← Book details Idan Kaya Ya Gaji Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 52

Sashe 34

Idan Kaya Ya Gaji Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To aini in su Felisha sun zo najeriya sai dai in kawo su nan wallahi unguwar kawai abun kallone.

Gaskiya Dad kana da Sa'a, nifa kai zan biyo wallahi zanyi agolanci fes"
Dariya kawai yayi mishi baice uffan ba.

Kiran Hajiya Balaraba nayi na fa
a mata gamu mun iso tace zata turo maigadi zai bu
e mana get.

Ba'a jima ba maigadin ya le
o ya kallemu ya juya da sauri ya bu
e mana get muka shiga.

Abinda ya sake
awata gidan a idan mai kallo bai wuci yadda aka
ayata gidan da shuke_ shuken fulawowi ba, ga wasu zomaye sunata cin fulawowi a tsakar gidan har
awusi ne a gidan da irin agwagin turawannan gigs farare
ima
ima.

"Tabbb ku
i suna inda suke lolo kunga waje?

"
Cewar Maigogul daya fito yana jingine a jikin mota yana
arema gidan da motoci kallo.

Ni kaina ko kusa banyi zato Hajiya Balaraba takai haka ku
i ba, na dai yi tunanin rufin asiri gareta
Wata matashiyace ta iso inda muke bayan ta gaishemu tace mu biyota.

A baya mukaita binta har zuwa babban falon gidan da yasha fararen kujerun leda komai tsab dashi ga turaren wuta an kunna a burner sai tashin
amshi mai sanyi da sauke ni'ima yake yi.

Ni dai turaren yayi mini sosai wallahi bamma ta
a jin turare mai inganci irinshi ba. ( ga dama a gareki in dai da gaske kina son kayan
amshi ga link nan ki fa
a group
in adashe ba zaki yi dana sani ba, kuma akwai kyauta ta musamman da zan ba kowa bayan an gama adashen dan Allah in kinsan ba adashe zaki yi ba kada ki shiga naro
eki da girman Allah 2k ne zubi duk sati, amman zaki iya ha
awa ki zuba 8k a wata)
"Ku zauna Hajiyan tana shiryawane"
"To to ai babu komai yarinya"
Cewar Maigogul da yake ta dariya hankalinshi kwance.

Wannan dai matashiyarce tare da wata Baba dattijuwa suka shigo aka jera mana dambun nama, cincin, samosa, da alkaki, soyayyun kaji jar suya, da lemukan kwali kala kala banda kayan marmari yankakku da aka caku
asu aka wadatasu da ruwan madara.

"Sannunku Alhaji ya hanya, kun sha hanya gaskiya"
"Hanya Alhamdullilliahi ke yarta ce nace?

"
"A_a mai aikinta ce ni fin shekara ashirin nike aiki a nan gidan marigayi ne ya
akkoni daga
auye"
"Allah sarki ashe
ar aiki ce.

To mun gode sosai ko"?

Duk fa Maigogul ke wannan maganar.

Suna fita ya soma zuzzuba mana wannan kayan marmari a kofin tangaran.

" Ku matso mu soma ci
ila tana can tana kwalliya ni kuwa banma karya ba.

"
Naman kaza ya saka a bakinshi ya soma ci.

Ni dai wannan kayan marmarin nake sha, Uzairu zuchiyata kuma dambun nama ya jawo yanata dam
a yana cusawa a bakinshi anga na banza
Ta wata
ofa muka jiyo
was
in takalmi babu shiri Maigogul ya shiga gyare_gyare ni da Uzairu zuchiyata sai kallon abun mamaki muke yi.

Da sallama ta fito tana sanye da ba
ar abaya mai kyau da tsada kuma gata fara sol itama kyakkyawa dan ba'a kirata mummuna ba, gata da kyan jiki babu laifi gaskiya.

Da murmushi ta
araso ta nemi kujerar dake fuskantarmu ta zauna sai
amshin humrar Mrs BUKHARI take yi mai wani irin sanyin
amshi.

"Hajiya Sabuwa ashe dake za'azo barkanku da zuwa.

