Sashe 44
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Sun shirya komawa masarautar burham da abram don ya duba sarki abdallah bin jabal dakansa ya fahimci irin gubar dake jikinsa,6angaren bimbii kuwa tana zaune ita da sumayya suna hira taji mararta tayi wani irin murdewa, skipping tayi ta runtse idanunta tare da riqe mararta, cikin sauri sumayya ta matso kusa da ita ta riqeta tana mata sannu, abu kamar wasa ciwo ya soma cigaba, fita sumayya tayi da hanzari ta nufi wurin ubaid ta sanar dashi abunda yake faruwa, shiga yyi ya sanar da prince, cikin hanzari ya fito suka nufi dakin da bimbii take, ubaid ya tsaya a bakin kofa,prince da sumayya suka shiga ciki, saurin qarasawa yyi inda take durqushe riqe da mararta ya tsuguna ya riqo hannunta, sumayya na gefenta itama, kallon prince tayi tace" kamar haihuwa ce ta matso mata" saurin dago da kansa yyi yana kallon sumayya bece komai ba yyi saurin miqewa tsaye ya fita, ubaid yyiwa mgn sannan ya dawo ciki, gbdy gumi sai tsatstsafo masa yake tamkar shine yake labour din, a telephone ubaid ya kira gdn sarautan even kan suna buqatar royal doctor, bada jimawa ba even house suka turo musu da wata likita, baturiya ce ta shigo itama atleast bazata gaza shekaru hamsin ba, shigowa tayi da gudu da qaramin briefcase a hannunta, ubaid na ganin shigowarta yyi mata jagora har dakin da bimbii take ta shiga, prince na ganinta yyi saurin miqewa ya bata wuri, bude briefcase dinta tayi ta fito da handgloves ta saka cikin azama take gudanar da abubuwa, sumayya na taimaka mata prince kuwa, kasa cigaba yyi da kallon yadda bimbii ke shan azabar naquda yyi saurin ficewa daga dakin,ita kuwa bimbii wani irin ninshi take sbd ciwon da takeji bata ta6a jin irinsa ba tunda uwata ta haife sai yau, bayan ciwon naquda ga kuma wani azababben ciwon kai tamkar kanta ze rabe biyu,ita dai gbdy ta sadaqar da rayuwa sbd ta soma jiyo qamshin lahira,Dr.Margaret pushing nata take sosai, itama tana numfasawa da qarfi, prince yana bakin kofa ya harde hannayensa dukka a baya yana jiyo sautin ninshinta, idanunsa ya kada yyi ja shi kadai yasan me yakeji but still he looks very smart, cikin izinin Allah sai ga kan jariri ya fito, hannun doctorn tasa ta ciro jaririn ta miqawa sumayya dake gefe, jaririn kuwa ya charke musu da kuka, prince da ubaid kukan jaririn kawai suka jiyo,murmushi ubaid shi kuwa prince kawai so yake yaji yaya lfyr uwar jaririn, yana son shiga dakin amma yana daurewa, bimbii kuwa tasha wuya ba kadan ba gashi kanta be dena ciwo ba, hknne yasa doctorn tayi mata allurar bacci sbd ta huta, sumayya ce ta fita cike da farin ciki ta yiwa babban prince albishir bimbii ta sauka ta samu yaro namiji, sai lkcin ya shiga dakin wurin gadon da take kwance ya nufa yana kallonta tana bacci, kallo daya ya yiwa fuskarta yasan ta jigata ba kadan ba, doctorn da kanta ta dauki jaririn ta miqa masa tana murmushi, hannu yasa ya amshi jaririn ya tsira masa idanu, yaron fari ne qal gashi dogo masha'Allah, yanayin ga6o6in jaririn ya kalla yasan komai nasa ne, murmushi yyi sosai har fararen haqoransa suka bayyana, bimbii baccinta yyi tsayi sosai har kusan yamma bata farka ba, hkn ne ya tashi hnklin prince ita kuma doctorn sai kwantar masa da hnkli take sai dare ta tashi a razane, tana kallon inda take, fuskar da bazata ta6a mancewa da ita bane ta gani kusa da ita, kallonshi take sosai shima ya qura mata idanu, fashewa tayi da kuka ta dora kanta saman kafadan shi, kallonta yake cike da mamaki, ita kuwa all that past events da suka faru take tunawa ta sake dago da fuskarta tasa hannunta tana shafa face dinshi sannan ta sakko da hannunta daidai wurin da mahaifinsa ya harbe shi da mashi, hannunta ya riqe dukka ya janyota jikinsa ya kwantar da ita tana kuka a hnkli, yace" ki dena kuka baki ganin yanzu kin zama ummi" ya nuna mata babyn dake kwance a gefenta, saurin janye jikinta tayi ta komar dakanta ta kwanta ta rufe idanunta tana son tuna komai da komai