← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 59

Sashe 40

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,idan kin tura saiki turomin da screenshrt na payment dinki ta whatsapp a wannan layin...07041195806....

Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

33

*I still love you, I still miss you*.........I just want to see you back,pls come back I'm still waiting for you💕💕

Baqi ne daga masarautar abu ansar sun iso ne bisa wakilcin ammar bin jabir don duba jikin sarki abdallah bin jabal,sun samu tarar girma sosai cikin masarautar burham, sarki abdallah kam yanzu jikin nasa babu laifi tunda yana iya miqewa zaune saidai baya iya furta komai,masarautu da dama sun ji dadin wannan cuta da sarki abdallah bin jabal ya kwanta, 6angaren da sarki abdallah ke jinya kuwa ko quda be isa ya ratsa ta wurin ba sbd tsatstsauran matakan tsaro, iyalanshi kawai keda damar shiga su duba shi shiyasa har yanzu babu wanda ze iya bada tabbacin ya jikin sarki abdallah yake ana samun cigaba ko ba'a samu game da lalurar data tadda shi, yau da dare sarki abdallah bin jabal ya daga idanu ya kalli prince akbar dake zaune gefensa yana son furta masa wata kalma amma babu bakin mgn, miqa hannunsa yyi yana buqatar a bashi takarda da alqalamin rubutu, prince ne ya dauki alqalamin da takarda ya miqa masa don ya fahimci abunda yake nufi, amsar takardar yyi ya soma rubutu a hnkli,yana gamawa ya ajiye alqalamin ya miqawa prince akbar farar takarda, amsar takardar yyi yana duba abunda ta qunsa, umartar prince akbar yyi kan yabi wadannan baqi da suka zo daga masarautar abu ansar don ganawa da sarki abu ansar da kuma yarsa gimbiya mariyatul qifdiya, saurin dago idanunsa yyi yana kallon mahaifin nasa cike da mamaki, sarauniya dake zaune gefe ta amshi wannan takarda dake hannun prince akbar ta duba, saurin dago idanunta tayi ta kalli sarki abdallah bin jabal tace" ranka ya dade, yanzu lfyrka itace mafarin farko a gare mu ba batun aure ba don Allah ka kyale wannan mgn har Allah ya tashi kafadunka,tayaya prince ze tafi nesa hk alhalin kaima da kanka kana buqatarshi kusa dakai" kau da kansa yyi gefe alamar hkn dai yakeson ayi, kun dai san taurin kai irin na sarki abdallah sam a tsarinshi baya zance biyu, washegari prince akbar tare da rakiyar babban hadiminsa ubaid da kuma wadannan manya baqi da suka zo suka dugumxuma suka nufi masarautar abu ansar, tun kan su isa sarki abu ansar yasan da zuwan prince akbar don hk ya shirya liyafar girma don tarar wannan dan sarki ma'abocin daraja da qarfin izzah,sun qawata wannan masarauta da kayan ado, jan carpet aka shimfida dogo inda takan wannan carpet prince ya taka har ya samu isa cikin fadar sarki abu ansar, yana zaune bisa kujerar mulkinsa fuskarsa da yalwataccen murmushi dakansa ya miqe ya riqo hannayen prince akbar ya zaunar dashi a kujerar da aka tanada domin shi,sarki abu ansar yyiwa prince akbar dayake tamkar surikinsa barka da ziyartar wannnan masarauta, bayan wannan jawabi na sarki abu ansar sai liyafar da aka shiryawa prince akbar ta soma gudana, gimbiya mariyatul qifdiya kuwa tunda ta samu lbrin zuwan prince take ta murna har farin cikin nata ya kasa 6oyuwa, gimbiya khamriyya tayi ruwa tayi maqarbiya wurin kimtsa tilon qanwarta tata sbd