← Book details Idan Kaya Ya Gaji Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 52

Sashe 1

Idan Kaya Ya Gaji Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Table Normal
No List
10/4, 10:30 PM] +234 810 593 2041: IDAN KAYA YA GAJI....

GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA HU
U (4)
SHAFIN FARKO.

BARKANKU DA JUMURIN JIRA INA GODIYA SO.

TEAM BABANGIDA
TEAM SABUWA
INA MI
O SA
ON GAISUWA DA JINJINATA GAREKU
MADALLAH DA
ARFAFAN HUJJOJI.

Canada
Abu kamar wasa bacci ya
auracema idanuna.

Duk wani motsi da tunanin Alhajin da ban sanshi ba nake yi.

Murmushinshi da cikar kamalarshi kawai nake hange.

Dana tuno wacece ni da irin gidan dana fito sai jikina yayi sanyi sosai.

Siraran hawayene suka surnanomun hakan saiya haifar mun da ciwon kai.

Haka dai na samu na yi baccin marar da
Da muka tashi aka taremu da
anzon masara da madara a matsayin abuncin rana.

Da daddare kuma shinkafa basmati da wata miyar kabewa ni
iya za
i zoi.

Ni wallahi na kasa ci.

Uzairu zuchiya kuwa duk abinda aka bashi kaiwa yake yi.

Na fahimci Uzairu zuchiya baima zo da wando dogo ba, duk gajerun wanduna da amles ya kwaso, naga kuma hakan ya burge Felisha sosai.

Da dare yayi ni dai ban ban jima ba nayi bacci mai cike da mafarkai barkate.

Bani na farka ba saida gari ya waye tangarangan abinka da gidan kirista, su ba sallah ba bare su tasheka kaima kayi.

Su ba kusa da masallaci ba bare kaji kiran sallah.

Alwala nayo na fito na gabatar da Sallah.

Nayi shiru a inda nayi Sallah ina tunanin da ni ka
ai na barma kaina sani.

Da wasa_wasa har sai sha biyun rana muka soma jin hayaniyar jama'ar gidan lokacin yinwa ta jigatani na shiga
akin Uzairu zuchiyata na sameshi ri
e da cikinshi yinwa zata kasheshi, gashi ya kwana gudawar gamje_gamjen da yake ta
irkama cikinshi.

"Ke lolo Kwana nayi cur ina gudawa ga yinwa na neman halakani, yanzu kaje cin abincin ma a kawo maka taliya mai madara kuma
ila tunda munci mai sikari, munci mai zumar ma.

"
To Uzairu zuchiyata kai da kake mijin Baturiya ai zaka saba da kunyi aure shikenan "
"Wa lolo?

Babu sabo.

Kinga muna kumawa zan sake zagewa in koyi girki da kyau duk da dai ina iya dafa taliya, taliyar
an yara.

Zagewa zanyi Dad ya koya mun abincinnan nashi nima in dinga mana girki ko kuma uban kowa yaci nashi"
Felisha ce ta shigo daga ita zai
aramin wando iya cinya da rigarta iyakarta ciki.

Tana zuwa ta zauna kusa da Uzairu Zuchiyata tana fa
in yayi kyau sosai.

Gaggaisawa dai muka yi sai wajen sha biyu da rabi muka hallara a teburin cin abinci
Muna cin abincin iyayen Felisha suna kafa ma Uzairu zuchiyata sharadi akan aurenshi da Felisha tunda dai taji ta gani.

Duk sharu
an da aka kafa mishi duk ya
aukesu suka gama tsayar da lokaci akan nan da wata uku me kyau sai su tawo najeriya ayi biki.
warewa Uzairu zuchiyata yayi ya dinga tari anata yi mishi sorry sorry.

Saida tarin ya lafa ne yake cewa.

"Ai mu da Dad
ina yace nan zamu tawo ayi bikin kawai in aka gama sai su koma"
Baban Felisha yace
"Bazai yiwu ba ya zama dole muga iyayenka da danginka kaima kamar yadda yau Felisha zata zagaya daku kuga nata dangin dukkansu suna nan Calgary."
Yawu ya ha
iye yace .

