← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 59

Sashe 50

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikinta yyi girma sosai tayi wani d'an lukutin kyau,fatar jikinta sai kyalli da sheqi tana glowing, hutu ya zauna ga bakinta ya fara fitar da inglishi yadda ya kamata, dayake masu abun dakansu ke koyar da ita harshenta ya karye da turancin cikin sauri gata dama da yaren fillo da larabci a bakinta sai turancin nata yake fita tamkar wata haifaffiyar ingila, duk wanda ya kalli bimbii a yanzu yasan yyi gamo da matar manya, bata aiki fari bare na baqi komai mata ake hutun har yaso ya mata yawa, yadda take sha'awar qafar prince dinta da take luwai luwai kamar tumatir hk nata qafar ta koma itama, prince kuwa kawai fama yake da kewar bimbii gashi babu damar yakai mata ziyara don sarki abdallah ya jibga masa duk wani nauyi nasa komai shike gudanarwa bashi da lkcin kansa sai na masarauta, saidai saqon shi yana tarar da ita 2akai kuma suna mgn ta telephone don lkcin babu wayar tafi da gdnka, yauma tana zaune kan cushion tana shan bornvita sumayya ta shigo ta rissina gabanta ta sanar da ita telephone din dake bedroom na yana ringing, tashi tayi dakyar ta nufi bedroom din ta zauna bakin gado ta janyo qaramin stool din da telephone din ke kai ta daga ta sanya a kunnenta, sweet voice nashi taji yana mgn cike da sanyi, shiru tayi bata tanka masa ba, shima sai yyi shiru, duk sukayi shiru suna sauraron bugun numfashinsu ta cikin telephone din, cikin wata maraitacciyar murya yace" can't you talk to me?" tura baki tayi gaba kamar tana gabansa ta sauke numfashi cikin sanyin murya tace" I really miss you, can't you come back to me?" numfashinsa yaja sannan yace" I miss everything about you baby" kwantar dakanta tayi tace" toh yaushe zaka zo" tayi mgnr ne cikin harshen larabci, murmushi yyi har tana iya jiyo sautinsa yace" yaushe kk son nazo me kk shirya na tara ta keda kkmin rowa abun ma" tace" kullum mafarkin ka nk, ina son ganinka" dariya yyi yace" yy lfyr babyna, ina son kina bashi kulawa na musamman" tace" he just want to see you" yace" I guess this woman miss me so much" dariya tayi suka soma hirarsu irin ta masoyan da sukayi nesa da juna suke kuma begen haduwa, sun jima suna hira har saceta saida yaji tayi bacci sannan ya ajiye kan telephone din, prince be leqa ingila ba saida cikinta ya cika wata na tara yyima qasar dirar mikiya,lkcin daya ganta kasa mgn yyi ya tsaya kawai yana kallonta don ta koma masa wata daban tamkar ba bimbiin daya sani ba, sai kuma ya soma takawa a hnkli ya qarasa wurinta ya dagata chak ko kunyar hadiman dake wurin beyi ba ya wuce da ita ciki, su kuwa hadiman dayake turawa ne hkn ba wani baqon abu bane a wurinsu hk suka cigaba da ayyukansu, prince be direta ko'ina ba sai saman royal bed din dake side din dayake, gbdy ta kasa gane masa daga zuwa kuma babu wani zance sai na biyan fashi da qarayi,ranar bimbii ta gane kurenta tun tana bashi hadin kai har ta soma kuka tana ture shi, shi kuwa ina ai sai daya fanshe kafin hnklinshi ya kwanta, janta yyi ya qanqameta yana bata hkr yace" kin qara kyau sosai fa my princess" dauke kanta tayi wai ita tayi fushi ya jiyo da kanta ta ture hannunsa, sai shima ya juya baya abinsa ya kyaleta, tana ganin hk ta matsa ta rumgumesa ta baya, juyowa yyi yana murmushi ya shafa qaton cikinta