Sashe 42
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bimbii na komawa turakar jira kuwa yan mata wannan turaka suka soma tuntsira mata dariya don su tunaninsu babban prince ya koreta ne, wata daga cikinsu mai suna veesha tayi saurin miqewa tayi wani irin juyi da rausaya tana karkada jikinta cike da salo, sauran yan mata suka dauki tafi da shewa, murmushi veesha tayi tace" ku duba fa ku gani da mata irinmu wadanda suka kware wurin iya sarrafa jiki da kissar dauke hnkli kowanne taurarren namiji amma wai duk a wuce mu dauki wannan mai tutsetsen cikin,hhhh" zeena tace" kedai yi shiru kawai ai daman sanya idanu nayi naga yadda abun ze kaya, ke kin ga haduwar wannan dan sarkin kuwa, tayaya ne ma ze sauke buqatarsa kan ragowar wani ga danyun yan mata irinmu masu cikakken budurci ga kuma salon hillata" tafawa sukayi suna sheqa dariya ita kuwa bimbii tana zaune gefe tayi tsuru tana kallonsu, ganin suna watsa mata baqar mgn yasa ta miqe ta wuce dakin kwananta,2kwata kasa rintsawa tayi burinta kawai ta sake shaqar qamshin jikin babban prince,miqewa tayi ta soma shinshina jikin kayanta ko ya kama qamshin nasa, hk ta din yi tamkar wacce ta samu aiki, shigowa wasu yan mata biyu da suke kwana daki daya ne yasa tayi saurin komawa ta kwanta amma a zahiri hoton fuskarsa ne yake mata gixo, hannu tasa ta daki kanta dashi tace" na shiga uku me nake yi hk" zuciyarta ta gargadeta kan ita fa qanqantacciyar baiwa ta tsaya matsayinta kar ta sake takai kanta inda Allah be kaita ba, hk dai ta din ga fama tana qoqarin manta fuskarshi dake mata yawo har ta samu bacci ya soma daukarta,washegari, suwaiba taje ta sanar da gimbiya mariyatul qifdiya wannan kyakykyawan lbri hkn yyi mutuqar sanyayawa gimbiya mariyatu zuciya, musamman aka shiryata cikin wasu kayan na alfarma don ganawa da masoyinta rabin rayuwarta, babban prince yana tare da sarki abu ansar a dakin ganawar sirrinsa, sarki abu ansar ya kalli prince akbar yace" tabbas maqiya sunyi amfani da baquwar guba ne wacce take sabuwa qirqira da har yau masana basu gano laqonta wurin cutar da mahaifinka sai zan tura ka ga wani bawan Allah tsohon masani ne kuma bayahude daya jima yana qirqirar gubobi masu tsananin cutarwa ga lfyr bil'adam, yasan sirrin kowacce irin guba, wannan bayahude yana rayuwa ne a wani tsibiri can arewacin spain da ake kira oldest Inland na tabbata wannan bayahude bazai rasa sani game da abunda ze daqusar da wannan guba dake jikin mahaifinka ba" shiru prince akbar yyi sai kuma ya dago ya kalli sarki abu ansar yace" yakai wannan sarki ma'abocin sani tabbas da yarda wannan raina ke hannunsa bazan koma ga mahaifina ba har sai da mgnin matsalarsa" murmushi sarki abu ansar yyi yace" madallah da d'a nagari kuma kyakykyawan jarimi a fagen fama" rissinar dakai prince yyi alamar girmamawa ga sarki abu ansar" hannun prince akbar sarki abu ansar ya riqe suka fito, babbar hadima ga sarauniya ita ta yiwa babban prince jagora har wani babban lambu mai cike da kyawawan furanni da tsuntsaye masu dadin kuka, wata kyawawan kujeru aka tana don zaman shi, bayan fitar ta bada jimawa ya soma jiyo wani sassayyan qamshi mai kwantar da hnkli, daga kansa yyi yana kallon 6angaren da qamshin ke tahowa, gimbiya mariyatul qifdiya ce sanye da wata doguwar riga mai ruwan kwai, tayi ado na awarwaron zinare ga sarqa ga abun wuya, tasha kyau na ban mamaki, kallo daya za'a mata a fahimci diyar girma ce kuma jinin sarauta, tfy take dai dai cike da qasaita da kuma izzah har ta qaraso wurin dayake daya daga cikin hadiman dake take mata baya ta gyara mata