"To shikenan Dady"
Nan dai muka karya sai kuma muka shiga shirin fita.

Ananne muka kira su Maigogul a waya aka gaggaisa, su a Najeriya lokacin dare ne kasancewar akwa bakwai ne a tsakaninmu.

"Lolo ya kika ga Canada kyanta dan ALLAH?"
Dariya nayi nace.

Ai Rakiya wallahi ba'a cewa komai.

Gashi iyayen Felisha mutanen kirki ne gasu masu ku
Maigogul ya fisge wayar inaji Rakiya na maganganu.

"Ke Lolo ina shi Uzairu zuchiyata yake bani shi inji yayi amfani da kwalli da turaren dana bashi kuwa?"
Uzairu zuchiyata ya kar
i wayar yana dariya yace.

"Ai Maigogul ko babu kwalli da turare na riga dana sace zuchiyar Felisha ballema turare da kwalli wallahi naga amfaninsu kwallinnan yanzu haka na sake ramba
ashi da kyau.

Mun samu tarbar mutunci.

Yanzu ma haka zamu jene ganin danginta a nuna ni kuma tunda kunsan ba jinawa zamu yi ba kwana bakwai ne kacal.

Bikin dai wata uku aka saka su Rakiya sai a soma shiri"
Su Labbai duk saida aka basu waya daga
arshe ma kashewa muka yi nan Felisha ta
auki mota muka wuni munata zagaye a gari da kuma gidajen
an uwansu.

Ni dai da zaran wayarta tayi
ara sai inyi tunanin wannan Alhaji ne yake nemana sai inga ba haka bane.

Sai da muke dab da dawowa gida lokacin dare ya rufa sai kuwa gashi ya kirani Felisha ta mi
o mun wayar.

Muna daidai wani kanti na cin abinci mai shegen kyau da
ara ma jijiyoyin ido lafiya wajen kallo.

Assalamu alaikum " na furta a
asan ma
oshina.

Kafin yace wani abun sai naji ya sauke wawuyar ajjiyar zuchiya kafin yace.

"Shalele barka da dare.

Da fatan kin wuni lafiya ko.

Sannan ina fatan kinyi waya da Alhaji Baba kun sanar mishi isowarku lafiya ko?"
Murmushi nayi da naji ya kira Maigogul da Alhaji Baba yaga wanka kayan girma ya
auka aljihunma da girma.

Lafiya lau gamu nan a waje muna ta zagaya CALGARY muna kallon gari.

Yanzu haka ma ina gaban wani gidan cin abinci mai suna.

Casino blactfoot.
an gida kuma munyi waya dasu"
Sai muka yi shiru na
an sakanni shi ya katse shirun ta hanyar cewa.

"To ni yaushe za'a bani dama in zo a zagaya garin dani ko dai nayi tsufa?

Kinsan nace inaso in ganki dan mu tattauna ko?

"
Murmushi kawai nayi bance uffan ba.

"Uhm baki ce komai ba ko dai bakya son inzo ne?

"
A_a ba haka bane.

Zaka iya zuwa duk lokacin da ka shiryama hakan.

"
"To nagode.

Yaushe zaku koma najeriya amman"
Nan da kwana shida in Allah ya kaimu.

"
"To shikenan zuwa jibi zan shigo da safe amman da yamma ne zanzo wajen naki"
Da mamaki na tambayeshi.

Dama kana da
an uwa a nanne?

"
Dariya yayi mun tunda yasan inda na dosa.

"A_a ni bamma ta
a shiga Calgary ba wajenki kawai zan zo.

Hotel zan kama in mun gama yawon sai in koma in kwanta wayewar gari kuma in kama hanya.

Gobe zan gama abinda ya kawo ni in sha Allah.

"
A haka dai mukai sallama ya kashe wayarshi.

Zuwa can sai gasu Uzairu zuchiyata da ledoji rigi_rigi.

Muna shiga gidan muka tarar babu kowa suma sun tafi sha
atawa.

Ni dai abincin da akayo oda naci na rama sallolina nabi lafiyar gado.

Abincin dai mun samu shinkafa fara da kaza gashin injin, wai miyar
anyen tumaturi da gishiri.

