← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 59

Sashe 9

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegeri da sanyi safiya suka tashi kamar yadda suka saba saidai yau ayyukansu yana dayawa sbd yau itace ranar zagayowar haihuwar PRINCE AKBAR... Princess hindu ita ta shirya qasaitaccen birthday partyn wanda ze gudana a lambun sarauniyya mar'atussaliha, bayi da barorin wannan gd na sarauta sai kai komo suke wajen shirya inda taron ze gudana, su bimbii kuwa su aikinsu a wannan wuri shine su rissina d'iyan saraki suna bi takansu tamkar sun sami gada sbd tsa6ar izzah da daukar bawa ba a bakin koman komai ba, dukkanin wadannan ya'yan sarakuna sun hallara shima kansa prince akbar ya iso cikin wata alkyabba golden da rawaninsa ruwan k'wai sai irqa baqi daya dora a saman kansa, princess hindu ita ta iso a qarshe cikin wani keken doki yasha ado, bayinta na biye da ita, dage keken dokin sukayi ta sakko, takan bayi itama ta wuce har ta isa wurin zamanta dake kusa da prince akbar, bimbii kawai baiwa idanunta abinci take tana 2kalle don taga wata al'ada ce ta daban, princess hindu idan mgnr tsantsar kyawu ake toh tabbas zata iya cin gasar sarauniyyar kyau don bayan izzar da take taqama dashi na jinin sarauta ga kuma na kyawu da cikar asali, tasha ado na kwala kwalai,wata doguwar rigace a jikinta irinta d'iyan saraki kalar sararin samaniyya, 2ciye suka soma da 2shaye suna raha da barkwanci a tsakaninsu jinin sarauta, prince akbar yana daga zaune fuskar nan tashi dai ba yabo ba fallasa, wata baiwa na hango tsaye a bayansa amma ita sanye take da kaya masu kyau tamkar ba baiwa ba, kallon israt bimbii tayi tace" waccar ta dake bayan prince wacce ita?" tace"itace lenah babbar baiwa a 6angaren prince akbar, ita ke kula da duk wani ci da shanshi da kula da wurin kwanciyarsa kai har ma ta tayashi kwana ta raya masa dare idan yana da buqatar hkn" jinjina kai bimbii tayi tana cin tuffan dake hannunta tana qara kallon lenah, tana da kyau itama ko hassadun iza hassada ze furta hkn, bimbii ta kuma kallon israt tace" kince har da tayashi kwana idan da buqatar hkn toh kuma ai ba matarsa bace" dariya lailah tayi don tana bayansu tana jin hirar tasu tace" su al'adarsu shine d'an sarki da sarkin shi kansa idan sun ga baiwa ta musu sukam maidata ta zama kwarkwararsu amma da kyakykyawan sharad'i kar baiwar ta yadda ta fad'a soyayyarsu bare har ki nuna feeling dinki garesu sannan kuma ba haihuwa tsakaninku dasu don basu hada jini da bayi, hukuncin kisa shi yake tabbata ga duk baiwar data qetare wannan sharad'i ko kuma daurin rai da rai har qarshen rayuwarta, mafi yawan bayi suna son su kasance a wannan matsayi sbd tamkar an y'antasu ne kuma duk abunda suke so zasu samu,zakici maikyau ki saka mai kyau ki fita ki tafi duk inda kkso sbd kina da y'anci, zakiji dadin rayuwa idan kk samu kanki a wannan matsayi saidai karki sake ki karya sharadin nan" jinjina kai bimbii tayi tace" yoo idan bakai kai ba meye hadin zomo da kura ai ramin kura sai y'ayanta,bawa ai sai ya tsaya iyakar matsayinsa" murmushi israt tayi tace" kin ga ni kuma wlh kullum addu'ata Allah yasa shekara mai zuwa idan na shiga gasa na samu" harararta khulood tayi tace" waye ya fada miki rukunin bayin da muke ciki suna samun damar shiga gasar, rukunin bayi na biyu dana uku suke da damar shiga wannan