← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 59

Sashe 55

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alkalamin Bintuu neâœðŸ»
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

49

*I love you without knowing how,when*.....what I really know is that I love you so much💕💕

Murmushi tayi batare data jira ramlatul aswat ta kawo mata sakamakon binciken data tayi kan bimbii ba ta hanzarta rubuta saqon takarda zuwa ga prince akbar ta aika daya daga cikin manyan hadimanta kan ya hanzarta isar da saqon takardar ga babban prince, batare da 6ata lkci ba wannan hadimi ya samu isar da wannan takarda ta hannu ubaid tabi kafin ta qarasa ga prince akbar, zaune yake bisa kujera yana shan ruwan inibi ubaid ya shiga masa da saqon takardar ya sanar dashi saqo ne daga gimbiya mariyatu, hannu ya miqa ya amshi takardar ya warware ya soma krtw kamar hk.....zuwa gareka yakai wannan dan sarki ma'abocin cikar izzah, tabbas nayi mutuqar mamaki da wannan mace ma'abociyar qasqanci ta zamto za6i gareka matsayinka na jinin girma, wannan mace dake tare dakai ba kowan kowa bace face qasqantacciyar baiwa wacce take a turakar jira take taron duk wanda aka turata ta tara, ko kasan kafin kai ta tari tarin baqinmu da wannan jikin nata dake rudarka dashi dai ta nishadintar da was....saurin dakatawa yyi da karanta wasiqar sbd wani irin abu daya taso masa tuni idanunsa suka sauya launi suka koma jajir yyi saurin jifa da takardan, ubaid dake tsaye gefe guda kansa a sunkuye yyi saurin dago da kansa yana kallonsa, bakomai ya gani tare dashi ba sai tsantsar 6acin rai daya jima be ga irinsa a fuskarsa ba, daga masa hannu prince yyi yaja da baya kafin nan ya juya ya fice cike da mamaki, daidai lkcin bimbii ta qaraso zata shiga 6angaren hannunta riqe da wani faranti na azurfa,ubaid na ganinta yyi saurin rissinar dakai qasa alamar girmamawa sauran bayin dake tsaye a bakin kofar suma duk suka sunkuyar da kawunansu ta taka a hnkli ta shige ciki, tana shiga ta hango 6arnar da yyi duk yyi watsi da abubuwan saman table din dake gabansa, yana zaune inda yake ya riqe kansa da hannu biyu, sauri tayi ta nufi wurin ta ajiye abunda ke hannunta kan wani stool ta matsa kusa dashi, tsugunawa tayi ta dora hannunta saman kanshi tana shafa sumar kansa yana jinta yaqi dago dakansa ya kalleta domin zuciyarsa tafasa take da muggan kalaman da gimbiya mariyatu ta fada kan macen dayafi so kuma yake tsananin kishi a duniya, ita kuwa bimbii batasan abunda ke faruwa ba ita dai taga ransa a 6ace, kwantar da murya tayi cikin sanyi tace" Allah ya huci zuciyarka sadauki na" dago da jajayen idanunsa yyi wanda ita kanta saida suka bata tsoro ta bishi da kallo har ya miqe ya wuceta ya fice abin shi, abun ya bata mamaki sosai tuni gabanta ya soma faduwa ta fara addu'ar Allah yasa dai lfy, shikam yana fita kai tsaye ya wuce lambunsa batare da rakiyar kowa ba, tunani ne 2kala ke kai kawo cikin zuciyarsa, tabbas yana son bimbii shiyasa yake jin kishinta sosai har qasan ransa, itama bata bar 6angaren nasa hk ta cigaba da jiran dawowarsa har bacci ya soma janyeta ta soma gyangyadi, dare ya soma shiga sosai amma shiru ba prince yaqi shigowa, shi kuwa yana cikin lambunsa zaune saman wani dutse ya kallon taurare, garin da hasken farin wata sosai yacce ko allura ce ta fadi za'a hangeta sbd muna cikin daren goma sha hudu wata ya raba, ita kuwa tana gyangyadi tayi firgit ta farka kamar wacce aka tsikara tana kallon ko'ina, saman tafkeken royal bed nasa ta kuma kallo taga baya nan alamu sun tabbatar mata be dawo ba, miqewa tayi daga inda take ta soma bi kusurwa kusurwa ta bude curtains daya rufe kusurwar ta gani ko yana ciki ta gama duba ko'ina bata ganshi ba, jan qafa tayi ta fita ta tarar da ubaid a kofa shima duk fuskarsa ta cika da damuwa, kallonshi tayi tace" ko kana da sani kan abunda ke faruwa" shiru yyi ya rissinar dakai yace" ranki ya dade bani da sani akan komai abunda na sani kawai shine gimbiya mariyatu ta aiko da saqon takarda, wannan saqo shine silar 6acin ran prince" tana jin hk ta koma ciki da sauri domin kuwa tabbas ta hangi farar takarda a qasa tana son dubawa taga ko itace takardan da saqon ke ciki, tana shiga ta sunkuya ta dauki takardar ta soma karantawa, komawa tayi ta zauna ji6is lkcin data gama krtw wasiqar duk jikinta yyi mugun sanyi ga wata faduwar gaba dake zuwa mata, miqewa tayi a hnkli ta fice daga 6angaren ta nufi yankinta,bata jima da tfy ba prince shima ya koma 6angaren