Sashe 58
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yammacin talata jirginsu ya tsaya a babban port na tsayawar jiragen ruwa dake birnin ikko wato lagos, that yoruba man mr.oluwola shine yyi musu jagora wani hadadden gd na shegun nairori dake victoria Inland, israt da khulood basu zaci akwai beautiful environment a qasashen africa hk ba coz sudai yadda suke gani yunwa da tsantsar talauci ya qare a qasashen baqar fata, victoria lnland kowa ya sani matattara ce ta isassu kuma bunkasassun masu hatimin nasara, ita kanta bimbii bata zaci akwai wuri mai kyau da tsaruwa a qasarta irin hk ba sbd ita dai kam bata ta6a ziyarar wuri makamancin nan ba don matsayinta bai kai nan ba, kwanan su biyu a lagos suka hau flight ya saukesu a garin gombe tun lkcin gombe na cikin maiduguri, bimbii bata gama tsinkewa da lamarin ba saida taga wasu fitinannu hadaddun motoci masu numfashi dai dai har shida sun zo daukarsu, itakam har tsoro abun ya bata, hmm, nikam nace toh ai daman tuwon girma dole miyarsa da tsoka, hk motocin suka kwashesu zuwa fadar mai martaba shehun borno, ranar kam bimbi saida tayi kuka bakomai ne yasa ta kuka ba kawai tarbar girma da kuma karimci data gani a wannan gdn sarauta, sun samu tarar girma wanda yafi qarfin na kwatanta muku shi da bakin alqalami na, daga nan aka wuce dasu royal louge na masarautar borno nan suka sauka, su israt kam nasu ido don basu jin yaren fulanci bare kanuri, larabci nan dai shine yarensu, kwanansu biyu shehun borno ya shirya musu shiga rugar lamido dake cikin gombe, lkcin da tawagarsu tahau hanyar shiga wannan ruga bimbii tayi mamaki sosai don yadda ta zata ba hk ta gani ba, rugarsu daba hanyar shiga mai kyau amma yanzu tfy motocinsu keyi kan hadaddiyar kwalta baqa qirin alamu sun nuna ba'a jima da shimfida kwaltar ba wanda silar zuwansu shehun borno dakansa yyiwa gomnan jihar mgn akayi wannan kwaltar don fita kunya, akan kwalta suka din ga tfy har motocinsu suka tsaya a kofar gdn malam abba wato gdnsu bimbii, duk da sauye sauye na cigaba da aka samu hkn be hanata kasa gane gdnsu ba, sun samu rakiyar jami'an tsaro sosai da masarautar borno ta basu don kare lfyrsu, baffi da lamido na zaune kan tabarmar dake saman dandamalin kofar gdn suka hango wannan tawaga ta motoci, jerin gwanon motocin shine ya janyo hnklin jama'a suna kallon motocin cike da mamaki ina zasu tsaya, baffi ya kalli lamido yace" wadannan motocin kuma daga ina ko gomnan jihar ne ya shigo mn" lamido da idanunsa na kan motocin yana son ganin inda zasu tsaya yace" tab, ni motocin har tsoro suka ban, gsky wannan tawaga ta gomna ce" shiru sukayi suna kallon motocin dake daukar idanu ga mamakinsu suka ga sun soma tsayawa a kofar gdn, hadimanta ne sukayi saurin fitowa suka bude mata kofar mota, lamido da baffi idanunsu duka na ga wannan mota suna son ganin wanda ze fito, qafar mace suka fara gano fara sol da ita don kuwa qafar bimbii tasha hutu yadda ya kamata, sanye take da wani heel din takalmi mai igiya, fitowarta ne sanye cikin farar doguwar riga da mayafinta ya sanya yawun bakinsu kafewa suka qura mata idanu babu ko qiftawa, fuskarta dauketa take da tsantsar farin ciki dawowarta gd, tana ganin mahaifinta ta saki ihu ta qarasa da gudu ta qanqame shi da tsantsar murna da farin ciki, baffi kam ji yake kamar mafarki yake ya zama kamar wani mutum mutumi, kawai kallonta yake, lamido kuwa daskarewa yyi don ya kasa motsin kirki kawai kallonta suke,a hnkli baffi ya furta sunanta yace" khadijah! khadijah ke nk gani da gaske ba'a mafarki ba" murmushi tayi tace" baffi ba mafarki kk ba nice da gaske, na dawo gareku" hawayen farin ciki ne kawai ya soma sauka a fuskar mahaifin nata yana kallonta,goge masa hawaye tayi da hsnnunta tace" baffi na dawo" kallon lamida tayi daya kafeta da idanu tayi murmushi tace" hamma lamido na sameku lfy" kasa mgn yyi sai kallonta kawai yake, baffi ya kalli tawagar dake tare da ita sai ya rige hannunta suka shiga cikin gd, sumayya,israt,khulood na biye da ita hannunsu riqe da yan uku sanye cikin kayan alfarma, inno na kwashe shanye juyawar daza tayi don miqa kayan shanyan cikin daki idanunta suka sauka kansu, gabanta yyi wani irin bugawa tuni kayan dake hannunta suka watse ta quresu da idanu bakinta sai motsi yake amma ta kasa mgn, bimbii ta ruga da gudu ta rumgumeta qam kawai sai kuka ya kubce mata, inno ta riqeta qam tamkar zata gudu tace" khadijah! kece da gaske nk gani gabana" qara qanqameta tayi tace" nice inno,nice kk gani" fashewa tayi da kuka har da majina tace" Allah na gode mk daka nunamin wannan rana,Allah na gode mk,Allah na gode mk" take kuka yaci qarfinsu gbdy saida