← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 59

Sashe 20

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Wasu ne daga cikin dakarun dake tsaron gdn sarautar, suna kewayawa ne ta ko'ina cikin wannan masarauta don tabbatar da tsaro, tun kan su qaraso wurin da suke, khulood ta kallesu tace" muna cikin rikici fa idan suka ganmu"neman wurin 6uya suka somayi amma duk wurin babu wurin da zasu iya 6uya,israt ta kallesu a rikice tace" mu haye bishiya kawai" aikuwa kafin ta rufe baki sai ganinsu tayi sun rigata hayewa bishiyar dayake bishiyar tana da yalwar ganye kuma ga duhu, hkn yyi daidai da qarasowar dakarun wurin, ganin gawar layla da sukayi ne a gindin wannan bishiya yasa duk suka ja limzamin dawakansu suka tsaya, babban cikinsu ne ya fara sakkowa daga saman dokinsa sannan sauran ma duk suka sakko, duba gawar sukayi cike da mamaki don tabbas sun gane gawar na daga cikin gawarwakin yan matan da aka jefe yau, abunda ya basu mamaki shine wanda ya jawo gawar daga cikin kogi ya kawota wurin bishiyar nan, 2waige suka soma ko zasu gano wata alama dake nuna da wani a yankin wurin amma basu ga komai ba kuma basu ji motsin komai ba, babban cikin nasu ne ya gano alamar sawun kafar su bimbii dayake wurin rairayi ne, bin sawun ya somayi har ya gano daidai wurin da sawun kafar tasu ya tsaya, su bimbii kuwa dake maqale akan bishiya tuni cikinsu ya duri ruwa,israt kan rufe idanunta tayi kawai tana addu'ar Allah ya fisshesu ya rufa musu asiri kar su gano su,babban cikin nasu ya kalli sauran yace" su duba kan bishiya" israt tana jin hk ta saki fitsari a wando, bimbii da khulood kuwa sun sadaqar kawai mutuwarsu tazo,duk sunyi 2tsuro a maqale akan bishiya suka ga dakarun nan sun soma qoqarin hawowa bishiyar, daidai lkcin wani mahayin doki ya bayyana, takun sawun dokin nasa ne ya janye hnklinsu daga hawa bishiya duk suka juya suna kallonsa sanye yake da baqin kyalle ya rufe rabin fuskarsa, wucesu yyi da gudu bisa dokin nasa,hkn da suka gani ne ya janye hnklinsu suka haye dawakansu suka rufa masa baya,hknne yaba su bimbii damar sakkowa daga kan bishiya duk da hk zuciyarsu tana tsananta bugawa, sake ta6a gawar layla sukayi suka ji 2kwata ta dena numfashi alamar rai yyi halinsa, dukkaninsu kuka suke suna tfy suna waiwayen gawar layla babu halin su mata suttura hk suka bar wurin cike da taka tsantsan kar a gane takun sawunsu har Allah ya basu sa'ar komawa 6angarensu, suna shiga daki suka rufe da sakata suka hau gadonsu da gudu suka ja bargo suka rufa dashi zuciyarsu na cigaba da bugawa 2tara don gani suke kamar basu tsira ba, aikuwa basu jima ba sukaji ana buga musu kofa kamar za'a 6alla, bimbii ta rada musu kar ku sake koma waye ku bari a gane alamun tsoro ko rashin gsky a fuskokinku ku aro jarumta idan har kuna son tsira,raggo baya zama gwani damu mutu ragwaye gwara mun mutu jarumai, wadannan kalmomi su suka sanya wata sabuwar jarumta ta shigesu tashi guda, bude kofar sukayi fuskarsu da alamun nuna bacci, masu tsaron farfajiyar gdn ne suke bi daki daki na bayi don tabbatar da kowa yana cikin dakinsa a kwance, suna ganinsu suka wuce zuwa daki na gaba hk suka din ga zagaye cikin wannan dare, su bimbii kuwa rufe kofarsu suka sakeyi suna sauke ajiyar zuciya don da bayin sun zo kafin su dawo suka ga basu nan toh asirinsu ya gama tonuwa kenan sbd sai sun bincika su ga inda sukaje da wannan dare, komawa sukayi suka kwanta amma cikinsu babu wanda ya iya rintsawa don zuciyar har yanzu tana cike da fargabar abunda ze faru gobe,6angaren dakarun da suka bi bayan wannan mahayin dokin kuwa basu samu damar qarasawa wurinsa ba ma bare su iya kintata siffarsa sbd kwarewarsa wurin iya gudu da doki tashi daya ya 6ace musu suka rasa inda yyi babu irin duban da basu masa ba, dole suka koma wurin bishiyar nan suka