Sashe 15
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Narma ta kasa sarrafa kanta akan son da take yiwa Omar, ta rame ta ɗan yi dogon wuya saboda tunani. Gangar jikinta ce kawai a England amma hankalinta da komai nata yana Nigeria.
Tana zaune cikin riga da wando masu laushi kanta babu ɗankwali ta zubawa waje ɗaya idanu. Ƙarar shigowar message taji kamar baza ta duba ba sai kuma ta duba taga daga WhatsApp ne ta buɗe tana karantawa. Ai da sauri ta kira voice call yana ɗauka ta ce, "Da gaske ka ke Dad ya saki Faruk?." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta ce, "Shikenan ina zuwa" ta faɗa hannu na rawa tana kashe wayar.
Farin ciki ya bayyana akan fuskarta a bayyane ta ce, "Dad ya saki Faruk, Faruk ya koma gida. Wayyo Allah daɗi, Allah na gode maka." Number Omar ta nemo babu wani tunani kawai ta kira voice call. Ringing ta dinga yi alamun ba a kunna data ba ta kashe wayar tare da cillar da ita gefe ta ce, "Ko ya yake? Ko yana tunanina kamar yadda nake tunaninsa?."
Najwa ce ta ƙaraso wajan ta ce, "Ya Narma ga ticket na siya mana zamu je emirate stadium kallon wasan arsenal da liverpool." Narma ta kalle ta ta ce, "Sai kin dawo, ni bazan je ba."
"Meyasa baza ki je ba? Kuma na ga Arsenal shine club ɗin da kike so, Meyasa baza ki zo mu je ba?."
"Najwa bana jin daɗi don Allah ki ƙyale ni, bazan iya zuwa ko ina ba."
Najwa bata sake magana ba ta koma ɗaki ta kira Mum, Mum tana ɗauka ta ce, "Mum Ya Narma tana gab da kashe kanta da tunani, tunda muka zo nan bata da wani aiki sai na tunani Mum. Kullum kuka, kullum cikin ganin hotonsa take tana magana ita kaɗai. Mum lamarin Ya Narma ya fara bani tsoro wallahi."
Mum ta ce, "kuma kina zama a inda take?."
"Mum bata bani wannan damar, yau ne fa take zaune a falo amma kullum tana cikin ɗaki ta kulle kanta. Har ticket na siya mana yanzu na zuwa kallon ball amma ta ce baza ta je ba, kuma Arsenal ne fav club ɗin da take supporting." Mum ta ce, "ki cigaba da jan ta da hira, in abin bata yu ba sai ku dawo kawai." Najwa ta ce, "daman ni na gaji da zaman nan wallahi" ta faɗa tana yanke wayar tana mita.
[22/09, 6:58 am] +234 906 075 3382: KRB2P009
Arewabooks@nanahaleema11
*Nigeria, Abuja.*
Lokacin da Mum ta yanke wayar Najwa kallon Sen tayi da yake jin duk abinda Najwa take cewa, cikin fusata Mum ta ce, "ana cikin wannan yanayi kuma wai ka saka aka sake shi, mu da muke so ya karya asirin da ya yi mata amma ka sake shi ya bar ma Abuja salin alin kamar wanda mu ke jin tsoro. Gaskiya Dear baka kyauta ba sam, baka kyauta min ba nida Narma, abinda ka yi bai kamata ace kayi shi ba. Ka san yadda muke ciki da Narma amma ka iya bari ya bar Abuja lafiya ba tare da wata damuwa ba, ka ga kenan ya yiwa banza."
Dad da yake jinta yana daga zaune ya ce, "Dear ki nutsu mu yi magana."
"Bazan taɓa iya nutsuwa ba wallahi, ya asirce min yarinya bata iya ganin kowa sai shi ka ce na nutsu?."
"Calm down please, ki zauna mu yi magana."
"Ina zancen ƴata tana london ta kasa sukuni saboda asirin da aka yiwa mata kana ce min I should calm down!. Wallahi dear in wani abun ya samu Narma, in Narma ta samu ciwo ta wannan dalilin, in Narma ta yiwa kanta illa ta dalilin wannan asirin da ya yi mata ba tiger ba, wallahi ko lion ne sai na ga bayan sa! Wallahi sai na saka an raba shi da numfashinsa gabaɗaya!" Ta faɗa cikin ihu tana kallon Dad da yake kallon ta.
Dad ya miƙe tsaye ya riƙe ta cikin rarrashi ya ce, "ki nutsu mu yi magana mana." Mum ta ce, "bazan nutsu ba! Duk kai ka jawo wannan abin, na faɗa maka kar ka haɗa min yarinya da ɗan daba amma ka ƙi ji. Ga abinda hakan ya haifar nan muna gani ni da kai, kuma ana ƙoƙarin samun mafita akan kuskuren da ka yi ka sake tafka wani kuskuren ta hanyar sakin sa da ka yi. Anya kaima ba asirin ya yi maka ba?."
Dad ya ce, "Nayi hakan ne saboda tafiyar siyasar mu dear. Ke kin san matakin gov nake nema, kin san yana da tasiri sosai a ɓangaren zaɓen baya. Barinsa a hannunna in labarin ya fita hakan zai iya taɓa carrier ta, sannan shima zai iya sakawa ayi abinda bazan kai labari ba. Shiyasa ana sake shi."
Mum ta ce, "babu abinda zai iya, babu abinda ya isa ya hana babu abinda ya isa ya saka ayi. Waye shi? Waye shi nace!? Ka manta da waɗanda aka yi gwagwarmaya ne? Ka manta ta yadda aka yi ka zo wannan matakin ne?."
