Sashe 1
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[20/09, 8:27 am] +234 906 075 3382: KRB2P001
Arewabooks@nanahaleema11
Faɗuwar da Narma tayi a wajan shi ya ɗauke hankalin su daga kan su Omar aka yi kanta a guje ana jijjigata amma Narma ko numfashi bata yi. Hankalin su ya tashi matuƙa aka ɗauki Narma aka tafi zuwa asibiti da gaggawa. Sen takaicin duniya ya ishe shi, ji yake kamar ya je ya saka wuyan Omar a gabas ya yanka kowa ya huta. Kowa ka kalli yanayin fuskarsa a cikin su kasan baya cikin walwala, ransu duk a ɓace yake da abinda ya faru.
Sai da daddare Narma ta buɗe ido ta kalli iyayen nata guda biyu da suke zaune kusa da ita, ta kalli ƴan uwanta suma da suke gefenta. Murya a shaƙe ta ce, "Dad Faruk ya tafi ko?." Maganar da tayi ne ya saka suka fahimci ta farka duk suka kalle ta.
Sen ya ja tsaki bai ce komai ba ya fita daga ɗakin, dan in ya cigaba da zama bai san abinda zai aikata mata ba. Mum ce ta ƙarasa inda take ta riƙe hannunta tace, "Narma ki yi shiru da maganar nan mu koma gida, yanzu kina kwance asibiti ne." Narma ta ce, "Mum in na rasa shi mutuwa zan yi." Ran Mum ya ɓaci amma bata nuna ba ta ce, "na ce ki yi min shiru ko?." Narma ta yi shiru tana tuna abubhwan da suka faru kanta ya yi nauyi sosai.
Babu jimawa suka nemi tafiya gida dan dukkan su basu da nutsuwa, ganin Narman ta dawo daidai ba laifi sai suka bar asibitin zuwa gida. Babu wanda ya yi mata maganar kowa ɗaki ya shiga dan ya huta dole itama ta kwanta amma ba dan tana son yin bacci ba.
Mum ta shiga wajan Sen ta same shi a tsaye a jikin window yana amsa waya yana cewa, "kayi duk abinda ya kamata ka yi, ni fa da zan samu dama direct prison nake so a kai shi, bana son wani ɓata lokaci wallahi."
Daga cikin wayar aka ce, "Calm down Sen, ba a kai mutum prison kai tsaye ba tare da laifin komai ba." A fusace ya ce, "ba na faɗa maka har gida shaƙe ni ba?."
"Wannan ma hujja ce da za a ɗaure shi life in prison ba, kuma dole kotu ce zata yanke hukunci." Sen ya ce, "Kaga ni bana son wani long process, me za a yi yanzu?."
Ya ce, "ka bar komai a hannuna, zan haɗa masa sharrin da bazai iya fitar da kansa ba. Sunan ka ma bazai fito ba, domin zamu saka masa cocaine a jikinsa mu sake shi, in ya fita kan titi sai mu tura masa Ndlea su kama shi. Da sun kama shi zan san abinda zan yi a miƙa shi kotu, daga nan sai a yanke masa hukunci a matsayin mai safarar cocaine, kaga shikenan sunan ka bai fito a maganar ba."
Dad ya yi tsaki ya ce, "Kana ji, ka killace min shi a wani waje, sannan ka tabbatar da anyi masa horon da hannunsa ma bazai iya ɗagawa ba. Ka yi masa horon da zai kasa banbance a duniya yake ko a lahira, ka tabbatar da ya kasa koda motsa yatsun hannunsa. Su kuma sauran biyun ku barsu su tafi, ina so su je su isar da saƙon Tiger bazai sake komawa Kano ba har abada!" Yana gama faɗar hakan ya yanke wayar ya juyo yana kallon Mum da take kallon sa.
"Tun farko ai na faɗa maka kar ka haɗa min ƴata da ɗan daba amma ka ƙi ji, har ka ke ganin zai yi maka aiki da hukuma baza tayi maka ba. Yanzu ga abinda ka jawo mana, wannan babban cin mutunci ne ga family. Ƴar da na haifa namiji kamar sa ya zo har gidan nan ya ce yana so, saboda akwai ka bashi fuska da sake har yake ganin mu dashi ɗaya ne" Mum ta faɗa a fusace tana kallon Dad dan ita gabaɗaya laifin sa take gani.
Sen ya ce, "Nayi kuskure, ban ɗauka abin zai zo da haka ba, amma yanzu zan gyara komai."
"Ko ka gyara ai an riga da an aikata, yaro yazo har gidan nan kana faɗa yana faɗa kamar sa'ansa?. Sannan ya kalle ka ya ce yana son ƴarka, akwai abinda yafi wannan cin fuska ne?."
Sen ya yi shiru bai ce komai ba amma shi kaɗai ya san zafin da yake ji a zuciyarsa. Mum ta sake cewa, "yanzu ya zamu yi da Narma? Na tabbatar asiri ya yi mata, tunda ya samu damar hawa mota tare da ita ba dole ya yi mata abinda zata haukace haka a kansa ba. Ka duba yanayin da take ciki, ga zafin zuciya, ga zafin asiri, ga zafin marin da ka yi mata ɗazu."
Sen ya ce, "London zan tura ta taje ta huta. sannan maganar Ashraf zata dawo, dama tun asali shi take so, aikin asiri da ya yi mata ne ya saka tace bata sonsa. Yanzu kuma maganar zata dawo, da zarar ta huta ta dawo zan aura mata Ashraf." Mum ta ce, "ya dai gama cutar mu wallahi, ya lalata mata tarihi gabaɗaya. Wai Narma yake so, just imagine" ta faɗa cikin da takaici tana kallon sa.
