← Book details Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 62

Sashe 48

Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A Zaune ta tadda wata mata a daya daga cikin kujerun falon sanye take da wa'insu hadaddun riga da skirt na Atamfa English Aura wax wani irin qamshin turaren Arabians na tasowa daga cikin ahankali Yana gauraya palon.
ganin kyakkyawar dirarriyar mace a zaune cikin palon saida yafadar ma Fifi da gaba duk dama bata san ta ba,dan karamar ajiyar zuciya ta sake saita dake takarasa shiga cikin falon tanajin wani rawar jikin sanyi na shigarta da tsantsar tsoro da wani tauri nason danne mata zuciya ta kakalo murmushi harta karasa inda Muhibba din take zaune tana pressing phone dinta, "asslm alaikm Ina yini" shine abunda Fifi tace a taqaice tana sake kallonta cikin tsananin sarewa da faduwar gabanta dake tsananta,
Kallonta ta sake dagowa muhibba tayi cikeda da qare Mata kallo tana qoqarin danne abinda ke taso Mata gameda fifin sbd Babu tantama wannan itace mufeeda wadda ta auri Marshall dinta Wanda ya kasance nata ita kadai....itadai Fifi murmushi tayi dan she don't really care
Wucewa room dinta tayi Muhibba tabi bayanta da harara mai zafi.
#Mamuh
[8/6, 10:58 PM] Miss Xoxo: *29*
5am ta farka da face dinshi tafara tozali sosai ta wani kafeshi da ido tana karewa face dinshi kallo soyayyar shi na huda duk wani gabobin jikinta har batasan sanda tasaki wani murmushi ba hade dakai hannunta tashafa gefen face din nashi, abunda bata saniba tun farkon tashin ta shima yatashi sai jin hannun shi tayi akan nata hannun sai tayi saurin zaro manyan idanunta hade da sauke su akan face dinshi dayake aika mata da wani rikitaccen murmushi me ma'anoni da dama saurin rintsa idanunta
tayi tana boye face dinta a jikin pillow,
a hankali yakai hannun shi kan lips dinta yana shafawa lips dinta yana daya daga cikin abunda yafi birgeshi da ita Duk dashi komi nata birgeshi yakeyi, cikin yar karamar voice dinta tace, "it's already late lokacin sallah yayi" lips din nata kawai yatsirawa ido sabida yanda take motsa bakin kamar ba daganan maganar tafito ba,
"I know" shine abunda yafada hade da daukan ta cak yakaita bathroom a tare sukayi wanka suka tsaftace jikin su still da zasu fito daga bathroom din daukar ta yayi yafito da ita yadireta akan gado, sannan yace mata
"pray nima zanje na shirya nayi nawa sallan" nodding kanta kawai tayi tana wasa da fingers dinta harya fice daga dakin saita tsinci kanta da sakin wani murmushi tabbas yanzu kam tagama yarda da soyayyar Marshall yagama kama Duk wani sashi na jikinta a hankali tamike daga kan gadon takarasa gaban wardrobe tasanya hannunta guda biyu tabude inda long abayas dinta suke tacuro wata purple color me manyan design a gaba tasaka hade da daukan hijab sannan takarasa ta dauki prayer mat tashinfida ta tada sallah,
Bayan 30min Marshall yashugo dakin zaune ya tadda ita akan prayer mat tana azkar kallon ta kawai yakeyi yanajin wani shauki akanta he loves her so much saida yakusan 5min a tsaye sannan yakarasa shiga cikin dakin yamaida door din yarufe karasawa yayi inda take hade da samun waje a bakin gado yazauna yana kallonta atare suka shafa addu'an sannan ta dago takalle shi
suka sakarwa juna murmushi cikin yar karamar voice dinta tace
"Good morning" saida yakai hannun shi yakama mata nata hannun sannan ya amsa da, "Morning mon amour, how's ur night?" sosai taji dadin sunan daya kirata dashi shafa tafin hannunta daya keyi shiya hanata amsawa dawuri dan haka saida ta dauki lokaci sannan ta amsa da
"Alhamdulillah dafatan kaima katashi lafia" takare maganar da dan dagowa tana kallon shi ta wutsiyar ido,
bata ankara ba saijin mutum tayi ya sunkuceta yayi kan gado da ita saida yakwantar da ita sannan yacire mata hijab din dake sanye a jikinta ya ajiyeshi a gefe guda sannan yacire mata long abaya din a cewarshi abayan zata takura ta itadai idon ta yana rufe har shima yacire nashi jallabiyan ya ajiye agefe sannan ya janyota zuwa jikinshi hade da rufe suda blanket, yafara wasa da long hair dinta dayasha gyara harshen shi yakai cikin kunnanta yana latsawa a haka wani baccin yakara daukan ta,
8am suka farka a tare suka shiga bathroom sukayi wanka half gown tasaka mara hannu milk color saita zubo da gashin kanta har gadon bayanta sosai tayi kyau Duk dako powder bata shafa a face din nataba sai kalolin perfumes data feshe jikinta dashi tana gamawa tawuce kitchen cikin 30min tagama hada musu abun breakfast,
Arabian meal tahada musu Wraps, sandwiches and manakeesh tana son kalolin abincin larabawa sosai shiyasa ta iya dukkan nau'o'in abincin su, anan dinning table na kitchen din ta jera komi tana juyawa zata fita daga kitchen din Marshall nashugowa sanye yakeda kananun kaya black jeans da white T-shirt yayi kyau sosai har batasan ta kafeshi da idanu ba saida yakaraso gabda ita sannan tayi saurin sunkwi da kanta tana sakin murmushi me cike da ma'anoni dayawa ita kanta ta shaida Marshall hadaddan namiji ne ita kanta tasan tayi sa'an samun gwarzon namiji kamar Marshall tana kuma jin shauki sosai a kansa,
Hannun sa yakai kan face dinta yashafa hade dacewa
"You look so cute Mon amour I like ur dress" saida takara murmusawa akaro na biyu sannan tace, "I like urs to" sannan tayi saurin karasawa taja kujera tace, "Seat" baiyi mutsu ba yakarasa ya zauna saidai Duk abunda takeyi idanun shi yana kanta harta kammala serving dinshi ta ajiye mai komi a gaban shi sannan tasaka nata taja kujera ta zauna,
saida yakalli Breakfast din sannan yakalleta sai yasakar mata murmushin gefen baki sannan yace, "so you know how to cook Arabian meals?" saida takai cinnamon tea bakinta tadan kurba sannan tayi nodding kanta tace, "Arabian Meal yana daya daga cikin favorite dina I will cook Arabian meal for dinner if you like it" tayi maganar da dage mai gira saidai kanta a duke yake,
"yeah I like it bakisan ina son abincin larabawa ba" hira sukeyi har suka kammala cin abincin a tare suka wanke dishes din suka maida komi inda yake sannan ta goge kan dinning din, yana rike da hannunta suka fito daga kitchen din a three seater suka zauna sai tayi pillow da cinyar shi suka fara taba hira kadan kadan anan yake kara sanin halinta itama tuni tagama fahimtar halinsa sabida anan zaman da sukayi ta fahimci yanada dadin zama sosai kuma baida matsala,
A cikin yan kwanakin wani shakuwa ne me karfi yakara shiga tsakanin su dan tuni Fifi tazubar da Duk wani abu tafara nunawa mijinta tsantsar soyayya shima anashi bangaren hakane dan har mantawa sukeyi da akwai wa'insu mutane a duniya bayan su sabida zallan soyayyar dasuke nunawa junan su.
#Mamuh[8/12, 12:04 PM] Nadady: *31*
Turo kofar tayi a gajiye tana maida numfashi Bata jima ba ta nemi waje a gefen gadon ta xauna a kasale,fuskar matan ne yaki fice mata arai wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki Wanda batayi tsammani ba.

