← Book details Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 62

Sashe 3

Kaunar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A karo na farko suka shirya fita su biyar yan mata maheeda meena harda hameeda da wasu kyafaffun yan mata guda biyu wato yesmin da arsala dukan su kowa tanajan sport car kaloli mabanbanta
Awani katafaren resort suka sauka ita da kawayen shakawatan nata All girls out so basu gayyaci wani namiji ba
ita yesmin yar gidan wani turkish tycoon ce arsala kuma brazillian ce gaba daya baya
Daga yanayin dressing dinsu zakasan suna matukar ji da wani abu waishi kyau kyaun jiki da asalin wayewa na iya kwalliya da daukar wanka uwa uba dukiya da wadata
Dukan su sanye suke da crazy jeans da brigt colour tops
Da manyan manyan sun glasses hannun su dauke da jakunan rataya na bvlgari wayayoin su masu tsadan gaske
saidai iya kokari sunyi wajen lullube kawunan su da muflers wasu da kananan veils wasu da hoodie ta inda da kaci karo da su dole zaka san cewa sudin musulmai ne
Kowaccen su ta sha kwalliyar ta na kece raini amma banda hameeda dake sanye da Egyptian jallabiya da pure red veil tayi roling kamar wacce ta fito masallaci
Tun suna gida da ta fito cikin nata haddenen shirin irin nasu fifi daddy ne ya umarceta data je ta sauya dresing dan dole.

Batayi musu ba tabi umarnin san amna Se ta ga mufida ta fito a kile amma bai ce mata uffan akan nata shigar ba and of course ta san bazai wuce dan yana gudun bata mata ranta ba ne
Hameeda ita ta fito odd a cikin su tayi daban sekace dukkan wajen ta girme su,shiru shiru zaka ganta kamar wacce bata da nacewa amma azahirin gaskiya zuciyarta ya fara hura wata wutar da takejin hala nan gaba bazata iya sassaita shi ba
wani irin surutayya suke yi a tsakanin su wanda ya nuna tsananin shakuwa jin dadi da hadin kai
Amma zuciyar hameeda cike yake da sake sake ganin dukan hankalin kowa akan mufida yake,ita kam ma har mancewa da zamanta awajen akeyi,a duk sanda akayi abun dariya ita murmushin karfin hali takeyi
Abu daya yake damun hameeda acan kasan ranta amma bata son bayyana ma kowa dan bata san tana ina zata fara ba.

Shin su dady basa kaunar nata farincikin ne ko ita ba yar su bace rayayya kamar yar uwanta fifi?

Cikin Wannan tunanin ta tsunduma sosai har aka kammala outing din kowacce ta shiga motar ta bata san anayi ba.

Tuki takeyi ita kadai tamkar wacce gangan jikin ta ne kawai ke motsi hankalin ta ya nitsa ne wajen tuno da asalin ciwon dake cin zuciyarta a kullum yana mata zugi.
#mamuh*_ZAFAFA BIYAR NA KUDINE KA NEMI WAINNAN NUMBERS DIN KABIYA KA KARANTA CIKIN AMINCI_*
07067124863
09032345899
Wannan cuta da yar uwarta mufida ke dauke da ita shiya kara rage kaifin kauna tsakanin ta da dukkan wani abu me samar mata da kwanciyar hankli da salama a zuciyar ta
Ta zama tamkar batacciya marar amfani a duniyar mutanen da ta dauke su jigo kuma babban madogara a rayuwa kaunar da duniya take nunawa yar uwarta mufidan wani abu ne wanda za"ace har ta mutu batasa ran zata ci karo da shi ba
Son da mahaifin su yake nuna mata na musamman ne mufida Allah yayi mata baiwar da tasan ita batasaka ran samun irinsa.

Bayan kyau kyaun jiki ilimi wayewa Allah sai ya kara mata muhibba da tsananin farinjini
Tun hamida batasan kanta ba Rayuwar ta ya kasance a karkashin inuwar yar uwata mufida kowa yakan nuna tasa fifikor a bayyane batare da sun lura da halin da zasu jefa ta aciki ba. ayanzu haka zuciyarta cike yake da kishi da kuma qaunar yar uwarta saidai abunda bata iya banbancewa ba shine wanne ne yafi yawa acikin ranta?

A kullum ta zauna cikin tunani takan raya aranta cewa
Tana matukar kaunar yar uwata mufida kuma tanajin tausayin ta aranta amma ayanzu hakan baida wani amfani awajen ta
A duk inda takai wajen kololuwar son ta nuna nata son da kulawar sai taga iyayen su da yan uwan su da dukkan kawayen su suna mata irin shi koma wanda ya fishi
Ta lura Babu abunda zatayi ta birge kuma ta sha kokarin kin son hakan ya zauna mata araina amma sai takasa.

Itama mutum ce me ra'ayin son jin dadin rayuwa,shakatawa da matukar son nuna wayewar ta a fili kamar yar uwanta Fifi sai dai babu wanda ya lura da hakan bare abata irin waccan kulawar
Kowa ya mance da cewa mintuna biyar ne mabanbanta a rayuwan mu,tunda ni da ita munyi zaman mahaifa guda kuma muka fito acikin uwa guda
Aka yanke mana cibiya rana guda aka saka mana suna a rana guda sannan aka shayar damu nonon uwa guda.

Yadda yar uwata mufida take tsananin son life haka nima nake matukar so araina
Na dade da burika irin na mufeeda musamman babban burin ta akan kalar mijin data ke so tayi rayuwarta dashi wato namiji kamar ameed dan gayu me karancn shekaru young,rich,kyakkwa me aji mai ginannen jiki wanda ya kwarance a iya rayuwa da soyayya.

