← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 59

Sashe 15

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dare yyi sosai amma gdn akwai yalwar fitilu ta ko'ina suna haske kowacce kusurwa ko allura ce ta radio take za'a ganota sbd wadataccen haske daidai lkcin bimbii ta fito sanye da wata doguwar riga bak'a qirin hkm mayafin rigar tfy take a wani dogon corridor hannunta dauke da wani faranti na azurfa da qananan kofina da kuma wani jug mai kyan gaske a tsakiya, green tea ne aciki kuma wannan dogon corridorn shine zai sadata da babbar k'ofar inda prince akbar yake wato sashinsa,jikinta rawa yake sosai don duk a tsorace take sbd batasan meze faru ba, tana qarasowa bayin dake tsaron kofar suka bata hanya,kofar ta bude da kanta ita kuma ta danna kanta ciki kanta a sunkuye tamkar wata munafika, tana sanya kafafunta ciki wani sassayan qamshi tare da sanyi yyi mata maraba, qasan wurin tamkar glass yake sai daukar idanu yake da kyalli, dakin qaton gaske ne kuma kusurwa kusurwa yake,kowacce kusurwa tana da kofa kamar ta masallaci an kame wurin da curtains na alfarma ga kuma shimfida na manyan royal center carpets masu ado, curtains din da aka kame kowacce kusurwa zaka gansu sharara,komai na cikin wurin abun kallo ne, 6angare guda kuma wasu kujeru ne irin royal chairs din nan kalar golden, kusurwar tsakiya idanunta suka kalla inda ta gano kusurwar tafi kowacce girma an kameta da wani qasaitaccen curtains shara shara milk colour, wani gado ta gano a cikinta tafkeke yasha bedshit na wawayen kudade shima bedshit din milk colour, bimbii tsayawa tayi kalle kalle tamkar yar qauye cikin ranta tana mamaki wai nan duk wurin kwanan mutum guda ne, tunda ta shigo yana zaune a wata kujera yana karanta wani littafi na tarihi ko dago da kansa beyi ba sai yanzu, ita kuma sai lkcin idanunta suka sauka a 6angaren da yake take taji wata faduwar gaba ta tsaya qam a inda take batare data qaraso ciki ba, miqewa yyi ya soma takowa a hnkli har ya qaraso inda take fuskarsa babu yabo babu fallasa kamar dai yadda yake kullum, tsayawa yyi yana qarewa shigarta kallo ya tsayar da kwayar idanunta akan fuskarta ita kuwa sai tayi saurin yin qasa da guiwowinta a gabansa, bata ta6a tsammanin zeyi magana ba taji muryarsa cikin tsadadden larabcinsa yace" kije ki sauya wannan kayan dake jikinki" abunda ya fada mata kenan ya juya cike da takun qasaita ya koma inda yake zaune ya cigaba da abunda yake, ita kuwa bimbii miqewa tayi da sauri ta juya da niyyar ficewa daga dakin har tana hard'ewa ta rasa dalilinsa nacewa taje ta sauya kayan jikinta sai ta soma wani tunani nata na daba take hnklinta ya qara tashi cikin ya duri ruwa hk ta koma dakin da take, tana ta cika da mamakin ganin su israt da suka sato jiki suka zo wurinta suka tarar bata nan suka bararraje a saman gadonta suna baccinsu, motsin shigowarta ne da farkar dasu suka tashi suna binta da kallon mamaki, khulood tace" bimbii daga ina kk badai daga 6angaren prince kk ba cikin wannan kayan" kallon kanta tayi ta dago ta kallesu tace" me kayan yyi" israt ta sakko daga saman gado ta iso gabanta tace" waye ya fada miki prince yana son baqin abu komai nashi fari ne shiyasa bayinsa basu sanya duk abunda ya danganci baqi" shiru bimbii tayi sai lkcin ta gano manufarsa ta kuma fahimci mugunta ummu sumayya taso mata tace ta sanya baqin kaya, zama tayi a bakin gado ta zabga tagumi, israt ta sanya hannu ta cire mata tagumin da tayi tace" mene ya faru yar uwa" murmushi tayi tace" wlh nikam tsoro nk gbdy nayi dana sanin shiga wannan za6en" israt tace" me kkce? sake fada naji, yanzu bimbii baqin ciki kk mana don gashi dai silar cin za6en nan da kkyi har muma mun samu arzikin shigowa wannan wuri har da kwana akan gado mai taushi shine kk cewa kina dana sani, toh meye abun dana sani anan" kwantar dakanta tayi ta kafadar israt, khulood ta matso ta zauna kusa dasu ta dafa bimbii tace" tashi ki cire wannan kayan dake jikinki ki shirya cikin masu jan hnkli" harararta bimbii tayi suka bushe mata da dariya, hk suka sake shirya cikin wata milk colour din doguwar riga mai cike da kwalliya sannan israt ta mata 6arin turare har sai da tace" israt wlh ya isa hk" sannan suka qara taje mata gashi suka tufkeshi da wani band shima milk colour, suka sanya mata wani mai kyalli a le6en bakinta, le6en ya soma shiny, suna cikin shiryata lenah ita da wasu bayi su hudu suka bankado kofar dakin suka shigo ta soma binsu da wani matsiyacin kallo sai ta bushe da dariya suma sauran dake biye da ita suka bushe da dariya, tace" idan kun sauya mata baqin kaya ai baku isa ku sauya mata kalar fatar jikinta ba koh" israt tana shirin maida musu da martani bimbii ta riqeta, matsowa lenah tayi kusa da bimbii tana mata wani kallon wulaqanci tace" basu sanar dake