← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 59

Sashe 56

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

6angaren gimbiya mariyatul qifdiya kuwa tayi mutuqar dana sanin saqon data tura ga babban prince sbd ramlatul aswat ta kawo mata binciken da tayi kan bimbii, cikin binciken kuwa taji ashe jikin dake cikin bimbii a lkcin na babban prince ne, wannan abu taji shi kamar al'mara, cikin wasiqar data yiwa prince ta sanar dashi mgnr cikin dake jikin bimbii a lkcin da take turakar jira wai na wani ne cikin bayinta tayi hkn ne don ta tozarta bimbii ta shafa mata baqin fenti a idanun prince, sai dai yanzu take ganin tsantsar shirmenta data fahimci ashe wai prince shine mamallakin cikin dake jikin bimbii tun lkcin,prince akbar kuwa daman bekai ga qarasa karanta wasiqar nata ba ya jefar da takardar shiyasa be ga wannan rubutu nata ba dake nuni da tsagwaron rashin sani daya fi dare duhu, wata dariya tayi mai tattare da tsantsar baqin ciki mara misaltuwa, tana jin tsananin tsanar bimbii cikin ranta wato kenan babban prince ne ya amshi budurcinta bata sani ba, wannan abu shi yafi komai dungunxuma tunaninta, yanzu data san cikakken lbrn bimbii sai taji tafi tsananta da kishi da ita fiye da kafin tasan wacce ita,6angaren sarauniya kuwa tuni tasa an damqe ummu nana batare da sanin kowa ba aka turata kurku, ta sauya sabuwar babbar hadima, komai yanzu cikin taka tsantsan take yinsa don abunda ummu nana tayi mata yasa ta soma sanya rashin yarda ga dukkanin bayinta,sarki abdallah kam jiya iya yau jikin nasa don ya kasa kwantar da hnklinsa ya rumgumi hukuncin Allah gani yake yana da mafita kullum, duk wanda yyi damarar ja da ikon Allah sai muce ga fili gamai doki.........

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki tura screenshrt na payment nk ta a whatsapp ta wannan layi...07041195806,

Alkalamin Bintuu neâœðŸ»âœðŸ»âœðŸ»âœðŸ»
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

50

*I always confess to your love dear*.....I gave you my heart, I just want you to stay behind me everyday cox u are my woman💕💕only me!

6angaren maheer zamu iya cewa jikin nasa babu laifi, yana kwance a gadon asibitin likitan dake duba shi ya shigo dayake kamar friends suke don tare sukayi medical college, jan kujera yyi dake kusa da gadon maheer yyi ya zauna yana kallon maheer dake qoqarin tashi zaune, taimaka masa yyi ya tashi ya koma shima ya zauna, kallonshi yyi sosai cike da tausayawa yace" ya kk jin jikin nk yanzu" murmushi yyi yace" jikin da sauqi" murmushi doctorn yyi sannan yyi gyaran murya yace" matsayinka na likita ko ban fada mk ba nasan kasan condition din da lfyrka ke ciki, don Allah doctor ka manta da yarinyar nan kamar yadda itama ta mance dakai tayi aurenta just forget everthing about her and let her go, free yourself frm worries, stop torturing yourself cox of woman u are capable to live alone without anyone support,pls man ka tausayawa mahaifiyarka da masoyanka,wannan itace alfarmar da nk nema a wurinka doctor" murmushi maheer ya dago dakansa yana kallon doctorn yace" kar damu doctorn zanyi iyakar qoqarina na mance da shafinta cikin rayuwata kamar yadda itama tayi" fadada murmushi doctorn yyi yace" sound good! keep praying by God grace u will succeed" duk sukayi murmushi, miqewa likitan yyi ya miqa masa hannu sukayi shaking hands sannan ya juya ya fita, komawa yyi ya jingina da pillow ya qurawa wani 6angare na dakin ido, tsanar bimbii ne kawai yakeji ya cika masa zucciya,gani yake idan da Allah zesa ya hadu da ita sai ya shaqeta ta mutu har lahira kowa ya huta sbd wani irin tsanarta yakeji cikin ransa, duk da wannan feeling din dake naso a sararin zucciyarsa qasan ransa soyayyarta ne fal, gsky bimbii tabar masa babban ta6o da har yabar duniya bazai sashe ba, yaci alwashin mantawa rufe babinta ya lalla6a ya cigaba da rayuwarsa cikin walwala, washegari akayi discharge nasu, ennah sai lalla6ashi take komai yake so shi take masa, fitittikewa mata yyi kan shi gdnsa ze wuce ba yarda ta iya dashi hk suka masa rakiya har gdn nashi ita da faisal, masu aiki har uku ta daukar masa sbd tsabar gata, maheer hali a qoqon rai rashin mutuncin nasa har yanzu yana nan amma kashi hamsin ciki dari ya ragu, masu aikin nasa duk maza ne komai masa suke, wani lkcin idan ya zauna shi kadai tunanin bimbii sai ya soma bijiro masa amma yyi ta yaqi da zuciyarsa don kam shima kansa yasan ta masa nisa, toh mudai muna masa ftn alheri Allah ya qara masa dangana........