ga ba gawar da suka bari a gindin bishiya, hkn ya basu mugun mamaki, kogin da aka watsa gawarwakin nan suka nufa suka tarar ruwa yyi gaba da kusan dukkan gawarwakin yan matan sai kadan kuma cikin kadan din da sukayi saura babu mai kama ma da wannan gawa da suka gani a bakin bishiya, so suke su gano asalin gawar sbd su bincika makusantan ta amma basu ga gawar ba, hk suka juya suka bar wurin amma sun sanar da dukkanin sauran dakaru masu tsaron masarautar su sanya idanu sosai kan kowanne lungu da saqo na masarautar, washegari su bimbii suka tashi suka shirya kowacce ta nufi wurin aikinta, sun 6oye duk wani tsoro nasu, bimbii sanye take cikin wata farar doguwar riga mai ado da kyalkyali, gashin kanta kuwa yasha gyara na musamman, kunnuwanta sanye da wasu manyan yan kunne masu kyau,hannunta kuma da wasu awarwaro, kitchen ta shiga ta hada abinci kala, bayin dake aiki a kitchen sai kallonta suke a yatsine, bimbii tana aiki ne cike da tsantsar takan tsan tsan, bata matsawa konan da can saita gama shirya komai sbd tsaro da kuma gudun kaidi da makirci na gdn sarauta, wani qaton basket ta dauka mai kyau ta soma sanya mazuban dake dauke da abincin a ciki ta dauka ta nufi 6angaren prince dashi, tana zuwa kofa ta bude ta danna kai ciki, yana zaune a wata royal chair yana rubuta wata wasiqa yana gama rubutun wasiqar ya dauki hatimin gdn sarautar burham ya danna a jikin wasiqar sannan ya rufe takardar ya sanyata cikin wani qaramin akwati, dago da kyakyawan idanunsa yyi yana qare mata kallo, ita kuwa tayi saurin yin qasa da kanta alamar girmamawa gareshi sannan ta wuce inda yake cin abinci ta soma jera masa abincin data shigo dashi shi kuwa rakata yyi da kallo kawai, bayam ta gama ne ta dawo wurin dayake tace"komai ya kammala" bece mata uffan ba ya tashi daga inda yake ya nufi wurin shimfidar alfarmar da abincin ke jera ya zauna, wurin itama taje ta soma zuzzuba masa abinci a qananan plate yana bin kowanne yana ci 2kadan, bayan ta gama bashi abinci ya koma ya kwanta akan gadonsa yace"tazo ta masa tausa" kwanciya yyi ruf da ciki ita kuma tana tausa masa baya, cikinsu babu mai mgn sai qarar awarwaron hannunta, muryarshi taji yace" ina sake ja miki kunne da ki guji sanya kanki a fitina idan kuma ba hk ba wataran zakiyi nadama mara amfani" saurin kallon fuskarsa tayi taga idanunsa a rufe suke yake wannan mgn, cike da jarumta ta 6oye tsoronta tace" zan cigaba da kiyayewa ranka ya dade" shiru yyi be kuma cewa komai ba ita kuma zuciyarta cike take da tunanin wannan mgnr ta prince, shi baya furta mgn kai tsaye saidai yyi shagu6e yabarka cikin tunani, tayi nisa cikin tunanin mgnrsa har ta dakata da tausan da take masa batare data ankara ba, shi kuwa yana ji ta dakata da tausan da take masa yasan tunanin abunda ya fada mata yanzu take, hannunsa yasa ta baya ya riqo hannayenta ya murzasu da karfi,saurin kallonsa tayi taga idanunsa a lumshe suke kuma yaqi sakin hannun nata, qoqarin janye hannun nata take a hnkli cikin dabara da hikima ya bude idanunsa ya saukesu akan fuskarta, yanayin yadda taga idanun nasa yasa tasha jinin jikinta tayi saurin sunkuyar dakanta qasa,ya jima yana mata wannan kallon qurullan da har yanzu ita ta kasa gane ma'anar kallon sai ta dauki hkn a matsayin al'adar prince akbar,yace" ki shirya zaki rakani wani wuri" rissinar dakanta tayi alamar amsa umarnin nasa,sakin hannunta yyi ya mata alama data tafi, sauka tayi daga kan tafkeken gadon nasa ta sake masa shara shara curtain din dake kame ta koma can wani gefe ta durqusa kan guiwowinta tana jiran fitowarsa, ya jima a kwance kuma ba bacci yake ba idanunsa biyu,babban hadiminsa ubaid ne ya shigo ta sanar dashi bazai samu ganin prince yanzu ba yana kwance,komawa yyi bakin kofa ya tsay yana jiran lkcin tashinsa, yana jinsu amma akwai abunda ke