babban prince bashi son baqin abu bane toh bawai baqin kaya ne kawai baya so ba har ma da baqar fata" khulood tazo iya wuya ta kallesu itama a wulaqance tace" dadin abun dai shiya za6eta kuma cikin gayyar fararen fatan yace ita ta dace ta hidimta masa wannan kadai abun alfahari ne" israt tace" idan ma ba naci da neman fada na wasu matan ba yace ya dena yayinki toh meye kuma na farkar jeji hk" kalaman nasu sun fusata lenah sosai amma sai ta dake tayi wani murmushin yaqe tace" toh muna nan muna jira muga ko iskar tusa zata hure wuta" dariya sauran bayin dake biye da ita sukayi suka juya suka fice abinsu,bimbii tayi tsuru tsuru da ita saida su khulood suka din ga binta da kalamai na qara qarfin guiwa,khulood tace" karki mance lailah tana nan tana jiran gudummawar mu gareta komai rintsi kiyi mn alqawarin ba zaki gjy ba" tashi tayi ta rumgumesu gbdy sannan suka mata rakiya har kofa ta fice ta doshi komawar 6angaren babban prince, tana shiga ta tarar dashi sanye da wasu kayan bacci farare qal, gashi kansa ya sauko masa har kafada yana zaune a wata kujera ta alfarma yana hada wasu takardu, shigowar ta ne yasa shi dago dakansa yana kallonta sannan ya dauke kansa ya cigaba da abunda yake, rasa abunyi tayi sai ta koma gefe ta sunkuya akan guiwowinta tana jiran umarninsa, kallonta yyi yace" wannan abun da kk kawo ni kkson na zuba dakaina" mgn yake yana abunda yake batare daya kalleta ba, tashi tayi da sauri ta matso wurin ta dauki qaramin jug din ta tsiyaya masa green tea din data kawo a daya daga cikin qananan cups din dake saman farantin ta rissinar dakanta tare da sanya hannu biyu ta miqa masa cup din, kallonta yyi sannan ya miqa hannunsa fari tas dashi ga yalwar gashi zarara ya amshi cup din daga hannunta ya komar dakansa ya kwantar jikin kujerar dayake yana sipping green tea din a hnkli tamkar bayason ya qare ita kanta na sunkuye cike da kunya irinta ta fulanin usul sbd ita tunda take bata ta6a ke6ewa da wani namiji irin hk ba, shiko prince akbar dayake mutum ne ma'abocin karantar yanayin jama'a yana biye da duk wani action dinta, sai jin muryarsa tayi yace"kinsan a tsari na hidimta mini zaki iya kwana dani da biyamin buqata koh, to meyesa kk shiga za6en duk da kinsan da hk ko kuma kin shiryawa hknne" tayi mutuk'ar mamakin jin wadannan kalmomi daga bakinsa, wani qasaitaccen murmushi yyi hkn ya kuma dulmiyata cikin tsagwaron ruwan mamakin wannan dan sarki da ta6a zaton yana mgn mai tsawo hk ba kuma kalmomin nasa sun sanya zuciyarta tsananin bugawa tana tsoron kar fa mai afkuwa ta afku akanta idan kuwa hk ta faru lamido bazai ta6a yafe mata ba har abada koda ta samu damar komawa gd, sai juyawa tayi bata ganshi a wurin ba dayake tana waiwaya ta gano shi saman royal bed nasa ya kwance ya saki curtains dinshi, alama ya mata data zo, wayyo Allah abunda ta furta kenan cikin zuciyarta dake tseren sukuwa sbd tsantsar bugawar da take, jiki a sanyaye ta nufi kusurwar da gadon nasa yake ta same shi kwance ya juya mata baya wannan alama ce dake nuni da prince din yana buqatar tausa, hk tahau gadon nasa cike da tsoro ta miqa hannunta dake rawa sosai ta dora a jikinsa dake fitar da wani tsadadden qamshi na musamman ta soma masa tausan cikin sanyin jiki, shi kuwa idanunsa a rufe suke tamkar besan me take ba hk ta cigaba da tausa a wannan jikin dan sarkin mai mutukar taushi da silbi tamkar jikin aljanu, tunda yaji bacci ya soma ziyartarsa yyi mata nuni data fice yana son bacci, take wani dadi ya ziyarci zuciyarta ta saukar da kafafunta qasa a hnkli ta fice da wurin ta sake masa curtainsa ta rage masa haske kamar yadda aka sanar da ita ta fice a millions tayi hanyar 6angaren da dakinta yake, tana shiga ta tarar dasu israt da khulood har sunyi nisa a bacci itama, rage kayan jikinta tayi ta nemi gefensu itama ta kwanta abinta take itama bacci yyi gaba da ita, khulood ce ta fara farkawa da asuba ta ganta kwance, israt ma ta tashi duk suna kallonta, baqin ciki ne ya cika zuciyoyinsu sbd ba hk suka so ba wato itama bimbii prince be amshi budurcinta ba kenan, kawai abunda suka qara yarda dashi a lkcin shine prince akbar yana tinqaho cikakkiyar izza mai k'arfi da take hanashi kusantar kowacce baiwa wato yana kyankyamin hada kyakykyawan jikinsa da bayi hkn suka aminta dashi, bimbii kuwa da farin ciki ta tashi tana musu albishir da Allah itama ya tsallakar da ita ta fito da budurcinta, harararta israt tayi tace" ke har wani murna kkyi sbd kin fito da budurcinki toh mu ba hk muka so ba" bimbii ta kalli israt tace" so kk daya keta min haddin budurci" khulood tace" tabbas da hk ta faru da mahassada da maqiya sun ji kunya saidai baqin ciki ya kashesu" dariya bimbii tayi ta miqe tace" wlh gwara da hkn bata faru ba don kuwa daga da hk ya
Chapter 15 · 0% Book details