ta fahimci mariyatul qifdiya bata da masoyin data mallakawa ruhinta kamar prince akbar, gimbiya mariyatul qifdiya tayi kwalliya na ruwan zinare hannu,wuya har ma da qafa, sanye take cikin wata lafiyayyen jar doguwar riga da mayafinta data yane kanta dashi,riga ce irin wacce yaran sarakai da manyan attajirai ke iya sakawa,gbdy ta zaqu ta gana da masoyinta prince akbar, shi kuwa babban prince ana qare wannan liyafa sarki abu ansar yasa aka kaisa royal louge na wannan masarautar,6angare ne na musamman suka tanada sbd baqi jinin sarauta, wurin yyi kyau sosai don an qawata wurin tun daga farfajiyar 6angaren idanun mutum zasu soma lumewa kan kyakyawan furanni masu mutuqar daukar hnkli tare da kukan tsuntsaye ta ko'ina,babban hadimin sarki abu ansar jamal tare da wasu hadiman suka yiwa prince akbar rakiya zuwa wannan royal louge, ubaid na biye da prince akbar har ya shiga cikin wurin shi kuma ubaid da sauran wadannan hadimai suka tsatstsaya a bakin kofa don tsaronsa, prince na shiga ya samu komai tsaftsaf, zama yyi bakin wani gado na alfarma yyi shiru, 6angaren turakar jira kuwa inda bimbii take lbrin isowar wannan dan sarki ya iso ga suwaibah don hk ta tashi ta shiga inda yan mata suke don za6o mai cikakken dirin halitta da kaifin basirah ta kasance da wannan dan sarki don hidimta masa, yan matan duk suna zazzaune kowacce tayi ado na a kalleta, kallonsu take daya bayan daya, idanunta ne ya sauka kan bimbii, tace" ke tashi na ganki" miqewa bimbii tayi a hnkli ta tsaya suwaibah na qare mata kallo tun daga sama har qasa, kallon buqasassun hips dinta tayi daya fito sosai ga albarkatun fulaninta tsaye qam tamkar danyar budurwa duk da cikin dake cikinta, kowacce a cikin yan matan burinta a za6eta don tarar wannan dan sarki amma sai suwaiba ta nuna bimbii tace" maxa ki biyo baya na" mamaki ne ya cika kowa wurin sbd kowa yasan ba'a tarar jinin sarauta da baiwar da ba virgin ba wato danyar budurwa toh don me shugaba zata za6i bimbii wacce take da yaron ciki,suwaiba kuwa sam bata duba hk ba abunda kawai tayi la'akari dashi shine bimbii tafi dukkaninsu cikar dirin halitta ta cikakkun matan girma burin kowanne da namiji duk da kasancewarta baqar fata kuma mai yaron ciki, kai tsaye dakin gyara ta wuce da ita ta shiryata dakanta cikin wasu sexy dress masu mutuqar janye hnkli ta taje mata gashin kanta ya saukar mata har tsakiyar gadon bayanta sannan ta dauko wata abaya fara sol ta sanya mata ya rufe wannan shiga dake jikinta,gashin idanunta kuwa shima yasha gyara yyi baqi qirin hasken kwayar idanunta kawai ake iya gani ga lips nata yasha pink lipatick sai glowing yake, murmushi suwaiba tayi yadda taga bimbii tayi masifar kyau na gasken gaske, hamshaqiya ramlatu ce ta shigo ta kalli bimbii sai kuma ta kalli suwaibah tace" shugaba wannan wa zata tara hk" murmushi suwaiba tayi tace" zata tari dan sarki prince akbar na gimbiya mariyatul qifdiya ma'abocin cikakkiyar izzah" hamshaqiya ramlatu tayi saurin kallon suwaiba cike da mamaki tace" amma baki gani wannan ba budurwa bace sannan cikin darasin jan hnkli da ake koyar dasu sam bata da fahimta gashi tana dauke da yaron ciki shugaba karki saba doka kinsan cikakkiyar izzah irin ta jinin masarautar burham tayaya zaki tari wannan dan sarkinsu