Sen ya ce, "zan tabbatar masa da tayi masa nisa, zan tabbatar masa da iya furta wannan kalma da ya yi guda uku ta ina sonta sai ya yi dana sani yafi sau dubu uku, zan nuna masa ni ba kanwar lasa bane, duk isakancin da yake ji dashi na dame shi na shanye. Zan tabbatar masa da ruwa ba sa'an kwando bane, zan lalata mara rayuwa, zan saka shi ya ji zafin da naji a zuciyata, zan saka ya ɗanɗana irin zafin da ya saka Narma tana ɗanɗanawa."
Mum a fusace ta ce, "meyasa ba za a ɓatar dashi daga duniyar ba gabaɗaya? In aka kashe shi an kashe banza da wofi, zamansa a duniya tamkar cin fuska ne a gare mu." Dad ya girgiza kai ya ce, "ki barni dashi akwai, mutuwa ai mai sauƙi ce ga rayuwarsa, in ya mutu yanzu ai ban ci riba ba, ban saka masa abinda ya saka min a zuciyata ba. Sai na gana masa azabar da zai manta a wanne gari yake sannan komai ya biyo baya." Zaman kurame suka koma a ɗakin, Mum tana nata tunanin haka shima Sen ɗin shiru ya yi yana tunani mai cike da dana sanin duk abinda ya aikata a baya, tabbas da bai haɗa Narma dashi ba da yanzu hakan bata faru ba, duk kuskurensa ne amma zai gyara.
Da safe haka suka tashi duk fuska babu walwala, Narma bata fito daga ɗaki ba sai da taji duk suna falo sannan ta fito tana takowa kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Duk da kallo suka bita kafin Dad ya riƙo hannunta ya zaunar da ita kusa dashi yana kallon ta.
Gabaɗaya ta rame a lokaci ɗaya, tayi wani iri kamar ba Narman sa ƴar gayu ba, tsana da takaicin Omar suka sake yi masa dirar mikiya, suka dabaibaye masa zuciyar sa. Kallon Mahaifin nata ta yi kamar yadda yake kallon ta kafin ya ce, "Ya jikinki?."
Narma cikin sanyi murya mai ɗauke da rauni ta ce, "Dad babu sauƙi. Dad Ina son Faruk a yadda yake, Ina so na rayu dashi. Kuma Dad zaka iya mayar da Faruk yadda ka ke so, zaka iya sakawa Faruk wani abu kamar yadda ka ke buri. Ni ban damu da bashi da abinda ka ke faɗa ba, shi nake so kuma shi nake so na aura Dad" ta faɗa tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta. Ya gama gasgatawa asiri ya yiwa Narma hakan ya saka ya kwantar da murya ƙasa ya ce, "Daughter ki daina wannan maganar kinga baki da lafiya, ki bari ki samu lafiya zamu tattauna."
Narma ta ce, "Dad bazan taɓa dawowa daidai ba indai baka amince da aurena da shi ba. Dad ni na fara furta Ina son Faruk, a hankali shima ya fara sona, Dad Meyasa zaka ce bazan aure shi ba?. Don Allah Dad kar ka bari a cutar dashi kaji...." ta faɗa cikin karyewar murya tana kallon mahaifin nata. Rungumeta ya yi a jikinsa tana kuka sosai, cike da tausayi yake shafa bayanta dan ya san ba yin kanta bane aikin asiri ne.
Nabil ya ce, "zai biya bashin asirin da ya yiwa Narma, Dad bai kamata a bar shi ba" ya faɗa cike da damuwar halin da take ciki. Narma ta ɗago daga jikin Dad ta kalli Nabil ta ce, "ni bai yi min asiri ba, ni ce na dinga bibiyarsa har sai da ya fara sona. Ba asiri ya yi min ba, haka kawai nake sonsa. Najwa ta ce, "daman haka zaki tunani ai, haka zaki ɗauka babu abinda ya yi miki dan ba yin kan ki bane, ya saka miki soyayyarsa zuciyarki ta hanyar asiri, ke bazai fahimci ba asiri bane ba ai.."
Narma ta kalli Dad ta ce, "Daddy kana ji suna cewa asiri yayi min ko? Kuma ba asiri ya yi min ba Dad, ni ina sonsa ne kawai. Har yanzu ina ƙaunarsa, shi kaɗai nake so na aura, in ba shi ba ni bazan auri kowa a duniya ba zan mutu a haka. Dad Ina ka saka aka kai shi?." Bai bata amsa ba ya kalli Najwa ya ce, "Najwa ki shirya zaku tafi London this week."
Narma ta ce, "Dad babu inda zan je, babu inda zan je na bar Faruk ɗina a Nigeria. Ni dashi zan rayu, aurensa nake so nayi da shi kaɗai zan iya rayuwar duniya. Dad in kace bazan aure shi ba zaka iya rasa ni! Zan iya mutuwa na bar muku duniyar gabaɗaya." Babu wanda ya iya tanka mata a cikin su, tausayi take basu gabaɗaya sun san aikin asiri ne ba yin kanta bane.
Mum ta taso ta riƙe ta tana rarrrashi itama kuma tana kuka sosai. Mum da kanta ta bata tea ta sha, sannan ta bata maganinta na jiya ta sha, ta kaita ɗaki ta kwnatar da ita a kan gado tana shafa kanta. Narma sai magana take yi ita kaɗai idanunta a rufe kafin bacci ya ɗauketa.