gasa" bimbii tace" au kafin ma ka samu matsayin kasance baiwar prince din sai anyi gasa" sukace mata" ehh mn, sai an gwadaku kafin a fitar, duk shekara yake sauya baiwa" bimbii tace"tirqashi!" fitowar wasu jerin yan matan bayi ne ya janye hnklinsu daga hirar da suke,yan matan su sha biyu ne suka fito don nishadintar da wurin da waqoqi, sanye suke da skirt mai baza ta qasa da wata qaramar riga iyaka cibiya,rawa suka fara tare da girgixa jikinsu sannan zabiyar cikinsu ta soma rera wak'a mai dadi, wurin yyi shiru kowa na sauraron baitocin dake fita cikin wannan wak'e nata, baitoci ne da suka shafi rabuwar masoya, baitocin nata sun samu ta6a zuciyar masoya dayawa dake wannan wuri, bimbii sunkuyar dakanta tayi tana murza wani zobe dake yatsanta na tsakiya tana kuka da hawaye don ta tuna ranar da lamid'o ya bata wannan zobe da kuma rabuwarsu dashi ta qarshe itace ranar da wad'annan turawa suka kamasu lkcin sun dawo daga tallan nono suna sauri su koma gd don magriba ta kawo jiki Allah ya hadasu da wadannan turawan akan hanyarsu ta komawa rugarsu suka kamesu suka sanyasu cikin mota, kullum tunaninta shine wanne halin innanta yadikko zata shiga silar 6acewarta,wanne hali baffi da lamid'o zasu shiga silar 6acewa, tabbas tasan rayuka dayawa suna cikin wani hali dalilin 6acewarta, kuka take sosai saida su khulood suka rumgumota suna bata hkr, idanun gimbiya hindu ne ya tsaya akansu lkcin suna rumgume da bimbii suna bata hkr, nunawa babbar baiwarta su tayi da idanunta tace"wadan can bayin dake bayan bishiya me suke" kallon wurin zulham tayi tace"ranki ya jima suna rarrashin yar uwarsu ne" tace"aikin da suka zo yi wurin nan kenan, basu san murnar zagayowar babban prince muke ba shine suka ware kansu daga cikin yan'uwansu bayi suka koma gefe, toh kije ki tahomin dasu nan gabana naji me suke tattaunawa" cikin sauri zulham ta nufo wurinsu tace" gimbiya na son ganinsu gabanta" dukkaninsu gaban ya fadi suna tunanin ko laifi sukayi, itako bimbii ko d'ar bataji ba tunda dai tasan babu abunda tayi, hk ta sakosu a gaba ta kawosu gaban gimbiya hindu duk suka durqusar da guiwowinsu gabanta tare da rissinar dakansu qasa, lkcin ne idanun kowa dake wurin yazo kansu har shima prince akbar ya kallesu sau daya ya dauke kansa ya cigaba da shan ruwan inibin dake gabansa, daya bayan daya gimbiya hindu ke binsu da kallo ta tsaida idanunta kan bimbii tana qare mata kallo, tace" kece kk janye hnklinsu daga kan aikinsu koh" shiru bimbii tayi su kuwa su khulood sai suka sake rissinar dakansu suka hada baki sukace" mun tuba ranki ya dade" kallonsu tayi ta yatsine fuska tace" su tashi su bata wuri amma bimbii kuwa ta tsaya saita musu rawa da wak'a na abunda yasata kuka" kallon zulham tayi tace" ta sanar da mai gabatarwa ya gabatar da bimbii a matsayin mai rawa ta gaba" aikuwa hk akayi, duk wurin bimbii suke kallo itako gabanta sai faduwa yake, bata iya waqar larabci ko guda ba sai na harshenta na fillaci, kama hannunta zulham tayi ta fice da ita suka shiga wani wuri ta sauya mata kaya ta saka mata rigar nan iya ci6i da skirt mai baza ta qasa ta taje mata gashin kanta ya sakko mata har duwawu gashi da cikowa kuma baqin qirin dashi, bimbii kallon kanta tayi ta kalli zulham tace" hk zan fita gaban mutane kuma ni ban iya wak'a cikin harshen larabci ba" tamkar tana mgn da dutse don zulham