Sashe 47
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Prince dakansa ya nufi qasarban ya taho da bimbii, ranar duk inda ka zauna cikin bayi tsegumin wannan zancen suke wai tsohuwar baiwar babban prince ta dawo tare da sabon jariri, mafi yawan masu tsegumin basu aminta cewa wannan d'an na babban prince bane, sarauniyya mar'atussaliha dakanta ta bada umarnin a shiga da bimbii 6angarenta, bimbii kam zuciyar cike take da tsoro musamman yadda taga fuskar wadanda suka tare ta, ummu nana da wasu kuyangi biyu suka kama hannun bimbii suka shige da ita,ummu nana ta amshi jarrin dake hannun sumayya ta wuce dashi ciki, wanka aka yiwa jarrin aka sanya masa kaya na alfarma sannan ta fito dashi ta wuce dashi ga sarauniyya, tana shiga ta sunkuya ta miqa mata jaririn, miqa hannu tayi ta amshi jaririn, qurawa jaririn idanu tayi tana kallon ikon Allah don wannan jariri babu ta inda ya baro kakansa sarki abdallah hatta idanunsa na kakansa ne, kasa dena kallon jaririn tayi tana qara jaddada mulkin ubangiji wato dai zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzu ana shaho sai yyi, yaro dai kakansa ya dauko, miqewa tayi dakanta hannunta biyu riqe da jaririn ta nufi 6angaren sarki abdallah ummu nana da sauran kuyaginta na take mata baya, uxair ne ya shiga ya nema mata iso sarki abdallah ya bata damar shigowa ta shigo, yana zaune a wata kujera ta sarauta tunda ta shigo yake kallonta, rissinar dakanta tayi a gabansa sannan ta miqa masa jaririn dake hannunta, qin miqa hannunsa yyi ya amshi jaririn ya daga mata hannu alamar ya sallameta, shiru tayi tana kallonsa sanin halin taurin kai da kafiya irin nasa yasa taja da baya jikinta a sanyaye ta juya ta fita, komawa tayi sashinta ta tarar itama bimbii ta shirya tsaf, itakam sarauniya ta zubar da makaman yaqinta tunda ta dora idanunta kan jaririn nan, bayin gdn gbdy sun saka idanu har sun gaji amma basu samu damar ganin bimbii ba bare jaririn dake tare da ita,shi kansa prince ganin bimbii ya gagare shi,kamar yadda sarki abdallah ya alqawarta hkne ya faru, safiyar alhamis al'ummar fadar masarautar burham suka shaida daurin auren bimbii da prince akbar, wurin wannan daurin aure tamkar wurin makoki babu mai annuri ko walwala, a dai daura, sarki abdallah ya tabbarwa al'ummar duniya shi sarki ne mai mgn guda da tsayawa kan alqawari, wannan rana baqa take qirin ga sarki abdallah da dukkanin wani jini na sarautar burham idan muka dauke babban prince da ranar take fara qal a wurinsa, a tarihin masarautar burham yarima akbar shine d'an sarki na farko daya karya tsaurarriyar dokar wannan masarauta ya auri baiwarsa, wannan aure ya zamto tamkar faruwar mugun abu ga jinin sarautar burham, dayake abun duniya baya 6uya kafin giftawar ido wannan aure tsakanin d'an sarki da baiwa ya karad'a sauran masarautun larabawa, sarakai dayawa idan suka ji wai duk qarfin mulki da izzah irin ta sarautar burham magajin masarautar ya bige da auren qasqantacciyar baiwa kuma baqar fata, hkn yasa sarki abdallah ya dena halartar taron sarakuna na nahiyar larabawa sbd wannan abun kunya da d'ansa ya janyo masarautarsa,bimbii har yanzu tana 6angaren sarauniyya daren yau za'a miqata 6angaren prince akbar, sun shirya sosai albarkacin hada jini dasu da tayi, prince yasa matakan tsaron sirri masu sanya idanu kan duk wani motsi na masarautar burham kan iyalinsa,keken doki na musamman aka kawo don daukar bimbii zuwa 6angaren babban prince, dakarun tsaro da yan matan bayi kewaye suke da wannan keken dokin, fuskarta rufe take da jan mayafin kayan dake jikinta, ta wata siririyar dake saman gada suka bi,hanya ce da dawakai ke ratsawa zuwa 6angarori daban daban na gdn, tfy suke zabiyoyi dake biye da keken dokin na rero waqoqi na masoya masu dadi har suka kai tsakiyar hanyar, suna tsakiyar wannan siririyar hanya sai gani sukayi kawai an tsagayesu, wasu mutane ne sanye da baqaqen kaya, fuskokinsu ma a rufe suke batare da wani 6ata lkci ba suka soma fada da dakarun dake janye da keken dokin da amarya ke ciki, sunyi masifar iya fada kafi kwabo sun soma kwantar da dakarun, burinsu kawai su qarasa wurin wannan keken doki su dauke amarya da jaririn dake tare da ita, ihu kawai kkji, jini duk ya 6ata keken dokin, yan matan bayin nan qoqarin