← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 52

Sashe 16

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Didi a sanyaye ta ce, "Wallahi ƙarya ne, in ma Senator ne ya faɗa maka haka ya faɗa dan ranka ya ɓaci kawai. Omar meye baka yi min? Duk kuɗin da ka samu a kaina yake ƙarewa, kana ɗinka min suttura ka hana kanka, ka bani kuɗi ka hana kanka amfani dasu. Don Allah kar wannan ya dame ka, ƙarya ce kawai da son ɓata maka rai."

Ajiyar zuciya ya sake yi idanunsa sun yi ja sosai ya ce, "ba a taɓa faɗa min kalaman da naji zafin su a duniya ba kamar abubuwan da ya faɗa a kanki da iyayen na, ba a taɓa yi min abinda naji zuciyata na rawa kamar abinda ya yi min ba. Ya kira ni jahili ya fi a irga, tabbas kuma na san bani da ilimi boko amma na addini ina da daidai nawa, ina da karatun addinin da bana tunanin shi yana dashi. Amma daman sai mai ilimi ne akwai yake zama wani a duniya?" Ya faɗa yana tsareta da idanunsa da suka koma jajaye.

Didi t ce, "A'a, Allah yana ɗaukaka duk wanda ya so a lokacin da ya so. Baka ji hausawa suna cewa dare ɗaya Allah kan yi bature ba? Wanda ba baturen ba ma dare ɗaya Allah yake yin sa. Haka arzuƙi, mutuwa, aure duk lokaci ne dasu, Omar in yanzu rabon ka ya kira ka rufe ido da buɗewa ya fi wahala akan ɗaukakar da zaka samu a lokacin da ka amsa KIRAN RABON ka. Shiyasa Allah ya ce tashi in taimaka maka, baza ka je kan titi babar mota taho ka kwanta ka ce Allah kare ni ba, baza ka ƙi karanta komai a yayin rubuta jarabawa ba ka shiga ɗakin jarabawa ka ce Allah zai yi min ba. Dole sai ka tashi sannan Allah zai taimaka maka."

Sunkuyar da kai ya yi kafin ya ɗago ya kalle ta ya ce, "Didi!." Ta kalle shi bata amsa ba ya ce, "Daga yau zan koma irin yadda ki ke so na zama, duk abinda nake yi wanda ba mai kyau ba ki faɗa min ni kuma daga yanzu zan daina." Didi ta yi murmushin cikin farin ciki ta ce, "Da za kayi haka da ka nunawa masu son ganin ka ƙasƙanta cewa da Allah ka dogara, da zaka bawa maƙiya mamaki Omar."

"Ina jin ki."
"Omar gabaɗaya harkar daban nan zaka ajjiye ta a gefe, ka daina ɗaukar wuƙa kwata-kwata, sannan ka nutsu ka kama sana'a ka zama mutum kamar kowa. Daman ba shiga harkar mutane ka ke yi ba, ka cigaba da rayuwarka ka sake ƙarfafa addininka. Sallah, azumin nafila, sadaka, taimako ka ƙara akan yadda ka ke yi, aikin alkhairin ka ya danne na sharrinka Omar."

Ya kalle ta bayan ta gama ya ce, "iya abinda zan yi kenan?." Ta ɗaga kai ta ce, "shine kawai. Sai kuma ka koma makaranta, sannan ka shirya da dangin mu, ka bar komai ya wuce a cigaba da zumunci."

Hannu ya ɗaga ya girgiza yatsansa ya ce, "har abada na gama yin karatu, bazan sake yin makaranta ba, Har gwara ma karatun addini akwai makarantar da na gani ana yi online zan shiga kodan sake gyara lahirata. Sannan batun dangi ma ki cire shi ya koma gefe, har gwara makarantar akan dai batun waɗancan matsiyatan. Ki cire batun karatun boko dana dangi, amma abinda kika ce da farko zan yi."

Didi ta yi dariyar farin ciki ta ce, "Allah ya baka iko Omar, Allah ya taimake ka ya yi riƙo da hannunka, Allah ya kai ka matakin da baka yi tunanin zuwa ba, Allah ya sa ka taka matsayin da baka yi tunanin takawa ba, Allah ya kawo maka alkhairin da baka yi zaton samunsa ba a rayuwarka. Naji daɗin wannan canjin Omar, naji daɗi, Allah ya sa ka yi abinda ka ce."

Kallon ta yayi yana girgiza kai ya ce, "zan yi, tunda na ce ai kin san zan yi" ya faɗa yana ɗauke ido daga kanta yana wani tunani daban. Didi ta ce, "Har makarantar da kayi magana zaka yi?."
"Da ban faɗa ba kin san da ita ne?."
"A'a ban sani ba."
"To tunda ki ka ji na faɗa zan yi."
"Ka yi mana register nima zan shiga."
"To."

Didi sai murmushi take tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba, Miƙewa ya yi ya fita ta bishi da kallo kafin ta faɗi a wajan ta yi sujjada ta godiya ga Allah da ya nuna mata ranar da ta faɗi kuskurensa ya amsa har ya ce zai gyara. Duk da bai amince da batun gyara zumunci ba, amma tunda ya fara karɓar gyara ta san a hankali zai bar komai ya zama labari. Tabbas soyayyar Narma a wajansa tamkar kiran rabo ce.
[22/09, 6:58 am] +234 906 075 3382: KRB2P010
Arewabooks@nanahaleema11.

Da wannan farin cikin Didi ta yini tana ta aikin ta cikin zafin nama da karsashi. Wajan Hajja ma take so ta shiga ta bata labarin abinda ya faru amma so take yi ta gama sai ta shiga. Bayan sallar la'asar ya shigo da sallama ta amsa tana fitowa daga kitchen tana cewa, "Ina ka shiga? Ga abinci ka zo kaci." Omar ya zauna tare da ɗan kashingiɗa ya kalle ta ya ce, "na je unguwa ne."

