Sashe 10
Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar marar gaskiya haka tayi ta sanda tana bin hanya a hankali har ta zo kofar dakin nata ta ja ta tsaya ta hau bubbuga kofar a hankali tana kiran sunan ta a hankali kamar bata son a ji ta..
Sai da ta dan jima sannan ta ji an zo bude kofar dakin,ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala dan bata so a zo a riske ta a wurin a fara jero mata ka'idoji dan ta zo da sassafe tada diyar gwal..
Ganin Hamida ce sai ta kuma murtsike idanun ta tana mata kallon mamaki dan bata fiye ganin Hamidar ta farka da sassafe haka ba..
"Lafiya me ya faru Hamee"?tura ta ciki Hamida tayi itama ta karasa ciki tana maida kofar ta rufe sannan ta jawo hannun fifi ta rike cikin nata suka samu wuri a kan gadon fifin suka zauna...
Kallon kurilla Hamida ta mata tana ta nazarin yadda zata kasance a tsakanin su bayan ta gama fada mata abin da ta nufo ta da shi..
Ganin kallon yayi yawa sai fifi ta tambaye ta ko lafiya,sai Hamida ta sauya fuska zuwa kalar damuwa ta saka idanun ta cikin na fifi sannan ta fara magana kamar haka..
"Fifi na matsala ce ta dumfaro ni babba amma ban san ya zan magance wannan matsalar ba, tun jiya toh bayan tafiyar ki sai na kasa samo mafita amma hankali na ya kawo min ke,tuno da karfin gwiwar da kika bani nasanar da ke matsala ta sai kawai na yanke hukuncin tunkarar ki sai dai kash,ko da na duba agogo,sai na ga har daya da mintuna talatin da tara ya buga,sai na fasa zuwa sanin cewa kin dade da yin bacci kuma baccin mai dadi ne dan baccin gajiya ne"!!
Hamida na kawowa nan sai ta ja tayi shiru tana kallon fuskar fifi dan samin amsoshi daga sauyin fuskar ta..
A ru
e fifi ta kuma riko hannun Hamida tana jin babu dadi,saurin tambayar Hamidar tayi.
"Hamee dan Allah ki yi saurin sanar da ni wannan matsala da damuwar da ta dumfaro ki,ni dama na sani,sam akwai damuwa a tattare da ke amma kika ki sanar da ni,yanzu Hamida har kina iya boye min damuwar ki ba tare da kin sanar da ni ba?ina yar uwar ki jini daya"?..
Wani irin murmushi Hamida tayi haka dama ta tsara ganin fuskar fifi bayan ta tunkare ta da wannan batun..
Dada langa
ar da kai Hamida tayi kalar tausayi ta kuma matsowa kusa da fifi ta cigaba dan samo asalin amsoshin da take so...
"Fifi yar uwa ta...,na so a ce ni ce ke cikin wannan matsalar sai dai a'a..ba ni ba ce,saidai na yarda da wannan kalmar ta masoyin ka masoyi ne ko a ina yake haka makiyin ka makiyin ka ne ko a ina yake, _*KAUNARMU*_ ta asali ce,yadda nake son ki nake kokarin ganin farincikin ki kema haka din ne,da wuya ake samin yar uwa mai kyakyawar zuciya irin taki"..nan ma tana kawowa ta ja tayi shiru..
Dulmiyewa fifi tayi cikin kogin tunanin inda kalamar Hamida suka dosa dan ta matsu ta ji matsalar yar uwar nata ba dan ta gaji da jin yabon da yar uwar nata ta mata ba sai dan ta damu da son magancewa yar uwar nata matsalar ta..
Zata yi magana Hamida ta riga ta dan bata son shirin ta ya wargaje bata so fifi ta fahimce ta dan ba halin ta bane bata saba ba,ko da tana da matsala yana damin ta bata iya tunkarar fifi da shi dan bata da lokacin ta is either tana yawon bude ido da kawayen ta,ko tana gidan Dr Fatima Yonas,so yau na cikin kwanakin da zata iya kirgawa ta zauna one on one su yi wata muhimmiyar magana,and wannan ya kasance rana daya da ba zata so tayi sake ya kufce mata ba..
"A jiya bayan mun diro kasar nan na iske sakon wata aminiya ta a inbox di na sai na share dai har muka iso nan gida,bayan na yi wanka na bude na karanta tun daga farko har karshe,kusan sau uku ina karanta sakon nan nata,sai da na kammala kai na ya kulle na rasa ya zan yi dan tana tsaka mai wuya
kuma taimako take nema na gaggawa daga gare ni,fifi ko kin san menene wannan damuwar nata"?da sauri fifi ta girgiza kai tana son jin menene..
Murmushi Hamida tayi wanda a ido da zuciyar fifi gani tayi kamar murmushin da hausawa kewa lakabi da ya fi kuka ciwo ne sai ta ji ta kara tausayawa yar uwar nata dan ta shiga damuwa sosai...