Wannan ma
an uwanki ne ko?

Kamanninshi da Alhaji Maigogul ya fito sosai"
"Eh wallahi ni wanta ne Hajiya.

Mun same ku lafiya?

"
Nan muka shiga gaisawa.

"Hajiya mun same ku lafiya ya zafin kano?

"
Cewar Maigogul wanda yayi magana da wata iriyar murya ta dattijan asali wanda mu dai a iyakar saninmu bamu sanshi da wannan muryar ba." Illahirin mamaki
"Lafiya lau barka da zuwa Kano ya gajiyan aikin Umara?

"
Dariya kawai yayi baice komai ba.

Niko illahirin kunya saita saki Maigogul ta kamani ganin yadda yake
arema Hajiya kallo yana bu
e ido yana mayar dasu ciki.

Hum zan yi sallah Hajiya naji kamar kiran Sallah akeyi ko?

"
"Eh lokaci yayi akwai masallaci a gidannan su Alhaji Maigogul sai suje ke kuma bari Saude tazo saita kai ki
akina kiyi sallah.

Saude, saude"
"Na'am Hajiya"
Saude ta amsa da sauri sai gata ta iso.

"Ki kai wannan
ar tawa
akin baccina tayi Sallah.

Shi Alhaji in ya dawo ki wuce dashi babban falo, wannan yaron nawa kuma ki bu
e mishi
akin Gaddafi a kai mishi abincinshi can"
Ni dai Saude nabi zuwa
akin Hajiya.

Masha Allah"
Na furta a fili bayan fitan Saude
akinne ya bani sha'awa sosai komai a killace gashi babu wani tarkace komai na ajjiye a muhallinshi.
aki na fa
a shima sai
amshin turare yake yi, kai gaskiya Hajiya na ta'amali da turarukan wuta masu
amshi da ri
e waje, ko wacce kusurwa ta gidan nata
amshi take yi. ( ga dai dama na muku adashen gata kuma zaku samu damar cin kyautar da zanyi ma duk masu adashen ko da kunfi mutum
ari.

Hajiya in fa ba adashen zaki yi ba kada ki shiga dan Allah)
Alwala na
auro na tada sallah dan Saude ta shimfi
a mun dadduma a gabas.

Ita kanta daddumar da nai sujjada
amshin turaren wuta take yi wallahi mai wani irin
amshin da
Ina sallamewa wayata ta shiga ruri.

Murmushi nayi dana ga Alhaji zaidu ke kirana.

Dama ko bai kira ba na
udurce a raina ina idar da Sallah zan kirashi in sanar mishi gani a Kano nasan zaiyi farin ciki sosai.

Amincin Allah ya tabbata a gareka kykkyawa.

Ga kano naga yau ana
walla rana ga zafi ko?

"
Murmusawa yayi yace.

"Tabbas kin canka Shalelena.

Kiyi ha
uri kin jini shuru ko?

Aiyukane suka taso mun zuwa jibi ma
asar zan bari gobe zaki ganni"
Sha kuruminka gani a kanon ni nazo ganin abun
aunata kana ina inzo in sameka har inda kake?

"
Sai da yayi dariya kana yace.

"Yanzu haka dai ina kamfanina na motoci dake mun shigo da motoci ana ta lissafe_ lissafe.

Da gaske kin shigo Kano kuma me kika zo yi Uhm?"
Na shigo kano Maigogul muka rako ni da Uzairu zuchiyata kazo ka
aukeni inason ganin kamfanin motocinka ka zazzagaya dani inga ko'ina"
"To shikenan Shalelena ki turo adireshin unguwar da lambar gidan yanzu zan bar duk abinda nake yi inzo in
akko matata ta kaina."
Sallama muka yi na ajjiye wayar sai ga Hajiya da Saude sun shigo.

Abinci Saude ta ajjiyemun ta fita ita kuma Hajiya bakin madubinta ta nufa ta gyara hodar fuskarta ta
akko wata humra a kwalba mai kyau ta shafe jikinta dashi
amshin wannan humara ta kara
e ko'ina a
akin.