Fitowa tayi ta zauna ta ce, "unguwar bata da suna?." Miƙewa zaune ya yi a kan kujerar ya ce, "zan faɗa miki."
"To abincin fa?."
"A'a bana jin yunwa yanzu." Didi ta ce, "zuwa jibi nake so mu je Kaduna gidan su Nayla mu yiwa mahaifinta godiya." Kallon Didin ya yi ya ce, "to" ya furta dan bai san me zai ce ba. Ya san dai bazata taɓa amincewa ba in ya ce bazai je ba shiyasa ya ce to.

Wayar ta ce take ƙara ta duba ta ce, "A'a wacce irin number ce wannan? Tun ɗazu ake kirana." Ɗauka tayi ta saka a speaker daga can ɓangaren aka ce, "Didi barka, Narma ce." Didi jin muryarta da suna ta sai gabanta ya faɗi ta kalli Omaar da ba ita yake kallo ba ta ce, "A'a Narma, barkan ki. Ina ta ganin kiran ashe kece ni ɗauka nake company ne duba da yanayin number." Narma ta ce, "ni ce. Ina kiran ki da layin ƙasar England ne shiyasa."
"Allah sarki, ya ki ke?."
"To gani dai kamar mai lafiya amma ba lafiya nake ba Didi."

Didi ta ce, "me ya faru kuma?." Narma ta ce, "Didi rabuwa da Faruk ba abu bane mai sauƙi a rayuwata ba, ban taɓa son wata halitta kamar yadda nake sonsa ba Didi. Har yanzu ban cire rai da samunsa ba."

Didi tayi ajiyar zuciya ta sake kallon Omar da ba ita yake kallo ba har lokacin amma ta tabbatar yana jin duk abinda ake faɗa, ta ce, "Narma addu'a zaki dinga yi itace maganar damuwarki, Allah ya kawo mafita ya yaye miki abinda yake damunki. Kin san duk abinda ya faru ba sai na faɗa miki ba, auren ki da Omar bazai yu ba, kafin ma aje ga maganar aure tarayyar ku ma baza taɓa yuwa ba. Tun farko na faɗa miki amma baki fahimta ba, yanzu gashi komai ya lalace. Kar ki sare ki ta addu'a, in kina da rabon auren sarabon zai kira ki a lokacin da zaki amsa bama ki san kin amsa ba."

Narma tayi murmushi ta ce, "haka nake ji a jikina Didi, jikina yana bani zan zama matarsa in sha Allah" sai muryarta ta fara rawa ta ce, "basu san wahalar da na sha kafin na samu ya saurare ni ba, na samu kansa daƙyar amma Dad ya lalata komai bayan ya yi min alqawarin bani duk abinda nake so."

"Ki yi hakuri" Didi ta faɗa a sanyaye cikin tausayinta. Narma tayi murmushin yaƙe ta ce, "babu komai Didi. Ya Faruk ya dawo gida? Ina fatan Lafiya?. Na Kira shi yafi a irga baya ɗaukar wayata, Ina so naji lafiya ya dawo amma laifin su Dad ya shafe ni. Ni me nayi masa Didi? Ban cancanci ya saurare ni ba?."

Jin ta fara kuka sai Didi ta tausasa murya ta ce, "Ba haka bane ba Narma, yana ƙoƙarin kiyaye abinda iyayenki suka ce ne shiyasa, amma ba wai dan yana ganin laifinki ba."
"To ko sau ɗaya ya ɗauki wayata ya yi min magana, na kira shi sau babu adadi amma baya ɗauka kuma san ya san ni ce. In ba laifina yake gani ba meyasa bazai ɗauka ba? Meyasa bazai saurare ni ba?."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "haƙuri dai zan ce ki yi Narma, ki ta addu'a." Narma tayi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan Didi zan yi. Ya dawo lafiya?." Sai ta sake bata tausayi matuƙa a sanyaye ta ta ce, "ya dawo lafiya lau Narma."
"Don Allah ki gaishe min da shi in yazo, sannan ki roƙar min shi ko sau ɗaya ne ya amsa kiran wayata, Ina cikin tsananin azaba da raɗaɗin zuciya, ni kaɗai na san abinda nake ji a zuciyata Didi, ni kaɗai na san zafin da zuciayata take min akan rashinsa. Ko sau ɗaya ne ya ɗauki wayata Didi zan ji daɗin hakan, koda bazai yi min magana ba saukar numfashinsa ya ishe ni."

Didi gabaɗaya jikinta ya gama yin sanyi ta sake kallon Omar har lokacin ba ita yake kallo ba amma shi kansa ta san yaji a jikinsa. Ta ce, "zan faɗa masa in sha Allah, ki cigaba da addu'a kin ji?."
"Zan yi in sha Allah. Sai anjima" ta faɗa tana yanke wayar Didi ta ajjiye wayar a gefe tana sauke numfashi.

Shiru bai ce komai ba itama bata ce ba, tausayin Narma ya gama mamaye mata zuciya, in ba soyayya ba wai Narma ce take wannan kalamai akan Omar ɗinta, in banda soyayya ina ruwan biri da gada? In ban da soyayya mai ya kai akuya gaida kura har raminta?. Kallon sa ta yi ta ce, "Omar Narma tana sonka, Allah sarki kaɗai ya san azabar da zuciyar take yi mata. Kaima na san kana sonta har yanzu, bamu san abinda Allah ya ɓoye ba baza mu yanke hukunci ba."
Chapter 16 · 0% Book details