ne, prince matsawa yyi kusa da ita yaja duvet ya rufeta, sunkuyawa yyi ya mata peck a kumatu, shiru tayi bata bude idanunta har saida taga ya fita daga dakin ta bude idanunta tana kallon babyn data haifa tana qura masa idanu,kuka take sosai tana tausayawa rayuwarta, tunani take yanzu idan qaddara ta kuma daukarta ta mayar da ita nahiyarta me zata fadawa su baffa da innah, tayi ciki har ta haife kenan bada igiyar aure ba, sosai ta kuma fashewa da kuka, sumayya ce ta shigo dakin ta ganta tana kuka tayi saurin qarasawa wurinta ta zauna kusa da ita tana rarrashinta da kalmomi masu kwantar da zuciya, prince komawa yyi side dinsa ya zauna ya dafe kansa, babban tashin hnklinsa mahaifinsa ne ya rasa ina ze dosa da wannan rayuwar, zuciyarsa fal take da tsantsar tausayin bimbii da babynsa dake tare da ita, har gobe yasan shine silar faruwar komai, tashi yyi da sauri ya koma dakin da bimbii take ya tarar da ita zaune fuskar nan nata babu alamar annuri, hannunsa yasa da niyyar kama mata hannu tayi saurin matsawa gefe ta dago da fuskarta tana kallonshi tace" kaga na haife muku jininku dake tare dani don Allah ku mai dani nahiyata na koma wurin iyayena na gaji da wannan rayuwar mara madafa" durqusawa tayi a gabansa ta daga hannunta alamar roqo tana kuka tace" don Allah ku maida ni nahiyata kar ka komar dani wannan masarautar na mahaifinka" shiru yyi komai ya daqule masa ya kalleta da jajayen idanunsa yace" kina son ki tafi ki barni kenan baki da damuwa, duk tsawon wannan lkcin dana dauka ina jiranki ki dawo gare ni kk dawo batare da kin iya shaida fuskata ba hk na kuma hkr har memory nk ya dawo kk gane ni amma abunda zaki iya fadamin kenan sbd baki dauki soyayyar da nk miki da daraja ba" kallonshi tayi tace" ranka ya dade ba wannan zaka duba ba, wannan son da kk fada tun farko na fada mk ze haifar da mtsl gashi silarta ne har rayuwarka ta shiga garari, mahaifinka dakansa ya harbeka da mashi duk silar wannan soyayya da kk fada don Allah kayi hkr ka taimake ni na koma qasata" wata uwar tsawa ya daka mata wacce ta sanyata shiga taitayinta, ubaid da sumayya dake waje su kansu sun razana da wannan tsawar da prince yyiwa bimbii, yace" kiyi yadda kkso" juyawa yyi ya fice ransa a 6ace sosai, bimbii fashewa tayi da kuka ita dai ta gaji da wannan rayuwar qasarta take son komawa don muguntar larabawan nan ya tsorata ta dayawa, basu dauki kisa a bakin komai ba, laifi qanqani sai su kashe rai batare da shakku ba, fushi sosai prince yyi da ita kusan kwana uku be sake shigowa inda take ba saidai sumayya ta dauki babyn takai masa duk safiyya da maraici, idan ya tuna abunda take fada wai ya maidata qasarta sai gabansa ya yanke ya fadi, tunani yake kar fa ya wayi gari ya rasa bimbii ta gudu tabar shi da dakon sonta, shi gani yake kamar bimbii ba sonshi take ba shine kawai Allah ya jarabta da soyayyarta, qanqame babyn dake hannunsa yyi yana kallonshi, idanunsa yyi ja tausayin kansa yake sosai, rana zafi inuwa quna, ta 6angaren mahaifinsa babu sassauci gata itama tana son ta gudu tabar shi, bimbii kam sai duk taji babu dadi fushin dayake da ita, tana zaune sumayya ta shigo ta sameta, kallonta tayi tace" kije ki bawa prince hkr sbd ranshi ya 6aci sosai dake tana mugun kafiya da zuciya bazai ta6a kallonki ba kar ki bari ya juya miki baya kece kadai macen da Allah ya dora akanshi" shiru tayi kawai tana sauraron sumayya, sai kuma tace"tohm" sumayya tace" ki same shi da dare a bakin teku nan yake zuwa duk dare" kallonta bimbii tayi tace" shikenan"da dare ubaid dakansa yyi mata rakiya har wajen teku, garin da hasken farin wata sosai, tunkan ta qarasa ta hango inuwarsa yana tsaye hannunsa dukka a baya ya qurawa ruwan teku ido, alamu sun nuna tunani yake mai zurfi, a hnkli ta qarasa inda yake ta tsaya a bayansa, shima ya hangi inuwarta kawai juyowa ne beyi ya kalleta ba, ita kuwa shiru tayi ta rasa abun fada, ta jima tana tsaye a wurin, juyowa yyi ya wuce ta da niyyar komawa gd, tana