damunsa ne kuma yake tunani akai shiyasa yakeson kadaici, saida ya dade a kwance sannnan ya tashi ya shirya cikin wasu fararen kaya hatta rawanin kan nasa shims fari ne sol, ubaid ne ya shigo ya tsaya a wurin kujerar da prince yake ya rissinar dakansa sannan ya dago yace" komai ya tafi yadda ya kamata" ita tana tsaye daga gefe abunda taji ubaid ya fada kenan, prince ya daga masa hannun alamar shikenan, sake rissinar dakansa yyi sannan ya juya ya fita ya tsaya a bakin kofa yana jiran fitowar prince, daukar wani qaramin box yyi mai kalar ja ya miqa mata, sunkuyawa tayi ta amsa box din, bece mata komai ba ya miqe yyi hanyar waje shima tabi bayansa da sauri, a keken doki aka daukesu suka tafi wurin taron, sarki abdullah bin jabal ne dakansa ya shirya wannan qasaitaccen taro wadanda ya samu halarta wasu daga cikin manyan sarakuna na wannan nahiya, taro ne na cikarsa shekaru hamsin da tara akan mulki, masarautar burham kuma tana da shekaru dari uku da sittin da uku da kafuwa, wurin taron ya qayatu da shiri na alfarma ga kuma jini na sarauta masu ji da kansu da taqama da cikakkiyar izzah ta sarauta duk suna hakimce bisa kujeru na alfarma, ko'ina ka hanga hasken farar fata kk gani suna mgn da yaren alfarma wato harshen larabci, bimbii dai tana bayan prince akbar dayake wani babban jigo a taron, ubaid kuma yana daga gefensa na dama hk suka rakasa mazauninsa ya zauna, wurin bimbii taga bayi dayawa wadanda suke baqar fata maza da mata amma yawancinsu qasqantattun bayi ne, gimbiya hindu na daga gefe tare take itama da wasu ya'yan sarakuna,ganin bimbii a bayan prince yasa abun ya bata haushi ta kuma shirya yadda zata toxarta bimbii a taron kowa ya shaida, kade kade ne ya soma tashi a wurin irin nasu na larabawa, prince akbar kuwa duk sakan daya sai ya waiga yaga ko bimbii na nan, ubaid yana lura dashi yyi mamaki sosai na ganin yadda babban prince ya damu da lamarin bimbii, yana lura da yadda yake yawan kallon bimbii hkn tamkar wanin baqon hali ne cikin halayyar prince din don yadda ya sani prince akbar yana da cikakkiyar izzar da baya yiwa abu kallo biyu musamman mace, macen ma baiwarsa, baiwar ma wacce suke kira mara asali jinsin baqar fata, taro yyi taro sai shagali ake da kuma shan shayi irin nasu na al'adar larabawa, gimbiya hindu ce ta tashi ta nufi wurin sarki abdallah bin jabal tadan rissinar dakanta kusa dashi tace" Allah yaja zamaninka sarkin masu adalci baqinmu na da buqatar babbawar baiwa ga prince akbar ta fito ta nishadintar dasu da waqoqi masu dadi don kwararriya ce a wannan fannin" murmushi sarki abdallah yyi ya juya ya kalli badakaren dake bayansa yace" ya sanar ana buqatar babbar baiwar ga prince akbar ta fito ta nishadintar da taron da salonta" batare da 6ata lkci ba wannan badakaren ma'abocin babbar murya ya soma shela cikin muryarsa data karade wurin,prince akbar yana jin wannan sanarwa ransa yyi masifar 6aci sbd bimbii babbar baiwarsa ce dole saida izininshi zata aiwatar da wani abu amma ganin daya yyi babban bawan mahaifinsa ne yake wannan sanarwa yasan umarni ne daga wurin sarki abdallah dakansa,shiru yyi don ba yadda ya iya, bimbii ko gabanta ne ya yanke ya fadi tana tsoron fita gaban wadannan bunqasassu masu fama da izzar mulki, wasu bayi ne suka xo suka mata jagora ta tafi dakin sauya kaya, kayan da suka bata ta sanya wasu shara shara duk qaurun kafafunta a bude suke ga cikin nata shima a wangale dakyar suka janyota ta fito don dagewa tayi bata fita hk, prince akbar na daga idanu ya hango wannan shiga dake jikin bimbii take ransa ya qara 6aci ya daure fuskarsa tamau,prince nasaar na gefe yana karantar yanayin prince din har lkcin da bimbii ta hau stage, tsayawa tayi sai kalle kalle take kafin zaqaqqiyar muryarta ta soma rero wasu baitoci.....
Chapter 20 · 0% Book details