← Book details Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 62

Sashe 6

Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihu zata fasa ko barin wurin zata yi ta koma cikin jirgin ya maida ta germany,rasa abin yi tayi,yanzu har a nan din ma babu wanda zai nuna ya san da ita bare ya nuna mata damuwar sa a kan ta bare a kai ga ana ririta ta ana tambayar ta nata lafiyar da rayuwar,a yanzu din ma still fifi ce ba ita ba?..

Take wani irin mugun tsana da kiyayya ya taso mata wanda a kan yar uwar ta duk wadannan abubuwan suka ta'allaka,ita shikenan haka tata rayuwar zata cigaba da tafiya..

Bata ida tunanin zucin ba ta ji su suna fadin Mufida zo mu tafi mun san kin kwaso gajiya ga yunwa...

Tun da Hamida take bata taba sanin tana da wani mummunar fanni a zuciyar ta mai karfi da yake kamar ya rinjayi daya kyakyawar fannin zuciyar ta ba sai yanzu dan kasa rike hawayen ta tayi sai da suka fito kuma ta kasa goge su sai juyawa da tayi ta basu baya tana mai warware nadin mayafin da tayi a kan ta dan ya taimaka wurin boye halin da ta shiga...

Yanzu Tsakani da Allah duk cikin su babu wanda zai tuna da wata wai Hamida? duk hankalin su na a kan Mufida kamar ita kadai ce mutum daya cikin zuri'ar su...

Kasa natsuwa Khalid yayi dan ba karamin dauke mai hankali fifi tayi ba musamman ganin irin shigar ta da yadda ta rinka exchanging tambayoyin da ake mata hakan ya bashi tabbacin ita din kamar shi ne
wato mace ce mai son rayuwa da faram faram bata da dagon kai da daukaka kan ta fiye da wasu halittun...

Tun a nan airport din Khalid ya sallamarwa kan sa ya sami abokiyar tafiya dan da alama ba iya son life kadai take da shi ba wanda shima yake da shi ba,hatta wasu dabi'un ta yana ganin zai zo iri daya da nasa dan haka ya dada saukar da kan sa fiye da yadda ya saba yi a cikin family din su...

Baki daya sun juya da zumar shigewa mota dan su kai gida fifi ta huta,shaf sun manta da Hamida har aka gama kwashe kayan fifi aka saka cikin booth itama zata shige ciki amma ganin kamar babu mutum daya cikin su sai ta tsaya ta hau dube dube
A nan cikin motar kuwa Ammy ce ke kiran sunan fifi akan ta shigo su tafi amma hankalin ta na ga yar uwar ta da ta hango ta chan tsaye..

Karasawa tayi gare ta ta dafo kafadar ta cikin farin ciki game da yi mata magana cikin yanayin jin dadin da take ciki..

"Hamee kin ga yadda su Ammy da Hajja ke murnar ganin mu kuwa,zo mu tafi gida dan duk mu suke jira "murmushin yake Hamida tayi sakamakon gama sauraron zantukar yar uwantan na wai su Ammy da Hajja na murnar ganin su
bayan baro baro ita kadai suka nuna a matsayin nasu yayin da ita aka ware ta kamar ba tare suka zo duniyar da ita mafi soyuwar nasu ba...

Kamar ba zata juyo ba sai daga baya ta juyo da murmushin da ya fi kuka ciwo zuciyar ta kuwa shake yake da kiyayyar yar uwar nata da take ma kallon katanga ce ma farincikin ta dan bayan ta karbe zuciyar daddyn su da na Ammy da Hajja har wanda take ganin Allah ya kawo mata shi shima fifi ta dauko hanyar kwace mata shi
Shin wai ita laifin me tayi ne da babu masu son ta da damuwa da ita ne?
menene aibun ta da bata samin kulawar kowa sai yar uwar ta kadai ke samu,shin ita a haka zata yi ta rayuwa komai nata fifi na samin sa ba tare da ta nema ba?..

Hankalin ta kamar baya jikin ta haka ta rinka bin bayan fifi har suka zo wurin motar wanda sai a sannan Ammy ta tuno da Hamidar amadadin ta ji wani iri ko damuwa batayi ba sai ta ce..

"Wai dama Hamida baki shigo cikin motar bane kika tsaya a waje kamar ba jinin ki kika hadu da su ba?..wannan tambayar ta Ammy ta kara tabbatarwa Hamida shikenan wani bakin cikin zata kuma fadawa ciki bayan wanda ta baro a germany...

Gyada kai kawai Hamida ta iya yi ta shige cikin motar ta zauna a kujerar baya yayin da fifi ta shiga na gaba,da so samu ne daga Ammy har Hajja so suka yi fifi ce a nan inda Hamida take amma ganin kamar ita ce ke muradin zama nan kusa Khalid sai suka bar ta dan kar su saka ta yawar magana...

Wani abin bakin cikin da ya sa Hamida jin zaman motar ya gundire ta taji ta matsu su zo gidan ta kebe ko zata sami sanyin zuciya shine,ita ce a tare da su a bayan seat din motar amma kaf hankalin su na a kan fifin ne
kowa sai son nuna mata so da kauna yake yi ta hanyar tambayar ta akan karatun ta,akan raywarta akan lpyarta a nan kusa da fifi kuma Khalid ne yake ta sakar mata murmushi yana nuna mata kulawar sa shima ta hanyar tambayar ta "if she will be comfortable da zaman nigeria din...