aikinta kawai take ba sauraronta ba, tana shiryata ta kamo hannunta suka fito lkcin yan matan dake wak'e sun bar wurin bimbii ake jira, idanun kowa nakan bimbii sbd yadda kayan nan dake jikinta ya fito da asirin dirin dake tattare da ita sannan suna mamakin tsawo da cikar gashinta kasancewarta baqar fata amma ta zarta dayansu tsawon gashi da tsantsar diri irinna mata, itako bimbii tsayawa tayi a wurin ta kasa komai sai kallonta suke suna jiran suji ta fara rero baitoci, a hnkli ta soma juya qugunta tana girgixa tamkar macijiya wata irin rawa take wacce take sabuwa a wurinsu, basu ta6a ganin salon rawan ba, cikin zazzaqar muryarta me amsa amo ta soma rero baitocinta cikin harshenta na fillanci tana juya qugu cikin wani salo rawa irin nasu na d'iyan fillo,rawar ce ta dauko hnklin kowa kanta, prince akbar dago da kansa yyi yana kallonta tashi daya yaji rawar da take da kuma wak'en da take cikin harshen nata ya sanyashi nishadi sosai har wani lumshe idanu yake, hk suma sauran yaran sarakunan dake wurin musamman prince nasaar daya qurawa bimbii idanu yana kallon zubin tsarin halittarta, kunsan dai san larabawa da mugun qulaficin jikin mace, gimbiya hindu kuwa gbdy haushin kanta tayi na kuskuren sanya bimbii rawa, kishi sosai taji tanayi data ga yadda rawar da bimbii take ta dauke hnklin ya'yan sarakunan dake wurin, miqewa tayi zumbur ta buga teburin dake gabanta cike da tsantsar masifa ta dakawa bimbii tsawa kan tabar wurin, duk ya'yan sarakunan suka jiyo suna kallonta prince nasaar yace" no, ta cigaba rawan nata ya birgemu" tace" wlh idan bimbii ta cigaba ita zata bar wurin" dage kafa bimbii tayi alamar ta gama rawan ta taho kanta a qasa ta soma qetarawa ta gaban prince akbar ta wuce shi kuma yana satar kallonta ta gefen ido sai wanda ya lura sosai ne ze fahimci ita yake kallo,ita kuwa bimbii shigewa tayi taje ta sauya kayan dake jikinta ta mayar da nata na asali, har aka gama taron gimbiya hindu tacewa baiwarta zulham kar ta sake tabar bimbii ta kuma dawo wurin taron, bimbii ta gama sauya kaya zulham tace" ki wuce ki koma 6angarenku karki kuma dawowa wurin taron nan" bimbii kuwa dadi taji don daman kunya takeji ta koma wurin,kai tsaye 6angarensu ta koma tana jiran dawowar su lailah, sai dab da magriba su lailah suka dawo suna shigowa duk suka taho da gudu suka rumgumeta, israt tace" gsky kin iya rawa zaki koyami nima" murmushi bimbii tayi kawai,ranar basu yi bacci da wuri ba sai faman jarraba yadda bimbii ke rawa suke ita kuma sai dariya take musu, israt tafi kowa zaqewa don ita a rayuwa tana son rawa da wak'a,bimbii na koya musu irin rawarta suma suna koya mata irin nasu hk suka 6ata darensu sun qi kwantawa da wuri duk da kasancewar gobe ayyukansu yana dayawa, aikuwa suna kwanciya bacci mai nauyi yyi gaba dasu, washegari ummul shukri taga dukkaninsu babu wacce ta fito kan aikinta, dogaro sandarta tayi ta shigo dakin nasu ta tarar dasu sai sharar bacci suke ba wacce ta tashi a cikinsu, juyawa tayi ta fice ba tashesu ba, suna tsaka da sharar baccinsu sukaji saukar ruwan sanyi a jikinsu gbdy an musu wanka dashi kafin su gama sanin abun yi sun soma jin saukar dorina a jikinsu, miqewa sukayi da mugun gudu suka fita, ita kuwa ummul shukri tana tsaye da dorina a hannunta ranta yyi mugun 6ace don batason sakaci da aiki.....
Chapter 9 · 0% Book details