nasa, washegari, kamar yadda ta saba taci ado cikin wata doguwar riga mai kalar golden tasha awarwaraye da sarqa masu kyawun gaske sai sheqa qamshi take ta fito ta nufi dakin yaranta, tana shiga ta tarar an musu wanka suna baccinsu, peck tabi ta musu a goshi kafin ta fita ta nufi 6angaren mahaifinsu, tana shiga ta tarar da leenah tsohuwar baiwarsa ita ke masa tausa yana daga zaune idanunsa a lumshe, abun ya 6ata mamaki sannab yyi masifar 6ata mata rai, wato hkn ya nuna bashi da buqatarta kenan shine yasa a turo masa da baiwa domin ita dai tasan ita ke masa komai kuma aikin ta ne wannan baiwa take yanzu, leenah tana ganin shigowarta taqi ta dakata da tausan ta cigaba da masa tausan cike da salo, hkn ya kuma qona mata rai batasan lkcin data daka mata wata uwar tsawa ba ta nuna mata kofa fita da hannu, tsawar ce tasa shi bude idanu ya sauke akanta, leenah tsayawa tayi tana kallon prince, tsawar da bimbii ta kuma mata ne a karo na biyu yasa prince ya daga mata hannu kan ta fice ta basu wuri, jikinta har 6ari yake ta kama hanya ta fice, tana fita bimbii ta qaraso wurin dayake batace masa uffan ba ta soma masa tausan har saida ya daga mata hannu sannan ta wuce ta shige dakin wanka ta hada masa ruwan wanka hadi da sinadaran wanka ta fito, daga ita har shi babu wanda yyiwa wani mgn, shine ma ta 6angare guda yake satar kallonta don yaga sam fuskarta ba annuri kamar yadda ya saba gani, har ta gama masa komai suka fito beyi mgn ba itama batayi mgn ba, wasu kaya masu kama da pakistan masu ruwan kwai ta za6a masa yasa ta feshe shi da turarukan sunfi kala shida, tana gama abunda ya kamata ta juya da niyyar fita daga 6angaren abinta don zuciyarta har lkcin tana cikin qunci, fahimtar nufin da yyi ne yasa yyi sauri riqo hannunta ya juyo da ita suna fuskantar juna, duk sukayi shiru sai ita da kuka ke neman kwace mata, dora tsinin hancinsa yyi kan nata yyi saurin toshe bakinta da nashi sautin kukan nata be fito ba, ba zato taji yajata sun afka kan tafkeken bed nasa, ko kalma daya beyi amfani da ita ba wurin bata hkr kawai da salon soyayyarsa yyi amfani wurin isar da saqonshi na ban hkr da neman afuwa kan abunda yyi, duk da yyi nasarar kashe mata jiki da salonshi amma hk tayi qarfin tattaro dukkanin qarfinta ta ture shi daga jikinta, murmushi yyi yasa qafa ya danneta yadda ba zata iya motsawa ba, tayi tayi ta kwace ta kasa tadan soma dukan broad chest nasa cike da shagwaba har da hawayenta, murmushi ya kumayi a karo na biyu yasa hannunsa mai yalwar 2tsaran gashi ya jawota jikinsa ya matseta, tayi dan qara tana qoqarin ture shi, kafin ta ankara yyi qasa da ita ya mata rumfa, lkcin duk jikinta ya mutu murus ta tsare shi da manyan idanunta shima ita yake kallo, dayake gwani a fagen lovayya tuni ya soma harbinta da wasu kibiyoyi wadanda suke fita daga idanunsa, saurin rufe idanu tayi don bata iya cigaba da kallon cikin kwayar idanunsa, dariya yyi har jerarrun fararen haqoransa suka bayyana, kwantar dakansa yyi a jikinta ya la6e har da wani lumshe idanu yana sauke wani nannauyan numfashi, bude idanunta tayi ta soma shafa kansa tamkar wani baby tana wasa da dogon gashinsa dake kwance saman kafadansa, cikin wani irin voice yace" ina sonki dayawa, kishinki yana dawainiyya dani don Allah ki kula dani ki soni ko ko kwatan yadda nk sonki ne, ke mace ta farko da kk ta6a birgeni kece mace ta farko dana mallakawa kaina da komai nawa, just love me the way I love you pls &pls" kallon tsakiyar idanunsa tayi taga har shiny yake tamkar ze mata kuka, tunawa tayi waye akbar, namijin fama wanda besan tsoro ba, daya tamkar da dubu a fage fama shine nan yake mata wannan magiya tabbas babu abun gdy sai Allah wanda ya halicci soyayya kuma ya rayar damu a cikin alfarmarta, zagaye wuyansa tayi da hannayenta ta hade fuskarsu wuri guda har suna iya jin numfashin juna tace" kana da shakku ne kan mace da tsawon lkci take dakon soyayyarka cikin ruhi da gangar jiki, macen da bata ta6a sanin waninka ba saikai daya tilo domin kaine sirrinta, macen da jininta ya gauraya da nk, nikam yadda na baka kaina hk na damqa maka ragamar rayuwata fata ne kar ka juyamin baya har gaban abada don zuciyata bata iya son wani cikin duniya idan bakai ba" kalamanta sunyi mutuqar tasiri akansa ya sake matseta sosai a jikinsa ya kamo hannunta ya dora kan zuciyarsa tana jin bugawar numfashinta sosai, rumgume juna sukayi cike da farin ciki wannan yanayi yasa suka dulmiya wata duniya ta daban......

**
Chapter 55 · 0% Book details