Zai kasance kamar ita ko kuma wanda ya fita da karancin shekaru wanda baifi uku zuwa biyar ba
Cikin sakin dogon numfashi ta rage gudun motar ta data keja ta danna horn abakin katafaren gate din gidan su tayi parking ta tattari yar jakan ta ta shiga ciki
Asalin damuwarta baifi tsoron meyene zata samu anan gaba wanda yar uwarta ta baxata rabata da shi ba
Sallama tayi ranta cike da kuncin hakan aranta mahaifin su dake zaune batare da ya dago kai ba yace wa'aliksam,bata karasa ba ya katse ta da cewa mufida kece?murmushin karfin hali tayi tace a'a hamida ce nan ya dago idanun sa yana me mata kallo mai kama dana tuhuma da tambayar ina ta bar yar uwarta mufida?

Hamida tace suna tare da kawayen ta amma tare muka kamo hanyar gida,yace meyesa zaki barta ita kadai baki da hankali ne call her now,yanayin yadda ya bata rai yasa Da sauri ta shiga dialing number mufidan yay ringing har sau biyu amma ba a daga ba...kasa cewa komai tayi ta tsaya tana kallon dady
ita kanta bata ji dadin yadda dadyn ya nuna rashin gamsuwar sa ba
Iya bayani ta masa kuma tasan ya fita sanin kalula irin na fifi,ta rasa meyasa ake yawan son nuna mata abunda bata fiye gane yuwar adalcin sa ba
Kowa yasan fifi tana rayuwar ta ne akan dokokin ta,she does what she feel like a lokacin da taga ya mata.. kuma banga lefin ta ba tunda su suka dora mata dukkanin gata da sakalci,sam basa iya mata fada kosu ce mata bari duk dan gudun kar ranta ya baci.

To meye ne nawa aciki shine ban fahimta ba.
sallamar ta ne ya dakatar da su gaba daya atare suka juyo suka tsura mata idanu,wani rau fifi tayi da idanun ta tana me aje jakarta akan table da dan sauri ta taho jikin dadyn su ta fada tana me dora kanta akan cinyoyin sa cikin sakaltaccen shagwaba cikin sanyin murya
"agafarce ni nayi latti ko?Girgiza kai daddy yyi ya dan shafa kanta cikin tsananin nuna kulawar sa tamkar ba shine yake shirin nuna damuwar sa akan rashin dawowarta yanzu ba
..shiru hamida tayi tana kallon su cikin tuno da Allah me kyautar kunci,ya dada ma kuma dole kace ka gode...
shiru me cike da tarairaya shi ya ratsasu hamida kuwa na cigaba da kwantar da wuyarta sulalewa tayi ta barsu awajen har takai bedroom din ta baxata iya bada tabbacin sun san ma tayi hakan ba
Haka rayuwar take tafiya a dadi babu dadi lamarin fifi da kawayen ta da dr ameed kai da gaba daya duniyar ma bai sauya ba
Wani abun ma gaba gaba yake yi musamnan tsakanin ameed da fifi inda yake nuna mata kulawar sa cikin tsananin nuna soyayayar sa agareta ita kuma fifi tana daukar sa ne a matsayin dan uwa kuma babban aboki
Rayuwar su atare gwanin ban sha'awa ce,"duk sa'in da suke tare sukanyi wasu abubuwan da in ka gansu ido da ido zaka ji ina ma inama kaine...

Hamida ma hakan takeji aranta dan ameed irin kalar mazan datake buri arayuwarta ne wanda anan ma yar uwanta fifi tayi mata fintinkau a zuciyar sa
Bayan windown hamida ne kawai agidan yake da lovely moonlight reflection kuma balcony ne ata kasan shi me dan fadi yana da step step na takawa
dake ba a ma yawan biyewa ta wajen akan iya zama akai a huta in waje yay sanyi
Hamida takanji matukar son tana kasancewa anan musamman can cikin dare dan ta dinga samun nitsuwa da daidaituwar tunani
Amma da ta doshi hanyar wajen sai ta shiga tuno da lokacin da ta same fifi da ameed sun jeru kafada da kafada suna kallon hasken wata suna hirar su irin ta masoya..

This is also her dream,and mufida is living it right behind her window.

Yawu ta hade tare da cewa hmmmm ta wuce dakin ta ta rufe kanta da damuwa ita kadai take mirginawa akan gadon ta,can ta mike tsaye ta bude right hand drawa ta dau wani tsohon family album ta xauna tana kallo
Tasan kwata kwata Basu wani jima da mahaifiyar su araye ba amma haka kawai takanji kewar ta da azaban kaunarta aranta duk dama tana harsashen da itama tana raye hala mufida zata zaba ba ita ba.

Cigaba da kare ma hotunan kallo takeyi tana dan shafawa da yatsun ta cikin wani irin yanayi me tafe da ssanyar sanyin zuciya.

Tabbas Mahaifiyar su kyakyawiyar mace ce kyaun ta da kalar fatar ta duk suka debo amma da alama mufida ta hada kamannin fuskn ta har dana kakar su hajja dan tafi su doguwar karan hanci da cikar suman gaban goshi
Kamar yadda mahaifin su yake da lotsawar gefen kunci na dimples haka ma mahaifiyar su take da su saidai na daddy a gefe daya ne na maman su kuma a duka site biyu
Nan ma fifi ce ta dauko kamanni mai kyaun ciki wato na mamar mu,nikuma dimple dina a site daya yake nunawa irin na daddyn mu.
Chapter 3 · 0% Book details