← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 52

Sashe 37

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa mamakin Abiy yake yi kawai kallon suke yi, a take aka kira mazan gidan cousins ɗin Omar kenan aka tara shaidu Kawu ya bada sadaki naira dubu ɗari biyu. Abiy ya umarci Jawad da ya je mota ya ɗauko goro da alewa ba jimawa ya kawo aka shaida saurin aure a wajan. Didi dai tana zaune tana kallon su kamar a mafarki take ganin abin, wai yanzu Nayla ta zama matar Omar, ko da wacce fuska zai karɓi auren ma oho, ko meyasa Abiy ya yiwa Nayla haka oho.

Bayan an ɗaura auren Abiy ya kalle su ya ce, "Na gode sosai da karamcin ku a gare ni, duk da baku sanni ba amma ku ka amince ku ka ƙulla aƙalar aure dani, naji ɗaɗi sosai Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan mahaifa. Sannan zaku iya tambayar kowa a garin Kaduna waye Abdullah Ahmad, in sha Allah zaku samu magana mai kyau a kaina."

Kawu Mamman ya ce, "Ni na sanka, mun taɓa yin wani taro an gayyato ka matsayin babban baƙo. Na san labarinka kaf, suma baza su rasa sani ba ai kai ba ɓoyyayen mutum bane." Murmushi Abiy ya yi ya ce, "Na gode. Sai a fara shirin tarewar amaryar nan da kwana biyu masu zuwa in sha Allah."

Kowa kallon Abiy yake yi dan gani suke kamar yana da taɓin hankali ko kuma ba ƴarsa ba ce. A haka yayi musu sallama cikin mutunci tare da karɓar number juna suka rako shi har harabar gidan yana kallon su.

Jawad suna so su yi masa magana amma ya ƙi bada fuska dole suka riƙe bakin su suka bari aje gida. Didi ce ta biyo bayan Abiy ta samu har sun fita zasu shiga mota ta ce, "Abiy." Ya jiyo yana kallonta ta ce, "Don Allah meyasa ka yanke wannan hukuncin akan Nayla?."

Abiy ya murmusa cike da takaici da ɓacin rai ya ce, "ki kwantar da hankaliki babu komai, ki fara shirin karɓar amarya ranar lahadi jibi kenan, ranar Nayla zata tare a gidan mijinta" ya faɗa yana shiga mota suka suma suka shiga suka bar unguwar.

Didi ko da ta koma su Kawu tsare ta suka yi da tambayar anya Abiy yana da hankali kuwa, Didi ta ce, "wallahi yana da shi, mutum ne na gari dattdijo ban san meyasa ya aikata hakan ba. Kuma baka ji Kawu ƙarami ya sanshi ba? Babban mutum ne mai kuɗin gaske a Kaduna, zan iya cewa kaf garin Kaduna an sanshi."

Kawu ya ce, "Nima na san shi Aisha, yana da manya-manyan store a garurun dake cikin ƙasar nan. Kawai tantama nake yi akan anya yana da hankali? In kuwa yana dashi anya ita Hauwa ɗin ƴarsa ce?."
"Wallahi ƴarsa ce wacce yake matuƙar ƙauna, kaf yaransa ma babu kamarta."
"Iko sai Allah, to yanzu shi Omar ɗin ya san labarin nan?."
"Wallahi bai sani ba Kawu, tashin hankalina bai wuce Omar ya sani ba. Ban san da wacce fuska zai karɓi auren nan ba."

Kawu ya ce, "kuma ke zaki faɗa masa ba, Haka zaki same shi ki sanar dashi zai iya fahimtar ki. Sai a fara shiri tunda ya ce jibi zata tare." Didi ta ce, "to Kawu ina Omar yaga gidan ma da zai saka amarya?."

Kawu ya ce, "wannan ba abin damuwa bane, ki san yadda zaki yi dashi, akwai gidan da na siyawa ƙaninki mai sunan Omar Baba kenan, an gyara shi anyi komai babu abinda ba a saka ba, hatta solar an haɗa 24/7. Da yake Allah bai nufa zai zauna a gidan ba kinga an fasa auren, ki lallaɓa Omar ki san dabarar da zaki yi masa sai ya zauna a ciki. Kar sunana ko sunan wani ya fito a kyautar gidan nan, ki san yadda zaki yi dashi amma kar ki ce daga hannuna ya fito. Kuma wallahil azim na bar masa kyauta, yadda na siya da sunan ɗana auren bai yu ba na barwa ɗana na wajen marigayi ƙanina Usman gidan halak malak."

Didi a sanyaye ta ce, "To Kawu, an gode Allah...." Dakatar da ita ya yi ya ce, "Aisha kar ki gode min, muje magana ta gaba." Didi ta ce, "To Kawu. Ni yanzu so nake a san yadda za ayi a tunkare shi tukunna." Kawu Yusuf  ya ce, "Aisha wannan ai aikin ki ne, mu a cikin mu akwai wanda ya isa ya tari Omar da wannan maganar ne?."

Sai taji jikinta ya yi sanyi a sanyaye ta ce, "kun isa mana Kawu."
"Ba mu isa ba wallahi, kema kin san bamu isa a wajan Omar ba. Tunda hakan ta kasance naji daɗi da kina nan, da bakya nan tsaf zai iya zuwa ƙofar gidan nan ya tara mana jama'a. Ki je ki san yadda zaki faɗa masa."

