← Book details Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 62

Sashe 28

Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni marainiyace gaba da bayana Banda kowa aduniya tunda na rasa mahaifiyata sbd nasan ita kadaice tasan ciwo da zafina bazata taba wareni kamar Mara galihuba,
Banda kowa Banda komai I have no other choice than to fight for myself Kota wace hanyace Koda kuwa ta hanyarda bai dace bane sbd kune kuka bani wannan choice din,
ohh Mufida kin gama sace min komai na duniyar nan kin
wace min komai na rasa me na tare maki kika za
i yi min haka"!!a
an tsawace Khalid ya kira sunan ta
"Hamidaa just shut up"!!itama a tsawace ta mayar mai da
"No ba zan yi shiru ba,gata nan Mufida ce silar faruwar komai da yake faruwa da ni a rayuwa ta,she stole everything for me and i don't want to forgive her"!!hawaye ne cike taf a idanun Mufida jin zafaffan kalaman da Hamida ke fa
a mata..
arasowa kusa da su tayi ta tsaya suna fuskantar juna ita da Hamida sai da Mufida ta sauke wata nunfashin kukan zuciya mai nauyi sannan ta ce cikin tsananin rawar murya da rashin
arfin gwiwa ta ce
"Hamida ina son sanin asalin abinda na maki a iya rayuwar mu da zaman da muka yi ni da ke"!!wani irin kallo Hamida ta bi fifi da shi sannan ta hau yi mata magana cikin fa
a da haushi..

"Yanzu zan fayyace maki asalin abin da kika min a rayuwa wanda bai da bambanci da ba
in ta
o duk da na so _
aunarmu_ ta
ore amma kika san yadda kika yi kika datse wannan
aunar tamu"!!kuma yi mata wata tambayar fifi tayi gaban ta na fa
"Hamee ta yaya na datse _
aunarmu_"?..

"Ta ko ina Mufida,Mufida kin mamaye min komai,soyayya,kulawa,rarrashi d
auna duk kin mamaye komai kin ri
e,ni ba mutum ba ce?ban dace a so ni bane?ban da
ancin samin gata ne?ke ka
ai ce mutum mai jini a jiki da kika cancanci gata?Mufida tun da muka taso da zuciya
aya na ri
e ki a matsayin
ar uwa ta ta jini ba
ar uwar dangantaka ba,tun yarintar mu Mufida kika fara
wace min abinda nake so,attention
in daddyn mu duk ke kika samu ni ban samu ba ban yi complaining ba,karatu ni ba a maida hankali akan nawa ba ke har special classes ake baki a gida ni kuma ko oho dan an fi
arfi na ni ban da gata,abincin ki sai an
ana kafin ki ci gudun kar ki ci ya maki illa ni kuma kai tsaye ake bari na na ci abincin haka,sutura sai wanda kike so kike sakawa kan ki tsaye ba a maki gyara bare a hana ki ni fah?idan zan saka wanda rai na ke so toh sai daddy ya maida ni in canza zuwa wanda ran sa ne ke so i never complained,soyayya da kafa kafa da ake yi da ke kar ran ki ya
aci Mufida ni bana samu ni ban ta
anar sa ba,kaf su Ammy da Hajja da ke suke magana in suka kira a waya dan ke ce tasu ni ko daidai da rana
aya ban ta
a ganin kiran su ba ni ba mutum ba ce?ranar da muka iso
asar nan imagine wai hankalin kowa akan ki ya komo ni dake tsaye an manta da ni ba a san ni ba sai ke,wai fah har wucewa aka yi da ke aka shige mota za a tafi a bar ni ana ta maki wasa da dariya ana gwada maki soyayyar da family ke nunawa
an su da
an uwan su,mun dawo gidan nan aka kai ni wani irin pit wai
aki aka ce shine nawa naki kuwa kamar ta princess Cinderella komai an tsara maki dan ke ce ka
ai aka sani ake considering a matsayin
iya,abinci sai an tabbatar wanda ran ki ne ke so sannan za a girka kuma ba a ci sai an tabbatar kina nan za a jira ki sai kin zo sannan a ci ni fah?wa ya damu da ni wa kuma ya san ina raye bare a ba ni abinci,dawowar mu
asar nan ke ka
ai ce kika rin
a experiencing soyayya da
aunar family
in mu ni ban samu ba,masoyi na abin alfahari na da nake muradin aure kafin in aura shima aka nemi a baki shi dan ni ban dace da shi ba sai ke tunda ke ce kika nuna soyayyar ki gare sa a fili,auren namu ma a sace aka
aura sa dan kar soyayyar ki da kulawar ki ya sami tangar
a we ran away,muka dawo muka yi bayani a tunanin mu za a yarda da auren amma sai aka juya mana baya aka
au fushi da mu dan mun yi tempering da tunanin ki,babu wanda ya damu da mu a gidan nan daddy,Ammy da Hajja duk babu wanda ke sauraron mu akan karon farko da na tashi nayi standing ma right
i na,ni ce wacce bata dace da jin da
in rayuwa ba aka
au wani a matsayin wanda za a ba ni tsoho mai mata wanda ni da ke duk mun san irin mijin da nake so,a lokacin da aka ce za a ha
a ni aure da yaya Saheeb Mufida kika maida ni abin tsokanar ki safe rana dare baki tunanin negative impact
in da tsokanar ki ke min a
walwa ta kawai ana nuna maki so and you think ke
in angel ce that deserves everything right?muna nan ni da ke Ammy ta aika aka kwashe duk kayan ki dake sashe na aka maida maki ni kuma aka kwaso nawa aka kawo min,ni da ke
in ba abu
aya bane?ba uterus
aya muka zauna ba?ba rana
aya aka haife mu ba?komai naki ba nawa bane?Ammy ta kawar da fuskar ta akan hakan ta min abinda ta min dan ni ba mutum ba ce i never complained,now miji na ya siyo abu na gani na ce ina so ya bani amma ya hau jayayya da ni akan abinda nake tunanin ina da iko da shi ashe still ban tsira ba Mufida kina nan kina bibiya ta da farinciki na kina yun
urin
wace min,for goodness sake Mufida me zan maki ne a rayuwar nan dan ki rabu da ni hakan nan in ji da
in sabuwar rayuwa ta??uhum?tell me please"!!hawaye ya gama
atawa Mufida fuska kaca kaca haka Hamidar mai magana itama fuskar ta ji
e yake da hawaye sakamakon tuno da irin rayuwar
inci da tayi a baya all because of Mufida..