da baiwar daba budurwa ba qarewa ma tana dauke da juna biyu wannan tamkar gangaci ne kk shirin aikatawa" dafata suwaibah tayi tace" sam babu gangaci cikin wannan hikima tawa baki da sani cewa prince akbar shine masoyi kuma miji ga gimbiya mariyatul qifdiya,itace ta umarceni kar na sake na tura virgin din baiwa ga masoyinta" shiru hamshaqiya ramlatu tayi tana tunani, tabbas ba komai ne yasa gimbiya mariyatu tayi hk ba sai tsantsar kishi irin nata bata son suwaiba ta tura danyar budurwa ga prince akbar don tasan idan ma yana da tunanin mace ta debe masa kewa yaga an tura masa baiwa mai yaron ciki tasan babu ta yadda za'ayi ya sauke buqatarsa kan wannan baiwa sbd yana da cikakkiyar izzah bazai ta6a kusantar macen da take a bude ba, kuma dakyar ne be koreta ba, ita kuma gimbiya mariyatu hk take so sbd tana da kishi akansa sosai, lkcin da gimbiya mariyatul qifdiya ta nemi ganin suwaiba ta sanar da ita buqatarta, murmushi suwaibah tayi tace" ranki ya dade kar damu don yanzu hkma ina da wata baiwa cikin yan matana dake dauke da yaron ciki kuma gata bata da wata dabara na janye hnklin namiji ita zan tura masa"wannan batu na suwaibah ba qaramin sanya gimbiya mariyatu qifdiya farin ciki yyi ba har saida ta yiwa suwaiba kyautar zoben gwal,bayan an gama shirya bimbii suka fito suwaiba ta kama hannun bimbii ta sanyata cikin keken doki wasu hadimai hudu suka soma jan keken dokin suka wuce da ita royal louge don tarar wannan dan sarki, suna isa ta sakko daga keken dokin fuskarta rufe da mayafi, babbar baiwar dake kula da wannan 6angare mai suna aslamiyya ita ta miqawa bimbii wani kyakykyawan kwando dan qarami mai dauke da kayan marmari ta nufi hnyr shiga cikin wannan 6angare, masu tsaron dake kula da wurin suka bata hanya cikinsu har da ubaid, sam be ganeta ba domin fuskarta a rufe take da mayafi ya bata hanya ta shige,tfy take a hnkli bawai da niyyar yanga ba ko jan hnkli ba saidai kawai ita daman hk Allah ya mata wannan baiwa, idan tana tfy tamkar tarwada duk wasu ma'adanai na jikinta juyawa suke suna tsole idon masu budadden ido suna musu kwalele,cikin wannan irin salon tfy ta samu shiga wannan louge, tsarin wurin yyi mata kyau sosai, bata bude mayafin data rufe fuskarta dashi ba amma tana ganin komai a hk, prince kuwa yana zaune bisa wata kujera fitowarsa kenan daga wanka don be aminta wata baiwa ta taimaka masa wurin wanka ba koh a gida babbar baiwar kadai keda wannan yancin bare a masarautar daba tashi ba, aslamiyya ita ta fara shiga wurinsa kafin bimbii ta iso ta hada masa ruwan wanka a kwarmin wanka ta sanya sinadaran wanka tana gama wannan aiki ya daga mata hannu alamar ta tafi baya buqatar komai bayan hk, yana daga zaune yaji motsin shigowa amma be waiga ba har ta tako inda yake zaune ta tsaya a bayansa,ta bude fuskarta ta dora kyawawan hannayenta wanda ke sanye da awarwaraye masu kyan gaske ta dora bisa kafadarsa ta soma masa tausa...........

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw saiki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, idan kin tura saiki turo da screenhrt na payment dinki ta whatsapp a wannan layin...07041195806........

Alkalamin Bintuu ne.......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

34
Chapter 40 · 0% Book details