zaman kujerar dake gefensa ta zauna, juyawa hadiman sukayi suka fice daga lambun ya rage daga ita sai babban prince, duk sunyi shiru don kowanne cikinsu yana taqama da izzah da kuma qasaita gdn sarautar daya fito, gimbiya khamriyya da kanta ta jaddadawa gimbiya mariyatu akanta 6oye soyayyarta ga prince akbar ta martaba izzar gdn sarautar abu ansar, ta bari shi ya soma sauke izzarsa gareta ya fallasa mata sirrin zuciyarshi, prince sau daya ya kalleta duk da kuwa tsantsar kyawunta irin na larabawan usul,sun jima a hk babu mai niyyar mgn cikinsu, gimbiya mariyatu kam taji ana ambatar cikakken izzah irin na wannan dan sarki amma bata ta6a zaton yakai hk ba, miqewa taga yyi ya soma takunsa mai cike da qasaita ya fice daga wannan lambu yabarta zaune tamkar an dasata, kuka ta fashe dashi tana dana sanin daukar shawarar yayarta kan ta nuna masa cikar izzarta gashi nan ya fita ya barta da izzar nata, shi kuwa prince akbar duk duniya mace daya ce zata iya gwada masa izza tasha kuma ita din ba kowan kowa bace face qasqantacciyar baiwa amma ita Allah ya dora bisa kansa ko durqusawa gabanta ze iya yi sbd ta gama da qarfin izzarsa, hadimansa na ganin fitowarsa suka take masa baya, ubaid na daga hannun damansa, bimbii ta tashi da kasala ranar sai bin jiki take babu abunda takeson ji sai qamshin jikin prince, fitowa tayi tana kwashe shanya tana zubawa cikin wani kwandon saqi, tana shiga 6angarensu ta hango dukkanin yan matan dake turakar jira sun fito farfajiya wurin sunyi jeri tana shigowa duk suka bita da kallo,ramlatul aswat ta gani tare da suwaiba sai kuma wasu qattan bayi, kallonta ramlatul aswat tayi a wulaqance cikin fada tace" ke daman gudandiyar baiwa ce daga gdn yasser bin walid amma har kk shigo wannan masarauta ta abu ansar" wani hadimi dayake cikin hadiman da suka siyo bimbii yace" tabbas bamu san gudaddiyar baiwa bace daga gdn yasser da bamu siyenta" ramlatul aswat ta galla masa harara sannan ta kalli bimbii take sauraronsu don bata gane abunda suke fada ba, turata cikin hadiman gdn yasseer bin walid ramlatul aswat tayi tace" ka baiwarku nan amma ku bawa nana hkr kar wannan zance yakai kunnen sarauniyya" hadiman gdn yasser suka ja bimbii suka fita da ita har suka fice daga masarautar abu ansar da ita, yasser bin walid shararren attajiri ne mai qarfin arziqi da yalwar bayi, sarakuna suna ganin darajarsa sosai sbd qarfin arziqinsa, yasser bin walid abokin kasuwancin prince akbar ne kuma shine ya tura ubaid wurinsa kan ya masa wannan alfarmar batare da bata lkci ba ya aika hadimansa gdn sarautar burham don aiwatar da wannan aiki, yasser ya damqa bimbii ga ubaid sai lkcin ubaid yaga bimbii shi kansa ya cika da mamakin ganinta, kamar yadda prince ya umarci ubaid hk ya aiwatar yasa bimbii cikin wani babban jirgin ruwa mai zuwa spain tare da wata amintacciyar hadima mai suna sumayya da yasser ya hadasu da ita don kula da lfyr bimbii har su isa qasar spain, sumayya mace ce mai mutuqar jarimta tamkar na maxa gata da hikima hk ta din ga kula da bimbii har jirginsu ya isa qasar spain suka wuce masaukinsu, ubaid ya isa ya sanar da babban prince jirginsu bimbii ya tashi zuwa spain, suma da yamma tawaga guda sarki abu ansar yasa suka yi masa rakiya har ya shiga jirgin ruwa tare da ubaid, sauran hadimansa kuwa suka koma ga masarautar burham suka sanar da tfyr babban prince spain don ganawa da tsohon bayahude abram dake oldest Inland, bimbii tunda jirginsu ya tsaya a port na tsayawa jiragen ruwa dake qasar spain ta fito sai kalle kalle take, gani tayi ta dena ganin masu rawani sai