← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 59

Sashe 59

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Wasu kyawawan samari na gani masu kalar larabawan usul, yarima ammar yana da tsayin gashi irin na mahaifinsa saidai na lura sosai prince ammar akwai cikar izzah da qasaita har ma yaso ya zarta mahaifinsa, princes adeel,prince areef kuwa hali suka gado irin na kakansu shegen kafiya da nuna mulki, sai kuma qannesu biyu prince abdallah da prince abdul jalal,sai kuma mace daya gimbiya afiya, bimbii ta cika gdn burham zuri'arta, sarauniya mar'atuusaliha tana tsananin son jikokin nata kamar me kunsan dai larabawa da shegen shagwa6a yara tana nuna yaran gata, bimbii da king dinta kam har yau soyayyarsu tamkar sabuwa basa gjy da juna, ita gani take kamar ma kullum sonta hawa yake a zuciyar king din nata, kusan dukkanin yaran nata a london sukayi krtunsu sai idan sun gama suke dawowa masarauta, lkcin da bimbii ta halarci wani taro na campaign against breast cancer ne ta hadu da maheer, yana cikin manyan likitocin da suke cikin wannan campaig, maheer ya manyanta shima, sun gaisa cike girmama juna, maheer yyi aure ya auri wata baturiya yar qasar german, ganinta bimbii a zahiri yaso fama masa da tsohon ta6o duk da kasancewa girma ya shigesu yanzu amma son bimbii har yau yana nan qasan zuciyarsa kawai dai ba yadda ya iya ne don kuwa Allah ya zartas da hukuncinsa, king tattalin bimbii yake kamar kwai, israt da khulood har da sumayya duk sunyi aure cikin daidaito don bimbii ta nuna musu halacci, ubaid shima yyi aurensa kuma har yau shine na hannun daman king akbar................END.

ALHAMDULILLAH!

Anan na kawo karshen wannan littafi nawa mai suna..... *DAREN GOMA SHA HUD'U*....saqon dana isar daidai cikinsa ALLAH ya amfanar damu dashi wanda na kuskure kuma ALLAH ya gafarta mana....

Masoya ina qara godiya da jinjina gareku na hkr da kkyi dani har na sauke wannan littafi, ina ftn sake kasancewa daku a sabbin littattafai na masu fitowa nan gaba, addu'oinku da kuma fatan alherin da kk bina dashi kodayaushe shine jigon dayasa bintuu ta zama kainuwa dashen ALLAH a duniyar marubuta ku cigaba da mini fatan alheri da addu' oin alheri, ubanhiji yabar qauna....son so jama'ata!ðŸ¤anan zan dire alkalamina sai kun jini a littafi na gaba.

Alkalamin Bintuuu ne.....
Chapter 59 · 0% Book details