A haka har suka iso babbar gidan dake dauke da different parts ginin duplex mai ban sha'awa saboda tsarin da aka yi ma gidan kadai abin a zo a gani ne,wannan gini ya sa fifi kasa boye kyawun da gidan ya mata ta fitar da shi ta hanyar furta
"Wow,nice house"nan take kuma aka maida hankali hade da ba maganar nata muhimmanci..

Sai nan nan ake ta yi da ita har suka shiga daga cikin gidan inda nan ma wata duniyar ce abin kallo,mai aiki aka kirawo akan ta zo ta kwaso kayan fifi dake booth dan a kai mata wata killatacciyar dakin da aka gyare sa musamman saboda ita nan kusa da na Ammy da site din hajja..

Ana shigo da kayan ne Hamida dake tsaya a matsayin batacciya tayi ta kallon su har suka gama shigewa da kayayyakin fifi ciki
Khalid ne ya fito dan gyara parking din motar sa sai a sannan ya ankara da Hamida...

Yace."Ohh no"da dan sauri ya karaso gare ta yana furta
"Hamida ki yafe ni ban nuna maki hanya zuwa ciki ba ko?kiyi hakr yar uwar kin nan is so attractive,waidama dagaske ku yan biyu ne?dana ganta hankali na duk ya koma gare ta shi yasa na manta in nuna maki hanyar shiga cikin gida im deeply sorry"..

Wani fushi me hade da Faduwar gaba ne ya riske ta toh me yake nufi da yar uwar ita is attractive kuma?mswww fifi fifi fifi and ffi again,ji tayi kamar ta rufe idanun ta ta bude ta ga bata nan cikin gidan...

Janyo mata trolley din ta yayi zuwa ciki yana mai dan jan ta da hira,gabadaya zuciyar ta na ayyana mata cewa kar ta sake Khalid ya kufce mata sabida fifi wannan kuma nata ne ba zata barwa Mufida shi ba,dan duk cikin su shi kadai ya dan nuna ma ya san da ita...

Wani babbar bacin rai dataci karo da shi kuma shine ganin hanyar dakin da aka kai ta nan kusa da wani new abandoned room da yake shiru shiru kamar babu kowa sai ita kadai...

Dannewa haushin ta tayi Bayan ta mai godiya garin boye damuwar tane yasa tayi saurin rufe kofar dakin da key ta jingina bayan ta da kofar tana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya akai akai wasu zafafab hawayen kunci na diga,jin kamar zuciyar ta zai fashe at any moment ya sa ta dauko karamar jakar ta ta hau lalubar maganin da Dr Fatima Yonas ta bata wanda dama kullum in ta tafi ta fadi mata damuwar ta shi take bata ta sha,bude robar maganin tayi ta zuba guda biyu ta hau nemar bottle water din da ta sha a jirgi ta rage,tana ganin sa ta bude bakin murfin ta jefo maganin ta bi da ruwa...

Gadon dake gyare a dakin ta hau ta kwanta a kai idanun ta na kallon gefe daya hawaye na silalo mata har bacci ya dauke ta bata sani ba.
#Mamuh*_Mamuhgee_*
_*Zafafa biyar na kudine ka nemi wannan numbern ka biya kudinka ko katinka*_
07067124863
09032345899
A nan fannin su Fifi tunda ta shigo cikin dakin nata da ya sha kayan alatu taji sam takasa zama dan tamkar wata sarauniya haka aka tsantsara mata dakin sai da ta karewa dakin kallo ta yaba kyaun sa hade da maimaita kalmar "_wow cancadi"_.

Cire kayan jikin nata tayi ta nufi hanyar bandaki dan watsa ruwa,nan ma duk abubuwan bukata an tanadar mata wanda diya mace da ta amsa sunan ta mace yar gata ke alfahari da shi,haka tayi wankan a karkashin shower ta gama ta fito daure da fari kal din towel..

Sallah ta fara gabatarwa sannan ta hau kan kujerar gaban madubin ta,dama tayi tunanin jere cosmetics din ta gaban madubin ne amma zuwan ta dakin sai ta ga wadanda aka jere mata ma sun dame nata sun sha dan kuwa kaf babu cosmetics din da suka fito daga wani kamfanin kwalliya dake african
hatta jam baki da hoda duk products din La pariso ne daga kasar Persia hka komai suka fito ras dan a jeren su suke suffar su daban da na kasar nan..

Nan ma sai da ta yaba da kyaun koma ta kuma kara yarda da kaunar da ake mata a cikin zuri'ar nasu,lallai duk soyayyar da tayi tsammanin samun shi daga gare su ya wuce yadda ta tarar dan tun a wurin dauko su ta gasgata hakan..

Kwaliyyar ta ta cancan
a mai daukar hankali dama akwai kyaun sai ga adon zamanin da ta dora a fuskar nata me sanyin haske..

Duk dakin nata ya gama amsawa da kamshin designers perfs din ta na matron daga haka ta saka suturar ta irin ta kullum bata canza ba wato shigar kananan kaya riga da wando ta kamfanin Dior sai ta dau kimono deep red ta dora a sama hade da saka head hoodies kalar rigar cikin da ta saka,flat foot wear ta saka ta dauko wayar ta cikin kazar kazar da karfin jiki ta fito da nufin tambayar inda yar uwar ta take..
Chapter 6 · 0% Book details