A Sashen su ammy saheeb ya jima by 8pm kusan kowa ya fito za'ayi dinner Allah Allah Fifi take ta samu damar ganawa da su ammy gashi har cikin ranta take matukar jin muradin ganin hamidarta.

Ayanzu ji take kamar Zuciyar ta yayi sanyi,wani sashi daga abubuwan da suke yawan damun ta game da tarayyar su da hamida ba laifi sun ragu mata,bathrum ta shiga tayi wanka kasalan data ke yawanji shi ya sa ta sanya doguwar Riga pure red material and masa design da wild rose hipup belt wanda ya Dan sake ta yau batayi wani kwaliya sosai ba
Babban sashen gidan ta nufa inda Tasamu duk an zazzauna a dinning wani sanyi ne ya mamaye Zuciyar ta ayayin da take kallon su kusan kowa fuskan sa dauke da murmushi musamman hamida da Khalid Wanda Babu wani Abu daya rage ayanayin su na nuna tsananin so da shakuwa dake wanzuwaa a zukatansu.

Purple atampa ta sa Mai kyau Wanda ya dau kalar fatan kusaan kala daya da tsadadiyyar yadin vice chair man Wanda ya amshe jikin Khalid ya masa kyau sosai Shima.

Agefe da shi ammy ne da hajja wani
murmushi me sanyi ne ya kufce mata ji tayi kamar taje ta rungume su Dan bakaramin zazzafan kewarsu takeji aranta ba,a hankli ta maida kallon ta kan saheeb Wanda kallo daya ya isa yasa kasan bai Saba zaman cikin su hakanan ba dago kanta ke da wuya caraf Suka hade idanu da muhibba agefen sa irin kallon datayi mata yasa tayi saurin dauke kai gyaran murya tayi sannan ta karaso ciki a yanayin fara'a da basarwa.

" Salam alaikum"
Tace da muryan ta na da can Wanda shi kowa ya fi Sanin ta dashi, hamida ce ta soma juyo ta kalle ta cikin dakakkiyar murmushin da ya kufce mata baxata
Ammy ce ta soma mikewa sannan Hajja tabi bayan ta wani rungumar ta sukayi atare ayayin da suke gaisawa
Fifi Fifi tuni waje ya kaure da sabuwar surrutayya.

Saheeb ne kawai baice uffan ba"fifi kuwa har ta xauna Bata wani samu cikakkiyar nutsuwa aranta ba Dan rasa gane inda zata ajiye tunanin tatayi,wani bangare yanaga hamida wani Yana ga mijin ta saheeb da matar sa dataa Sha uban kwalliya tana serving kowa a nutse wacce Babu alaman kasawa ko yaranta a fuskan ta.

Normally wajen ya dau shiru kowa ya nitsu ya maida hanklinsa akan dishes dinsa ana hira sama sama,Banda hamida data fiye bada hanklin ta a kan Khalid kadai Dan in ba shi yayi magana ba Sam Bata cewa komai.
Chapter 48 · 0% Book details