Hamida tace
"Kawata Tana da yar uwa wacce suke ciki daya mahaifin su daya haka mahaifiyar su daya,tun yarintar su sun taso ne cikin kauna da kulawar junan su,suna kafa kafa da bacin ran junan su,basu son abin da zai taba dayan su,a haka suka taso cikin rayuwa mai inganci har girman su,ana haka sai yaruwar kawar tawa ta tsinci kan ta cikin son kula wani masoyi wanda wannan masoyin kuwa ba masoyin kowa ba face masoyin wannan aminiyar tawa,bata da masaniya akai tana chan tana dakon soyayyar sa tun haduwar ta da shi ta farko sai dai bata sami damar sanar da shi ba sbd alkunya irin ta mace,abin da bata sani ba shine,tun ranar da ta hadu da wannan masoyin nata yaruwar ta ta hadu da shi itama
Amma ita aminiyar tawa ita ta fara ganin sa kafin yaruwar nata ta gan sa,nauyin baki ya sa ba a jima ba ta gano cewa yaruwar nan nata ta gama fadawa soyayyar wannan masoyi nata kuma da alama shima yana shirin fadawa a tarkon soyayyar ta,duk yadda aminiyar nan tawa tayi dan ganin ta hana faruwar hakan ta yi amma abin ya ci tura dan tana chan tana tunanin madafa yaruwar nan nata ta fara niyar kawo mata labarin kusancin ta da wannan masoyin aminiyar tawa,bata kai ga kawo mata ba sai tayi tunanin sanar da ni dan in bata mafita,..iya tunani na yi fifi,ta bani tausayi kar fah ki manta masoyi ne da ta jima da soyayyar sa a zuciyar ta kuma take ta dakon sa sai dai alkunya da nauyin baki ya sa tayi delay akan fallasa masa sirrin dake ran ta,kuma kar ki manta,yar uwar nan nata ta riga da ta gama shirya sanar da ita abin dake tsakanin su da masoyin nan nata,tunani na ya
afe
af,hankali na ya gama hango min iya mahanga,nazari na ya tsaya akan hanya,kai na ya kulle,tausayin ta ya gama mamaye ni dan shirun da tayi na nemar cutar da ita cuta ta har abada da in tayi wasa lallai zata zanawa kan ta tambari mai wuyar goguwa har abada dan tana ji tana gani yar uwar nan nata zata kasance cikin rayuwar da ya dace ita ce ta kasance ciki amma hakan bai yiwu ba, .
Mufida ina mafitar ki kan wannan matsala ta aminiya ta da yar uwar ta?me cece gudunmawar ki akan wannan labarin rayuwur tasu"?..
Kakkarfar ajiyar zuciya fifi ta sauke mai abubuwa da dama dan ba karamin tausayin aminiyar yaruwar nan tata tayi ba,labarin ya fi mata kama da irin labarun da ake sakawa a fina finai dan da wata ce ta bata wannan labarin toh nan take zata karyata ta dan bata ga ta yadda za a ce kana son mutum kayi shiru ka ki sanar da shi ka rinka boye abin dake zuciyar ka wai dan kar wata ta ji zafi da wani abu wai shi sunan shi alkunya?ita ba zata iya yarda hakan ya faru da ita ba,kasancewar yar uwar ta ce ta sanar da ita wannan labarin sai ta gasgata dan yar uwar ta ba zata taba tsara mata karya ba..
Rau da idanu fifi tayi tana jijjiga kai hade da alhinin wannan labari sannan ta yi nata maganar.
"Hamida yau da ba ke kika sanar da ni wannan labari ba,ba zan taba yarda da dan na fi ganin irin sa cikin fina finai,amma na san ba zaki zauna ki tsara min karya ba shi yasa na gasgata zantukar ki"!jin wannan kalama ta karshe da ya fito daga bakin fifi wato _"Gasgata"_ sai Hamida ta ji wani dadi ya mamaye ta dan ko da ta fara bada labarin tayi zaton fifi zata ki amincewa da labarin sai kuma ta sha mamaki dan haka ba karamin dadi ta ji ba..
Kara kyabe fuska Hamida tayi kalar tausayi ta tsurawa fifi ido tana jiran jin amsar ta..
Sai da fifi ta rinka shafa bayan Hamida tana bata magana akan komai zai wuce sannan ta cigaba da magana..
"Hamida kin ga dai rayuwar nan ita daya ce gare mu in aka bar ta ba dawowa ake yi ba sannan baya ga hakan akwai
ancin kai,
anci zaben abin da kake so a rayuwar ka,toh dan me wannan aminiyar taki take daukar lokacii wajen yin wasu tunani?in ta zuba ido tana kallo yaruwar nan nata ta mallaki muradin rayuwar ta kuma suka kasance cikin farinciki shi kenan burin ta na son yin Tarayya da wannan masoyin nata a matsayin abokin rayuwar ta ya tafi kenan ba tare da ya sani ba?
matukar ta bari wannan damar nata ya tafi tabbas rayuwa ce zata yi amma cikin kadaici da rashin ingancin abokin da ya dace dan babu wani da namiji da zai zauna mata a zuciya sama da wannan masoyin nata,sbd haka tun kafin wannan yaruwar nata ta tunkare ta da zancen ita yakamata ta dau mataki dan kare faruwar hakan,ba sai ta bayyana mata ba amma dabi'un ta su zasu nunawa yar uwar nata cewa akwai wani sirri tsakanin ta da masoyin nata kin ga daga haka ita kan ta yar uwar zata rabu da su ba sai an yi hayaniya ba,let her go for what she want,ko ba haka bane yaruwa ta"?..