƴar Senator Sagir yake so dan tsabar bashi da hankali, to ko ni zauna gari banza babana ba Senator ba yazo ya ce yana sona ba sai na saka an yi masa abinda har ya mutu bazai manta dashi ba?. Ke ko bani ba, ko wacce bata kai ni rufin asiri ba ya ce yana so sai mun haɗu mun hana ta sonsa saboda ba mijin da za a so bane. Wai ƙafa ya ɗauka yaje har Abuja gidan Kano centaral Senator wai yana son ƴarsa Narma. Ki ji fa Nayla, Barr Nass fa wacce ki ke gani a social media yaje neman aure dan tsabar ƙarfin hali irin nasa. Tsabar wiwin da yake sha ta taɓa masa ƙwaƙwalwa harda kwasar gajojin ƴan daban yaransa suka tafi wai neman aure. Ai kam Sen ya yi ram dashi, ya saka an ɗaure shi yana neman hanyar da zai kai shi prison, kuma ya ce  sai ya yi life in prison."

Dum dum dum dum! Haka ƙirjin Nayla yake bugawa, ta zazzaro idanu waje kamar Salma ɗin tana ganinta. Duk da a.c da take ɗakin gumi ya gama wanke mata jiki saboda tashin hankali. An kama Omar? Omar ɗin ta da ake zancen zai yi life in prison? Omar fa masoyinta.

Salma ta katse mata tunaninta hanyar cewa, "Shine fa hankalin baiwar Allah ya tashi, ta shigo tana kuka abin tausayi. Allah ya haɗa ka da ɗan uwa irin Omar ma ko ƙaddara, haka kawai ya saka hankalin baiwar Allah ya tashi. Hajja har Daddy ta yiwa magana ya ce zai san yadda za ayi, za a yiwa Sen ɗin magana ko zai fito dashi. Gashi an ce bashi da kirki ko kusa, baya ɗaga ƙafa akan komai daƙyar ya amince ya bada Omar. Ke ni fa a wajena Omar ya cancanci fiye da haka, tsabar raini da tsaurin ido ya ɗauki ƙafa ya je har gida wai ƴarsa yake so? Ni ban ga laifinsa ba."

Nayla bata iya cewa komai ba domin ƙwaƙwalwarta tafi hutun rabin lokaci. Salma bata damu da shirun ba ta kuma cewa, "jiya da daddare Hajja ta saka ta dawo nan ta kwana saboda gidan babu kowa, kuma kin san ƴan daba ƴan uwasa masu jin haushinsa zasu iya shigowa su cutar da Didi. Inda mutumin kirki ne ma sai ka tauyasa masa, gwara ma haka."
Chapter 4 · 0% Book details