Kawu Mamman ya ce, "Aisha ni kuma in za a haɗa lefen amarya kizo ki yi min lissafi zan siyi komai in sha Allah." Didi tayi murmushin yaƙe zata yi godiya ya dakatar da ita ya ce, "kije ki tattauna da Omar kawai."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "To Kawu zan yi. Bara jama'a su ɗan ragu a gari sai naje na same shi" ta faɗa a sanyaye tana kallon su. Suka amsa mata ta shiga ciki tana tunanin dalilin Abiy da aikata wannan ɗanyen aiki.

Su Abiy sai da suka tsaya a hanya suka siyi abinci sannan suka wuce gida. Suna shiga Abiy ya ɗauki pack ɗaya na abincin yana ci ba dan yana jin daɗinsa ba sai dan babu yadda zai yi ne. Jawad kam sun kasa ci kallon Abiy kawai suke yi suna jiran ƙarin bayani, ƙarfin hali Yaya Ahmad ya yi ya ce, "Abiy meyasa ka yanke wannan hukuncin akan Nayla don Allah? Wannan ba yukunci bane, taya zaka ɗaura auren ta da wannan yaron?."

Abiy bai yi magana ba Jawad ya ce, "Abiy don Allah meyasa aka yi mata haka? Ko me ta aikata ai yarinya ce sai ayi mata uzuri a tsawatar mata, amma ɗaura mata aure dashi ba hukunci bane ba Abiy." Abiy bai ce musu komai ba ya ajjiye abincin ya tashi ya shiga ciki.

Jawad ya kalli Yaya ya ce, "wannan hukunci ne Yaya? Wannan ai lalata mata rayuwa aka yi ba aure aka yi mata ba. Ko me tayi ai wannan ba hukunci bane, sai a zaunar da ita ayi mata faɗa, in auren ya zama dole sai aura mata wani amma ba irin wannan yaron ba." Yaya cike da damuwa ya ce, "ni ban san ma abinda zan ce ba wallahi, ban san abinda ya saka Abiy ya aikata haka ba. Dan ta ce tana sonsa akwai sai a bata shi? Haba gaskiya Abiy bai kyauta mana ba wallahi." Abincin da basu iya ci ba kenan Abiy ya fito ya kalle su ya ce, "abinda ya kawo mu Kano mu yi, ku tashi mu wuce gida."

A sanyaye suka tashi suka bi bayan sa bayan sun ɗauko abincin har wanda Abiy ya ajjiye. Yaya ne yanzu ya shiga gaba wajan mai tuƙawa Jawad ya shiga kusa da shi Abiy ya shiga baya. Har zai kunna motar Abiy ya tuna ya yi mantuwa ya koma ciki. Jawad kasa haƙuri yayi ya ɗauki waya ya kira Nayla yayi sa a ta shiga, tana ɗauka kafin tayi magana ya ce, "Malama duk abinda ki ke yi a Kano ki tabbatar kin wuce Kaduna yanzu, ko me ki ke yi ki ajjiye ki wuce gida." Nayla ta ce, "Yaya J rana ta yi yanzu, driver Hajja baya nan waye zai kai ni Kaduna yanzu?."

A tsawace ya ce, "ki san yadda zaki yi ki dawo gida, in ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci sosai" ya faɗa ya yanke wayar ganin Abiy ya taho. Yana shiga motar Jawad ya ce, "Abiy mu biya gidan Hajja mu tafi da Nayla?." Abiy ya ce, "tare muka zo da ita?." Jin abinda ya ce sai ya yi shiru amma zuciyarsa gabaɗaya babu daɗi akan abinda Abiy ya yi, to babu yadda zasu yi ne dole su yi shiru kamar yadda ya ce. Fita suka yi daga gidan bayan sun bawa mai gadi abincin suka ɗauki hanyar Kaduna.

Nayla kuwa da suka je gidan Didi bata nan sai kawai suka wuce gidan Jidda, suna zaune a Jawad yayi mata waya duk sun ji abinda ya ce. Ta kalli Twiny ta ce, "Yaya J ne yau yake yi min wannan faɗan, yanzu waye zai kai ni Kaduna?." Twiny ta ce, "ke share shi, gobe sai ki tafi. Haka kawai sai yaja Abiy ya yi miki faɗa daman gashi Abiy na fushi."

Nayla ta ce, "yanayin maganar Ya J da ɓacin rai ciki sosai Twiny, ko dai naje na hau motar haya na koma?."
"Ki share shi, gobe da safe sai ki tafi." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya sa Abiy bai yi fushi da tahowa ta Kano ba, Allah ya sa ya fahimce ni ya yafe min laifin da nayi masa." Suka amsa mata da amin. Hira suke ta janta da ita amma ta kasa sakin jikin saboda bata da walwala ko kaɗan, yamma nayi suka wuce gida a motar gidan Hajja da Salma ta kawo su.
[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P021

Su Abiy da suka koma gida bai cewa kowa komai ba sama ya hau ya barsu a wajan a tsaye. Mama ta kalle su ganin fuskar su ɗauke da damuwa ta ce, "Wai ne ya faru ne? Me kuka je yi Kano?." Jawad ya kalle ta ya ce, "dangin wannan yaron Omar muka je, abin mamaki Abiy ya bada auren Nayla, dan yanzu haka Nayla matarsa ce." Mama ta wara idanu waje a zahiri, a baɗini kuma farin ciki ne ya mamaye mata zuciya ta ce, "Aure kuma? Auren Nayla da ɗan daban aka yi?."

Yaya ya ce, "Wallahi shi aka yi Mama, Abiy yaƙi faɗa mana dalilinsa, sannan kuma ya hana mu tamabaya. Yanzu zancen da nake miki an ɗaura auren su ita dashi, kuma ko sani Omaar ɗin bai yi ba, haka Nayla ɗin ma bata sani ba."
Chapter 37 · 0% Book details