fito da amarya suke su gudu da ita kafin wadannan mutane su qaraso, tuni suka gane nufin kafin suyi wani yunquri wani cikin mutanen ya yarfa musu wani sai ga wasu kananan allurai masu guba sun fita sun sossoki jikinsu suka zube a wurin, sai da suka gama da kowa suka bude keken dokin suka janyota waje wani daga cikinsu yasa hannu ya wafce jarrin dake hannunta, jin jikin jaririn yyi wani iri, saurin bud'e kyakykyawan farin towel din da jaririn yake ciki yyi,tirrqashi! kunsan me ya gani qatuwar teddie, kallon juna sukayi cike da tsantsar mamaki, aikuwa tamkar hadin baki su duka suka sanya hannu suka yaye mayafin da armarya ke rufe dashi sukaci karo da wata baiwa itama duk a tsorace take, batare da wata wata ba babban cikinsu ya daga takobi ze fille kan wannan baiwa a fusace,wani mahayi fuskarsa rufe da baqin kyalle ya bayyana bisa farin doki tunkan ya qaraso yake harbinsu da kwari da baka har ya qaraso wurin, hkn yasa hnklinsu gbdy ya tafi ga wannan mahayin doki suka gyara riqon takubban dake hannunsu hkn ya bawa wannan baiwa daman barin wajen don tsira da rayuwarta, wani irin fada suke gwabzawa tsakaninsu da wannan mahayin dokin burinsu kawai suyi masa illah saidai salon fadansa yyi masifar basu mamaki sbd fada yake irin na cikakkun jarumai masana sirrin takobi, gashi da zafin nama da iya gociya, suna ganin hk sukayi wani irin alkafira suka fada qasan gada su dukka, sauka yyi a hnkli daga saman dokinsa yana kallon irin 6arnar rayukan da sukayi sbd kawai son zuciya, shikam taurun kai wannan sarki na bashi mamaki besan sai yaushe ne ze ajiya wannan kiyayyar da taurin kai ba, qara jinjina kaifin basira na prince yyi daman yasan hkn na iya faruwa shiyasa ya bawa sumayya kayan da bayi ke sanyawa yace ta bawa bimbii ta saka ta fito da ita a sace ya tura mata wannan baiwa ta zama a madadin bimbii, saida sumayya ta bari an gama shirya bimbii daga ita sai ita tayi saurin sanyata ta cire wannan kayan dake jikinta sannan ta shigo da wannan baiwa ta cire kayan jikinta sukayi musaye, ita baiwa ta zauna a madadin bimbii ta rufe fuskarta da mayafi, sumayya sanya jaririn cikin kwando bimbii ta fita dashi batare da kowa ya ankara ba ta nufa inda sumayya ta fada mata don daman tasan ko'ina cikin gdn, sai qasa take da fuskarta kar wani ya ganeta hk har ta samu ta fice daga 6angaren sarauniya ta nufi daidai gdn magani wurin da sumayya ta fada mata ta hangi inuwar mutum tana waigawa ta hangi ubaid ta qarasa, batare da wata doguwar mgn ba ya samu ya qarasa da ita 6angaren prince akbar ta shige, wannan shine zahirin abunda ya faru a 6angaren sarauniyya, lkcin da bimbii ta shiga ta tarar da prince tsaye yana sauraron qarasowarta don ya aminta da hikimar hadiman dayasa wannan aiki yasan dakyar ne a samu kuskure, yana ganin bimbii ta shigo yyi murmushi tare da bude mata hannayensa, tsayawa tayi don kunyarsa take ji, murmushi yyi ya qaraso ya amshi yaron dake hannunta ya rumgume shi a qirjinsa itama ya janyota ya rumgumeta suka qarasa bakin gado suka zauna hannunsa yasa ya dago da fuskarsa data 6oye a saman kafadarsa yace" kin zama sarauniyata nafi kowa farin ciki da hkn kefa?" shiru tayi masa ta qara 6oye fuskarta a kafadarsa, juyawa yyi ya kwantar da babyn dake hannunsa a saman gadon ya dawo ya zauna ya sake janyota jikinta suna fuskantar juna, numfashinsu na haduwa, bakinsa ya matso dashi daidai da dan mitsitsin bakinta ya dora saman nata a hnkli kuma ya soma kissing nata cikin wani salo mai saurin rikita lissafi, bimbii kam idanunta na lumshe, sun yi nisa cikin wannan yanayi suka ji qarar kukan babynsu yana wani irin kakari, a rude suka saki juna suka juya don ganin me ya same shi................
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki tura screenshrt na payment ta whatsapp ta wannan layi...07041195806.....
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
41
*Your love is the most precious gift to me*.......You are my weakness coz i love you so much💕💕
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki tura screenshrt na payment ta whatsapp ta wannan layi...07041195806.....
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
41
*Your love is the most precious gift to me*.......You are my weakness coz i love you so much💕💕