Kwalbarma ta musamman ce wallahi a ido kawai kaga humrar kasan duka
auka ne
Kai Hajiya Balaraba a saudiyya, ko sudan kike siyan kayan
amshine naji
amshin humrarnan da turarukan wutan na musamman ne"
Dariya tayi ta zauna akan gado tace.

"Ai kuwa anan gida Najeriya nake siye a hannun Mrs Bukhari
ar mutan Kanuri wannan marubuciyar littattafan hausan wacce sanadin littafinta na Shanono na santa.

Bari kiga akwatin turarukan wutan dana siya a hannunta, amman anan kano hannun Anty Zee Agent
inta na kar
o dake
orayi da zama dake ita a Lagos take Aure amman har Saudiyya tana tura kayanta, nijar, kamaru, Ghana duk tana tura kaya kuma cikin aminci"
Ai kuwa kwalin da turarukan suke ciki ka
ai abun kallone, bare kwalaben uwa uba
amshin turaren nata.

Gashi turarenta saita zuba a leda ta silin
inshi sannan zata zura a cikin kwalba kamar dai kayan kamfani.

Ga wasu irin humrori da turarukan wuta.

Hajiya Balaraba tai ta sammun ina shafe jikina dashi, har humrar gashi da kulaccham ta gashi saida ta bani na shafa.

Naita santi wallahi.

"To abunda za'ayi tunda nan da sati biyu zaki tare nayi miki al
awarin show Glass guda zan saka ta ha
a miki daga nan sai
akin mijinki in sha Allah.

Wannan
inma ki tafi dasu ki soma amfani dasu kafin ki tare duk suturunki ki turaresu da turaren turara kaya dana fesawa yayin turarawa, wannan kinga na tsugunnone, wannan turaren turara jikine kullum ki dinga yi.

Kinga wannan
ar kwalbar ita kuma humrar mata aurece da kike ganinta.
awata ta jima tana bani labarin humrarnan da tasirin da take ma maza. ( masu son siyan
ai su tumtu
eni akwai kayana a Kano hannun Anty Zee dake
orayi.

Sannan akwai a hannun maman Inteesar kaduna)
"Kinga na bar Alhaji Maigogul yana cin abinci kema bari in barki haka.

To shikenan Hajiya nagode sosai nima Alhaji nake jira zai zo mu
an fita kafin ku gama"
"To shikenan muma in ya gama zamu je wajen yayana dashi su gana mu ba yara bane Hajiya Sabuwa in za'ayi ayi kawai nan da sati
aya ma sai a
aura auren ai"
Fita tayi tana cike da farin ciki marar musaltuwa.
e kular abincin nayi naga jallof
in soyayyar shinkafa wacce ta wadata da kayan lambu ga hanta baja baja
ayar kular kuma kazace soyayya ta cikin jajjagen attaruhu da albasa ga wani lafiyayyen kunun aya.

Zubawa nayi naci nayi
at na kora da kunun Ayannan.

Sai ga Alhaji ya kirani yana
ofar gidan
ewa nayi na fita na tadda Saude a falo tana turaren wuta.

Saude dan Allah wajen
an uwana zaki kaini zamu fita"
"To Hajiya muje in kaiki"
Kaini tayi
arayin yaron Hajiya Uzairu zuchiyata harda cire riga yana ta
ura abinci babu wasa.

Yayi
ai a kafet.

Taso muje ka rakamu zaga Kano ni da Alhaji Zaidu ko in barka kana kallo?

"
"Wallahi Lolo prison break nake kallo an tsaya a daidai inda na tsaya na kalli season 1 a gidan abokina.

Amman muje dai zamu dawo ai in sha Allah sai an auremu a gidannan zadai a yita da Rakiya dan bata da da
i sai dai fa mu duka muna bayan Maigogul wallahi nan gidan yafi dacewa dashi ita kanta tafi dacewa dashi su Rakiya yadda kika san su suka haifeshi fa.

Dariya muka yi ya wanko hannunshi ya shirya muka fita.

Alhaji Zaidu saina ganshi a wata
aramar mota mai kyau ja sai she
i take yi.
Chapter 34 · 0% Book details