"Ya isa dear, Dear ya isa. Zai iya taka rawar gani wajan ganin ya kai ni ƙasa." Mum ta ce, "Shiyasa ai nace a gama dashi, shiyasa nace a raba shi da numfashinsa amma ka ƙi ji. Yanzu me ka ke so ayi? Haka zamu bar Narma kenan?."
Dad ya ce, "Aura mata Ashraf zamu yi a tura shi su zauna na ɗan lokaci, in yaso daga baya sai su dawo ayi biki. Hakan shine mafita kuma na tabbatar Ashraf zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajan ganin Narma ta dawo hankalinta saboda tana sonsa." Tsaki Mum ta yi ta ce, "wannan ba shawara ba ce, ka ƙyale ni da kaina zan ɗauki matakin da kai ka kasa ɗauka, zan yi masa abinda zai karya asirin koda ba ya so, na san abinda zan yi" ta faɗa tana fita daga ɗakin da yake ya bita da kallo yana ajiyar zuciya cikin ƙunar zuciya.
•••••••
Haka Omar ya yini a gida babu inda yaje saboda baya jin daɗi ko kaɗan. Didi ce take ta hidima dashi har dare a lokacin AbdilHamid yazo. Ya yi farin cikin dawowar Omar ko babu komai Didi zata nutsu su fuskanci abinda ya ke gaban su.
Washe gari ya tashi babu laifi ya ɗan ji ƙarfin jikinsa, da ya shiga falon ya same ta tana karatun alkur'ani, da sallama ya ƙarasa ya zauna sai kuma ya tashi ya shiga kitchen ya zuba tea ya dawo ya zauna yana sha a hankali. Sai da ta kai ƙarshen aya sannan ta rufe ta kalle shi ta ce, "ya jikin?."
"na ji sauƙi. Ya ku ka yi da AbdulHamid jiya?."
"Maganar gida ce. Ni wallahi ban san ma ya za a yi ba, ya ce zai zo da makullin gidan a je a gani dan asan abinda za a zuba. Sai kuma batun kawo lefe, shi na ce kawai maza su kai gidan Kawu."
Kai ya girgiza kafin ya ce, "Allah ya kaimu."
"Amin" ta amsa a taƙaice dan baza ta yi masa maganar hidimar biki da kayan ɗaki ba a yanzu saboda yanayin da yake ciki. Kira ne yake shigowa wayarsa ya kalla yaga Narma ce ya ɗauke kai ba tare da ya ɗauka ba yana kulle ido.
Didi ta ce, "ana yi maka waya." Bai buɗe ido ba balle ya amsa mata, a lokacin wayar ta sake shigowa nan ma bai ɗauka ba kuma bai katse ba. Didi ta kalle shi a sanyaye ta ce, "Narma ce take yi maka waya?." Buɗe ido ya yi ya kalle ta ya ce, "tun jiya take kira na, ni ban san me zance ba." Didi ta ce, "gwara kar ka ɗauka ɗin ya fi alkhairi. Ka cigaba da addu'a Allah ya cire maka ita daga zuciyar ka, ita kuma sonka da Allah ya ɗora mata ya canja mata da mafi alkhairi."
Bai amsa ba ya sake mayar da ido ya rufe, baya jin daɗi gabaɗaya a zuciyarsa sai yaji kamar bai kyauta mata ba. Ko babu komai ai tana sonsa kuma mai sonka yafi wanda ya ce baya sonka. Gashi abinda yake ji a kanta a baya duk ya sire masa, ya kasa gane dalilin da ya saka baya jin abinda ya ji dah a kanta. Duk da ya alaƙanta hakan da abinda ya faru amma bai kamata ace ya daina ji gabaɗaya ba, ya ɗauka wani abun zai rage ko ya ya yake amma babu ba. Ya ajjiye batunta a gefe, ya tsallake ta ya wuce gaba dan shi giwa ce baya waiwaye, in dai har ya wuce to ya wuce kenan har abada.
"Didi!." Jin yadda ya kira sunanta sai ta kalle shi a nutse ta ce, "Na'am." Zuba mata idanu ya yi ya ce, "dama hiv ta kashe mahaifiyar mu?." Didi ta runtse ido a sanyaye ta ce, "ƙarya ne wallahi, ƙarya ce kawai aka faɗa mana dan mu ji zafi a zuciyar mu amma ba haka abin yake ba. In da ace haka ne kaima ka san da labarin bai kai yanzu bamu sani ba. Da lokacin da muke gidan su Kawu mun san labarin, tunda har basu faɗa mana ba wallahi ba haka bane Omar."
Ajiyar zuciya ya yi yana tuna irin kalaman da Senator ya yi amfani dasu masu zafin gaske a gare shi, in ya tuna kalamansa akan iyayensa sai yaji kamar duniyar tana juya masa. Yafi jin zafin zagin iyayensa da ya yi fiye da komai, ya ji raɗaɗi da ƙunar zuci wacce bai taɓa ji ba a rayuwarsa. Buɗe ido ya yi ya kalli Didi ya ajjiye kofin hannun sa ya ce, "Didi daman ashe kece ki ke ciyar dani a gidan nan? Na kasa yarda da gaske kece ki ke ɗaukar ɗawainiyata. Daman kallon da ake yi min kenan?."
Didi ta ce, "ba gaskiya ba ne Omar, ka tuna kana bani kuɗi a siyo abinda babu a gidan nan. Kaine ƙarfin yin abubuwa na gidan nan Omar bani ba, kar wannan maganar ta dame."
"Amma kafin na baki kuɗi a siya ke kin siya, saboda haka ki ke sana'a mai wahala domin ciyar dani. Tabbas abinda aka ce gaskiya ne, ban iya ɗaukar ɗawainiyar Yayata ba ta ya zan iya ɗaukar ta wata mace?."