turawa nasarar asarar duniya, qasar spain ta mata kyau ko'ina hasken fitilu dayake da dare suka qarasa, sun sauka ne a wani orchard house mai kyau, qaramin gini ne irin na turawa amma ya tsaru sosai, ko'ina ta gefe bishiyoyin fruit ne da shuke shuke, tsarin wurin kawai akwai kwanciyar hnkli, bimbii ranar bacci tayi mai rai da lfy sbd peaceful environment din data samu kanta ciki, cikin kwana uku ubaid da babban prince suka iso qasar spain, suma a wannan orchard house suka sauka sbd tsarin wurin yana yiwa prince dadi idan ya shiga spain a wannan wuri yake rayuwarsa, nesa kadan da wannan orchard house teku ne,bimbii dai kam batasan dalilin zuwanta wannan waje ba ita dai kawai gata nan ne batasan ina rayuwarta ta dosa ba,da dare sumayya ta sanar da ita wanda ya siyeta ya iso yana buqatar takai masa abun sha, ba musu bimbii ta tashi ta hada lemon zaitun da zuma ta zuba a kyakykawan mazubi ta din ga qetare corridor har ta isa bakin dakin da prince yake,ta6a kofar tayi taji ta a bude tayi sallama ta shiga, bedroom ne mai girman gaske, komai na wannan bedroom fari ne da dark blue, everything is so cool, qamshin da take maita ta soma shaqa, prince kuwa yana kwance a tafkeken gadon dake dakin yana duba wani littafi yaji ta turo kofa, ita bata lura dashi ba kawai kallon dakin take sai data waiga wurin da wannan tafkeken gadon yake ta hango shi kwance ya tsareta da idanu,gabanta ne ya yanke ya fadi ta tsira masa idanu cike da tarin mamaki da al'ajabin ganinsa a wannan wuri, shafa idanunta ta somayi tana son tabbatarwa wannan dan sarkin ne kuwa.....
***
6angaren maheer kuwa tuni ennah ta kira faisal suka nufi hospital dashi, hnklinta duk a tashe sbd tana da masifar son yaranta,maheer yyiwa kansa rauni sosai, bayan hk likitoci sun tabbatar musu jininsa yahau dayawa a kowanne irin lkci zuciyarsa zata iya bugawa, ennah kuka take sosai sai lkcin take nadamar dauke masa bimbii da tayi har kasuwar saida bayin data kai bimbii ta koma amma wannan balaraba ya fada mata shi wlh ya saida ita dole hk ta dawo hospital din da maheer ke kwance cike da tarin dana sani, zama tayi ta tsura masa idanu, shi kuwa yana kwance duk an sanya masa oxygen a hanci da bakinsa, numfashinsa na fita a hnkli, tunani take wai wanne irin so kuwa maheer yake yiwa wannan baiwa hk, she can't imagine this kind of sacrifices until she witnessed it on her son......
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw saiki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turo da screenshrt na payment nk ta whatsapp ta wannan layi..07041195806.....
***
6angaren maheer kuwa tuni ennah ta kira faisal suka nufi hospital dashi, hnklinta duk a tashe sbd tana da masifar son yaranta,maheer yyiwa kansa rauni sosai, bayan hk likitoci sun tabbatar musu jininsa yahau dayawa a kowanne irin lkci zuciyarsa zata iya bugawa, ennah kuka take sosai sai lkcin take nadamar dauke masa bimbii da tayi har kasuwar saida bayin data kai bimbii ta koma amma wannan balaraba ya fada mata shi wlh ya saida ita dole hk ta dawo hospital din da maheer ke kwance cike da tarin dana sani, zama tayi ta tsura masa idanu, shi kuwa yana kwance duk an sanya masa oxygen a hanci da bakinsa, numfashinsa na fita a hnkli, tunani take wai wanne irin so kuwa maheer yake yiwa wannan baiwa hk, she can't imagine this kind of sacrifices until she witnessed it on her son......
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw saiki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turo da screenshrt na payment nk ta whatsapp ta wannan layi..07041195806.....