baffi yyi gyaran murya tukun yace" kukan ya isa hk tana tare da baqi" a hnkli inno ta maida kallonta kan kyawawan yan matan larabawan dake tsatstsaye hannu kowacce cikinsu riqe da jariri suna kallonsu, mamaki ne sosai ya bayyana akan fusksrta ta juya ta kalli bimbii tace" wadannan larabawan ma tare kk dasu" murmushi bimbii tayi tace" eh tare muke" tashi tayi da sauri ta shiga daki ta fito da qatuwar tabarmar kafa ta shimfida musu suka zazzauna, suna gaida ita cikin harshen larabci, itakam shiru tayi kawai tana son jin yadda diyarta ta samu rakiyar wadannan larabawa, lamido na tsaye can gefe yyi nisa cikin tunani yanzu kam ya tabbatar bimbii itace jikin wannan jarida daya gani, tsoro tare da rudani tuni sun dade da masa qawanya don kallon farko kawai daya mata yasan bimbii ta masa nisa, sallamar yaddiko da hauwa'u tare da wasu matan ne yasa suka waiga, hauwa'u kasa qarasowa tayi lkcin da idanunta ya sauka kan qanwarta ta, abu kamar al'mara bimbii ta koma balarabiya, miqewa bimbii tayi ta qarasa ta rumgumeta suka fara kuka hk dai suka qaraso ciki suka nemi wurin zama, batare da wani 6ata lkci ba bimbii ta soma gabatar musu da mutanen dake tare da ita, kowa yyi shiru suna sauraronta har lkcin data soma musu bayanin komai ta kuma gabatar musu da jikokinsu, Allahu akbar! Allahu akbar!! kalmar dake amsa kuwwa kenan a wannan wuri, lalle godiya ta tabbata da wanda yyi rayuwa da qaddarar dake cikinta, maxan sune masu qarfin hali amma kaf matan dake wurin kuka suke, hk kowa ya din ga amsar yaran yana yabawa da kyawunsu, inno zubawa yaran idanu tayi hawaye na fita daga idonta,Allah abun godiya ita ko cikin mafarki bata ta6a irin wannan mafarkin ba, yau dai ga qaddara ta kawo mata jikoki larabawa, itace wai yarta ta auri dan sarki kuma balarabe yaren fiyayyen halitta,tsawon rayuwarta bata ta6a farin ciki irin na yau ba, tuni gdn ya soma cika da jama'a, dangi da abokan arziqi suna shigowa taya murna, rugar nan ta dauka bimbii yar gdn malam abba tayi gamo da arziqi, bimbii ta tako arziqi abunda mutane ke fadi kenan, yadikko ta kalli inno tace" ki gode Allah ke kam kinyi farar haihuwa irin haihuwa da akeso" lamido tuni ya sallama shima yasanya yan uku albarka amma a zahiri shi kadai yasan me yake ji a zucciyarsa saidai dole ya yarda da qaddara kuma ya rumguma,satinsu biyu suka soma shirin komawa don prince ya aiko da saqo kan su hanzarta komawa gd, bimbii sam batason komawa batason sake barin gd, saida baffi yyi da gaske tukun ta soma shirinta,inno kuka take gani take idan bimbii ta tafi bazata kuma ganinta ba saida bimbii ta din ga kwantar mata da hnkli tukunna, ranar asabar tayi sallama da yan'uwa da abokan arziqi suka dauki hanya sai birnin ikko, daga nan kuma jirginsu yahau saman teku, kwanan biyar a saman ruwa jirginsu ya isa qasar kuwait, tunkan su iso tawagar zuwa tararsu take jiransu, 6angaren prince kam satin ukun nan da ba bimbii kusa dashi ji yake tamkar shekara,yyi kewarta mutuqa ga begen yaransa dake qunshe cikin zuciyarsa shiyasa ya musu aike don qara tunatar dasu, bimbii ta koma masarautar burham, ranar prince rasa inda ze cusa ransa yyi sbd farin ciki, itama tayi kewarsa sosai hk suka rumgume juna, watanta daya da dawowa majalisar nadin sabon sarki ta fitar da sunan prince a matsayin sabon sarki, ranar nadi bimbii taga shagali da wasu kalar 6oyayyun al'adun larabawa daya birgeta sosai, bimbii ta zama sarauniya a qasar larabawa cikin ikon Allah, cikin shekara daya sauyi sosai ya samu cikin wannan masarauta, tozarci da daukar bawa a matsayin wani abu wulaqatacce tuni yakau cikin gdn sarautar burham, bimbii ta taka muhimmiyar rawa wurin kawo sauye sauye mai tarin yawa a masarautar burham, bimbii itace sarauniya ta farko a wannan masarauta da sunanta ya fita sosai cikin qasar kuwait, ta zamto wata tauraruwa dake haske alqarya, a shekarar alif dari tara da sitti da biyar ne bimbii tayi wata hira da yan jaridu tayi kushe sosai kan yadda mahukunta na duniya suka zuba idanu kan cinikin bayi, wannan furuci nata shine ya janyo cece kuce wanda hkn ya jawo hnklin masu fashin baqi da kuma masu fafutikar kare haqqin dan adam suka fara tofa albarkancin bakinsu kan furucin nata, ana cikin hk majalisar dinkin duniya ta kafa dokar cinikin bayi a dukkkanin qasashen duniya, tabbas masarautar burham suna alfahari da bimbii, cikin wani taron yan jaridu da suka taba kai mata ziyara nan taga farhan shima ya zama shararren dan jarida, sosai tayi farin cikin sake haduwa da wannan mutane da suka nuna mata halarci cikin rayuwa........
*BURHAM KINGDOM AFTER 25YEARS*âšœï¸
âšœï¸
*BURHAM KINGDOM AFTER 25YEARS*âšœï¸
âšœï¸