← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 59

Sashe 25

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Prince sam ya kasa control kanshi saida ya samu isa babbar headquarter yyi 6arna sannan ya soma dawowa cikin hayyacinsa, fuskar bimbii ya kalla yaga tasha kuka har ta qoshi ta koma kukan zucci, duniyar juya mata take kawai ga wani radadi da zugi dake damunta, gefe yyi ya kwanta ya juya mata baya yana fitar da numfashi a hnkli sannan ya lumshe idanunsa, zuciyarsa a wannan yanayin cike take da tsantsar nadama da dana sanin abunda ya aikata, wani 6angaren na zuciyarsa ya soma tuna masa matsayin bimbii ba kowa bace face qasqantacciyar baiwarsa, kusantar ta da yyi alfarmar ce gareta da qarin daraja, duk bayinsa babban burinsu kenan su janye hnklinsa ya kusancesu amma basu ta6a birgeshi ba, ita bimbii kuwa hk kawai yaji Allah ya jarabceshi da qaunarta, bimbii ko tana daga gefe ita kuma ji take babu wanda ta tsana a duniya sama da prince akbar, miqewa tayi zaune a hnkli taja duvet ya rufe mata kirji sannan ta janyo doguwar rigarta ta saka ta saukar da qafafunta qasa, tashi take son tayi abu ya gagara sai cixe le6e take, sauka tayi dakyar ta koma qasan floor ta durqushe tare da sanya fuskarta a tsakanin cinyoyinta tana kuka mara sauti, tashi shima yyi ya sauka ya wuce dakin wanka ya jima kafin ya fito sanye da wasu fararen riga da wando, alamu sun nuna wanka yyi, kallon 6angaren da take durqushe yyi ya matsa kusa da ita sosai ya tsuguna gefenta, hannunsa yasa ya janye dogon gashinta daya zuba mata gaba ya maidashi baya, dago da kumburarrun idanunta tayi ta ture masa hannun, murmushi yyi yace" ki tashi ki shiga ki wanke jikinki" harararsa tayi tace" akwai alfarmar da nk nema a wurinka, don Allah ka sanya a maidani inda kk tsinto ni" kallonta yyi tamkar beji abunda take fada ba, tace" idan baka sanya an komai dani inda kk tsinto ni ba toh wataqila nice ajalinka don wlh saina dauki fansar abunda kayimin sbd bani da maqiyi sama dakai" kalamanta sun bashi mutuqar mamaki wanda suka sanya ya qura mata idanu,batare data ankara ba kawai taji ya rumgumota ta baya tayi tayi ta tureshi ta gagara,kwantar dakansa yyi a dokin wuyanta ya sanya bakinsa daidai kunnenta yace" kinsan me? ko yanzu kk bani guba da hannunki zan sha,ingarman namiji kamar akbar gwara ya mutu a hannun mace kamar ki" maganar cikin rada yake mata a kunnenta,yana gama mgnr ya sake ya koma ya zauna akan wata kujera ta alfarma mai ruwan zinare ya qureta da idanu, yace" ko ki shiga wanka ko na taso" bimbii na jin hkn tayi saurin afkawa dakin wankan,sama sama tayi wankan batare data wani gasa jikinta ba ta fito, kai tsaye wurin kofa tayi da niyyar ficewa, kofar taqi budewa,durqusa tayi a bakin taqi dawo ciki,shikam be kuma ce mata uffan ba ya dauki wani littafi yana dubawa,washegari da sanyin safiya bimbii ta janye zanin gadon ta fice dashi,cikin sanda ta soma satar hanyar zuwa qorama, tana zuwa ta soma wanke zanin gadon da sauri sauri don batason kowa ya ganta, hk ta gama ta shanya babu wanda ya ganta ta koma 6angarensu, tana shiga ta tarar har sun fice, dadi taji sosai don daman bata son su fuskanci komai game da abunda ya shiga tsakaninta da prince, shiga tayi ta gasa jikinta sosai da ruwan dumi sannan ta dawo ta kwanta, wannan abu daya faru da ita yasa walwalarta da annurinta sunyi hijira,abu kamar wasa prince ya dena ganin digon rahma a fuskar bimbii, yau tana gama hada masa abun sha ta sanya a mazubi mai kyau ta dauka ta nufi 6angaren nasa, baya nan yana lambunsa sai yamma ya dawo, tana shiga ta ganshi yana rubutu jan gefe tayi bashi wuri saida ya gama sannan ya dago da kanshi yana kallonta, qara tamke fuska tayi ta soma tsiyaya masa abun sha din, cup din ya amsa ya soma sha batare da wata shakka ba,gani yyi tana kallonsa, yace" da matsala ne" ...shiru tayi kawai ta juya ta fice abinta, dare na shiga ta fito a sace ta soma sanda ta nufi wurin wannan qaton kogin da aka yada gawarsu bimbii batare da wani tsoro ba ta afka cikin kogin kuma gashi bata iya ruwa ba.......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

21

*If words were sufficient enough to ease out your sorrow and pain*.....I will keep talking never ever stop it even beyond after.....💕
Chapter 25 · 0% Book details