Kai munga duniya
Washegari sai da daddare wajajen tara ma muka fita hmm club ta kaimu.

Anan muka ga ainihin watsewa irin ta turawa.

Wasu ma tsirara_tsirara gasunan.

To daga su sai rigar Mama da gwari na tsuma.

Rawa kuwa sai ti
arshi akeyi, Uzairu zuchiyata a wannan waje ya
ona mun kaina tas wallahi hiye wai ku kunga rawa kuwa hmm.

Felisha dai a bige muka dawo da'ita gida danma Uzairu zuchiyata ya iya mota kuma yana da
war gane waje.

Sai fa biyun dare muka shiga gida.

Amman a titi yadda kuka san rana.

Washegari sai na jini na tashi da farin ciki wanda ni kaina bansan musabbabin hakan ba.

Wajajen yamma ina
aki Uzairu zuchiyata ya le
"Lolo zo ga waya Rakiya zata yi magana dake.

Cewar Uzairu zuciyata.

Kar
ar wayar nayi na kara a kunnena.

" Lolo mutan turai ya kuke ya surukar tamu?"
Lafiya lau Rakiya turai gata nan muna shanta.

Ina su Labbai?

"
"Uhm suna gidan Adama kishiya ta watsa mata talge a hannu shine suka je dubata.

Amman kinsan Adama a
onen wallahi saida tayi mata kafirin duka ita a kwance Adaman ma a kwance.

"
Hankalina take ya tashi na shiga salati.

Uzairu zuchiyata ya shiga tafa hannaye dake yana jiyo mu.

"Tayi daidai Rakiya amman duk yadda akayi Gaza bai sani ba nasan da saiya mata yadda ake sa
ule gashin kaza ko?

Ni wannan Aure na Adama babu sa'a" Cewar Uzairu zuchiyata.

Rakiya tace.

"Baya gidan gangar siyasa ta doka kaima kasan Gaza bazai zauna ba.

Yana aiko yaran nashi da cefane dai a ba matarshi amman bama iya sakashi a idanunmu.

Ga wannan Yarinya Salma
akin Hauwa itama ta dawo babu auren ita kam harda goyo ta dawo abu goma da ashirin.

Maigogul babu ruwanshi ya shiga ya fita ko a jikinshi wallahi ya dai barmu da damuwa.

Kai Allah wadaran naka ya lalace.

Kunga ga ma su Adamannan sun tawo ra
e ra
e da hannu duk magani, ashe
unace bata wasa ba fa.

Adama shine kika biyosu kuka dawo gida a wanne dalili da ba zaki zauna a
akinki ba.

Wai shin gidannan da
i yake yi muku ne?

"
Ina jiyo Hauwa ta na magana.

"Haba Rakiya bakya ganin irin mummunan
unan dake hannunta ne, ai gara dai ta dawo ta zauna ta warke tukunna Allah bashi daga baya ta koma"
Wayar Rakiya ta datse tana ta fa
"Kin gani lolo shi yasa nake son ki kar
i tayin maigogul kiyi aurenki gidan arziki.

Amman naga kamar wannan Alhajin da muka ha
u a jirgi sonki yake yi ko.

Kun yi wata maganane?

Naga dai yana da kamala kuma da gani akwai ku
e a hannunshi gaskiya "
Ajjiyar zuchiya na sauke jikina duk ya mutu nace.

Yau dai muka yi dashi zamu ha
u yace zamu tattauna to bansan me zaice dani ba.

Amman biri yayi kama da mutum.

Uzairu zuchiyata na gaji da rayuwar ma gabaki
aya wallahi ji nake kamar in kashe kaina ko in gudu in tafi wata duniyar daban inda zan dena jin labarin kowa"
"A_a lolo kin soma gudu da
yamar tsatsonki ne?
addararmu ce a haka shine dalilin da yasa muka fito ta tsatson maigogul da Rakiya har fa gara Maigogul akan Rakiya wallahi.

Ni a hakan dai bana sha'awar dena jinsu.

Zan dai matsa ganina zaiyi wuya.
Chapter 1 · 0% Book details