***

Mariyatul qifdiya ba shiri ta soma haramar komawa gd, zuciyarta cike da damuwa 2iri, damuwarta na farko shine ta tabbatar bata da gurbi ko kadan a wurin babban prince sannan gashi tana masifar shakkar tunkarar mahaifinta kan kunyata shi da tayi a idon duniya,hk dai sukayi shiri tfy, sarauniya ta hadata da dakaru su rakata har boader ita da tawagarta, cikin sanyin safiya suka dauki hanyar komawa masarautar abu ansar,cikin hukuncin ubangiji suka isa lfy, saidai tunda ta koma ko kadan bata ga fuska a wurin mahaifinta ba har tsawon kwana uku, yayarta gimbiya khamriyya ita ta bata shawara kan ta fuskanci mahaifin nasu da batu na neman gafara don yyi fushi mai tsanani da ita, batare da wata gardama ba ta tunkari mahaifin nata, tabbas ta nuna tayi nadama kuma tayi masa alqawarin zata manta da yarima akbar ta rumgumi duk wanda ya za6a mata, hkn shine ya sanyaya ransa ya sakko daga fushin dayake da ita, yyi mata nasiha sosai kan tsautsayin dake tattare da bijirewa umarnin mahaifa, Allah ya bamu ikon rabuwa da iyayenmu lfy ya kuma bamu qarfin guiwan yi musu biyayya, 6angaren masarautar burham kuwa babban prince shine yake gudanar da dukkanin abubuwan daya kamata sarki abdallah ya gudanar sbd shine daman magajin masarautar, ammar, adeel, areef tubarkallah masha'Allah sun fara wayyo sosai ga wani irin girman jiki da suka taso dashi abunka da ya'yan hutu kuma jinin girma, bimbii kam bata da wata mtsl daya wuce ta ziyarci nahiyarta don ta gana da danginta da iyayenta su ganta ta gansu, bimbii kan qaddara ta fito da ita duniya ta tako arziqi, bata ta6a fadawa prince cewa tana son zuwa africa ba shima kuma be ta6a tmbyr kan hkn ba saidai ya shirya tsaf don bata mamaki, yau da dare aka kai masa ya'yansa 6angarensa ya shirya ya nufi yankin mahaifinsa dasu, gbdy yaran basu dauki komai na bimbii ba, hk suka fito larabawa ziryan tamkar ba ruwa biyu ba, areef kan idan ka gansa kaga kakansa kamar har ta 6aci, lkcin da sarauniya, prince da bimbii suka shiga dasu wurinsa kawai da kallo yabi yaran idanunsa suka saukan kan areef da shi kansa ya gano kamanninsa da yaron ko prince dayake dansa beyi kama dashi hk ba, saurin dauke kansa yyi gefe, idan ya tuna baiwa ce ta haifi yaran sai baqin ciki ya tokare shi, hmm, niko nace lalle kam wallah bimbii yanzu ta zarce ajin ka kirata baiwa ka gyara tunaninka tsoho,atoh, bimbii na daga bayan prince riqe da adeel, be ganota ba saida prince yyi gefe ya hangeta tayi saurin rissinar dakanta cike da faduwar gaba don wallah har yanzu tana masifar shakkar wan ga tsoho daya kusa zama ajalinta, tsayar da idonsa yyi akanta yana mamaki sauyawarta gbdy tamkar ba wannan baiwa daya sani ba wacce ta kawo masa fitina a masarauta, bimbii uwar tsoro kamar farar kura, jikinta sai rawa yake sauran qiris adeel ya su6uce daga hannunta, hnklin kowa yakai kanta, murmushi prince yyi don ya fahimci tsoron mahaifin nasa take, hannu yasa ya amshi adeel din daga hannunta, take mata qafa yyi tayi saurin dago dakanta tana kallonshi ya kashe mata idanu, sarki abdallah yana kallonsu, tashi yyi zaune ya miqa hannunsa ga sarauniya dake riqe da ammar ya amshi yaron, duk suka kalleshi cike da mamaki, matsawa prince yyi kusa dashi ya miqa masa areef, kallon areef yyi ya saki murmushi yace" Allah ya rayaku yasa kar kuyi za6i irin na mahaifinku" shiru kowa yyi suka sunkuyar dakansu qasa, ya jima yana kallon yaran sannan ya dauke ido a kansu ya maida kan bimbii, kallon sarauniya yyi yace" ku fita ina son mgn da uwar yaran" gaban prince yyi masifar faduwa ya kalli mahaifin nasa, bimbii kuwa saurin riqo hannun prince tayi cike da tsoro, da ido ya mata alama kan karta damu babu komai, janye hannunsa yyi ya juya ya fita itama sarauniya tabi bayansa ya rage daga bimbii sai sarki abdallah, nuna mata kujera yyi da hannunsa ta zauna jiki a sanyaye, tana sauraron abunda wannan tsoho ze fada mata,duk da batasan abunda ze fada ba amma tana da tabbacin ba alheri bane ze fito daga bakinsa musamman yadda taga ya tamke fuska kamar wanda yaga mutuwarsa.........

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screen shrt na payment naki a whatsapp ta wannan layi...07041195806.......

Alkalamin Bintuu neâœðŸ»
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

51

*You will always be mine even if we are miles apart*........your love is a blessed to me,huuuu lovvey💕💕
Chapter 56 · 0% Book details