ganin hk tayi saurin qarasa kusa dashi ta sanya hannunta cikin nashi, tsayawa yyi chak ya juyo yana kallonta, cire hannunsa yyi daga cikin nata yyi gaba abinsa, da gudu ta kuma binsa ta rumgumesa ta baya ta qanqamesa da dukka hannayensa tana masa kuka tana bashi hkr, shiru yyi sannan ya juyo ya riqeta sosai a jikinsa duk sukayi shiru,hannunsu ta sarqe dana juna suka soma tfy a hnkli kanta na kafadarsa hannunsu na sarqe har suka qarasa bakin teku suka nemi rairayin suka zauna suna kallon ruwan teku, shiru sukayi saidai zuciyoyinsu na amsar saqonnin juna, muryarsa a hnkli cike da sanyi yace" har yanzu kina son ki tafi ki barni koh?" yanayin yadda yyi mgnr ta fahimci akwai rauni tattare da muryar nasa, dago da idanunta tayi tana kallonshi, daga hannunta tayi ta cusa a gashin kansa tana wargaza masa sumar kanshi, shikam binta kawai yake da kallo, cikin sanyin murya tace" bazan barka ba komai wuya zan kasance tare dakai" tsayar da idanunsa yyi kan fuskarta sai kuma yyi murmushi, nuna mata bakinsa yyi yace" kimin abunda zan so anan" sosai ta gane abunda yake nufi tayi saurin rufe ido ta 6oye fuskarta a saman shoulder dinsa cike da kunya irin nasu na fulani, shi kuwa dariya ta bashi yadan murmusa yace" kina son akbar?" sosai tmbyr tasa ta qara bata kunya, ta6e baki yyi kafin ta ankara sai ji tayi ta kwantar da ita a wurin rairayin shima ya kwanta ya dora kansa a saman qirjinta, dukka kansu na sama suna kallon hasken farin wata da taurarin dake watse a sararin samaniyya,hannunta ya kamo ya hade da nashi, ita kuma tana wasa da sajen fuskarsa da dayan hannunta, wannan yanayin da suke ciki ya kore musu duk wata damuwa ji suke tamkar su kadai ne a duniyar, tmbyrsa take abubuwan da suka faru dashi duk ya fada mata amma sai ya 6oye mata sanya shi a kurku da mahaifinsa yyi gudun kar ya qara mata karayar zucci, har dare ya shiga sosai basu sani ba suna nan kwance wurin, hadarin da suka gani ne yasa suka miqe suka soma tfy suna manne da juna suka nufi orchard house din da suke, kafin su isa ruwa ya tsuge sosai, hnklin prince ya tashi sosai sbd gani yyi bimbii ba wani kwarin jiki ne da ita ba ga danyen jego kar ruwan saman ya sanya mata zazza6i, itama dan qaramin hannunta ta daga wai zata kare masa ruwa amma tsayinta ya gaza kaiwa saman kansa sai dage take, dariya yyi, kallonsu tayi don ita wallah bata saba ganinsa yana dariya ba saidai murmushi,rawanin dake kafadarsa ya cire ya rufa mata amma duk da hk saida ruwa ya jiqasu, tfy suke kamar masu tausayin qasa a hk suka qarasa, dakyar ta iya kwace hannunta a cikin nashi ta shige dakin da take shima ya nufi dakin dayake, washegari, sun tashi ne da shirin komawa gd, bimbii dai gabanta faduwa yake idan taji an ambaci sunan masarautar burham, dukkaninsu suka shiga cikin jirgin ruwa tare da abram, bimbii fuskarta a rufe take kuma batare suke da prince ba tamkar ba tfyrsu daya ba sbd tsaro, sumayya tana rumgume da baby dayake cikin yalwatattun kayan sanyi, abram yana zaune kusa da ubaid, tmbyrshi yyi alaqarsu dasu bimbii, batare shakku ba ubaid ya soma bawa abram lbrin soyayyar dake tsakanin bimbii da prince mai cike da sarqaqiya da tarin qalubale, sosai wannan tsohon bayahude ya tausaya don lbrin nasu ya ta6a masa zuciya,hk har suka qarasa yankin masarautar burham, tunkan jirginsu ya iso dakarun masarautar burham suka iso don tararshi, lkcin da jirginsu ya iso fasinjojin jirgin suka soma fitowa, kamar yadda prince ya shirya tuni sumayya ta wuce da bimbii ta wani 6angare daban babu wanda zeyi tunanin tare suke da prince, bimbii fuskarta na rufe cikin niqab, sumayya tana da wayo shiyasa yaseer ya hadosu da ita, yadda prince ya umarceta ta wuce da bimbii qasarban wani asirtaccen gd ne da babban prince ke zuwa shan iska yana nesa ne sosai da masarautar burham,bimbii cike take da tunani kar wannan sarki mara imani ya ganota cikin yankinsa ya turo a kasheta ita da jaririnta,tuni tsoro da fargaba suka mata dirar mikiya...