Numfasa fifi tayi tana kuma matsawo kusa da Hamida ta kawo hannu ta ri
o ta tana tambayar ta murya a karye.

"Hamida yaushe duk wa
annan abubuwan suka faru?ban sani ba baki sanar da ni ba ban ta
a gani ba,Hamida all these happened amma baki tsayar da ni kin sanar da ni ba?why"?fizge hannu Hamida tayi ta amsa mata.

"Yaushe na sami lokacin sanar da ke?kina da lokaci na ne?soyayyar family
in mu ya mamaye ki baki da lokaci na baki ta
a lura da yanayi na ba ta yaya kike tsammanin zan iya tsayar da ke in nuna maki wannan abin?already akwai third party a tsakanin mu Mufida tell me how did you think i have been feeling lately all those years"!!kuka sosai Mufida ke yi Khalid kan sa a
asa Hamida kam hawayen ne ka
ai ke fitowa amma babu kuka tsantsar
acin da ran ta ke mata...

Mufida bata ha
ura ba ta kuma matsowa ta ri
o hannun Hamida tana kallon ta ta fara magana da sansayyar murya..

"Amma Hamida for once kin ta
a tunanin kira na ki fa
a min ni da ke?Hamida all my life na yi sa ne ina so maki farincikin rayuwa kamar yadda kike so min Hamida ban ta
a kawowa a rai na wannan kulawar da ake ba ni yana ta
a maki zuciya ba,ban san ana treating
in ki a haka ba,zuciya ta da tunani na bata ta
a kawo min ana
ata maki irin haka ba tun yarintar mu har girman mu,Hamida ban san irin rayuwar da nake yi kike so ba believe me i swear,Hamida kina ganin kamar da niya nake
auke kai na akan ki??no, Hamida ban san halin da kike ciki ba,har zuciya ta ban san kina jin zafin wannan abin ba,Hamida ban ta
a lura ba Allah ne shaida na ban ta
a lura da yanayin rayuwa ta mafarkin ki bane,Hamida komai nawa naki ne komai naki nawa ne,ki yafe min na maki katsalandar a rayuwar ki soyayya da kulawar daddyn mu Ammy da Hajja duk na tara a kai na ni ka
ai ban bari kin mora ba Hamida ki yafe min am so sorry and i promise to make it up to you Hamee tun yanzu zan sanar da su Ammy da Hajja su canza su daina saka ki jin irin wannan feelings
in am coming"!!?duk a ru
e take maganar zata juya Hamida ta wani finciko ta a hasale ta ce
"Stop this i don't like it,ki daina wannan pretence
in i hate liars and pretenders,Mufida duk wata so da zai fito daga wurin su Ammy,Hajja da daddyn mu a
ashin alfarmar ki bana so ki je ki cigaba da more goodies
in ki all i want is you to leave me and my husband alone na ro
e ki Mufida ba dan hali na ba na ha
ura da jin da
in family
i na dan na san ba zan samu ba sai a dalilin ki ni kuma bana so dan haka ki rabu da rayuwa ta da na miji na please Mufida"!!!a yanzu sosai kukan Mufida ya fito sarari ta kasa
oye sa,zafin da take ji a zuciyar ta ya sa ta kasa tsayawa ta juya da zumar kawa sashen Ammy amma sai me..

Ammy ce da Hajja ke share hawaye suna jan hanci abinda ya kuma girgiza Mufida kenan dan ta tabbatar suma sun saurari abinda ya faru sai kawai ta
arasa ta fa
a jikin Ammy tana matsanancin kuka tana kuma nanatawa Ammy abinda ya faru Ammy ba abinda take yi sama da kuka mai sauti,hankalin ta in yayi dubu ya tashi bata ta
a kawo maltreating Hamida suke yi ba da soyayyar da suke nunawa Mufida..
Chapter 28 · 0% Book details