yace" wannan cikin yafi na baya girma" shiru ta masa tana kallon gashin kansa daya sake tsayi kamar na mata, hannunta ta dora akansa tana jan gashin nasa, ranar ta kasance wani farin dare ga wadannan masoya da suka jima rabonsu da juna, bimbii kamar jiran zuwan mijinta take kwana uku da zuwansa da sanyin safiyar litinin ta soma naquda, batare da 6ata lkci ba aka turo musu royal doctor, wannan haihuwar bata jima rana labour ba sai ga kan jariri ya fito, likitan tasa hannu ta fito da jaririn yana kuka, cigaban da tayi da labour ne ya dawo da hnklin likita kanta, sumayya na tsaye daga gefe tare da wata midwife itama jar fata, midwife din ce ta amshi dayan jaririn ita kuma likitan ta matsa wurin bimbii ta cigaba da taimaka mata har kan wani jaririn ya kuma fitowa shima suka fito dashi amma bimbii bata dena naquda ba sai ga kan na uku shima ya biyo baya, prince dake tsaye gefe matsowa yyi kusa sosai don be fita daga room din ba a gabansa bimbii ta haifo wadannan zaratan mazaje guda uku, kwatanta farin cikinsa a wannan lkcin ba'a mgn jikinsa har tsuma yake ya miqa hannu yana son amsar na qarshen, likitan ta janye hannu saida suka yanke musu ci6i suka gyarasu sannan ta miqa mishi dayan, dukkaninsu fuskokinsu dauke take da tsantsar farin ciki suna taya prince murnar samun wannan kyauta daga Allah, bimbii kam takanta take kawai burinta kawai ta kwanta ta huta, sumayya ce ta kamata suka shiga bathroom ta hada mata ruwan dumi, midwife din nan tayi mata wanka irin nasu na likitocin turawa mai cike da taka tsantsan, tana fitowa daga wanka taga dakin a gyara tsaf, har suma yaran an musu wanka an shiryasu cikin kayan sanyi dayake yanayin qasar akwai sanyi sosai, prince na fita hadiman gdn sai taya shi murna suke, murmushi da farin ciki ya kasa barin fuskarshi, ji yake tamkar a mafarki wai shine aka haifawa yara har uku dukkaninsu maza masu kama dashi, an dakatar da dukkanin hadiman gdn shiga 6angaren da bimbii take ita da yaranta, sumayya itace kawai hadimar dake kai kawo a wannan 6angaren sbd tsaro sai kuma likitan yara da prince ya dauko don duba lfyr jariran nan yan gaban goshi, abunku da jinin sarauta basu son zuwa asibiti qwararrun likitoci ke basu home treatment, bimbii tamkar ba mai jego ba hnklinta kwance cike da qoshin lfy ga soyayyar miji ta samu,zero tension hk take, kulawa take samu fiye da tunanin mutum wurin prince da dukkanin hadiman take gdn,ubaid kam tamkar shi aka yiwa haihuwa sbd farin cikin daya nuna, dakin guda aka cika da kayan babies da dukkanin abun buqatarsu, bimbii tana zaune ita kadai kawai hawaye ya soma sauka mata a kumatu, bakomai ta tuna ba sai iyayenta da danginta zata so ace sun ga yadda Allah ya qaddara mata nata rayuwar tasan sai sun fi kowa farin ciki, bata sani ba kawai taji hnkchf nasa a saman fuskarta yana share mata hawaye yace" meye abun kuka ga kyauta Allah yyi miki" nuna mata inda babies din ke kwance yyi kowanne a gadonsa irin na kwantar da jarirai,lbrin wannan haihuwa na bimbii tuni ya samu isa masarautar burham, sarauniya mar'atussaliha har sujudun shukr tayi na nuna farin ciki da godiya Allah, 6angaren sarki abdallah haihuwar tazo masa a bazata musamman dayaji cewa har yara uku dai wannan baiwa ta kuma haifa kuma dikkaninsu maxa, hkn ya tabbata baiwa ta zama uwa a wannan masarauta don ta haifi magada,baxan iya kwatanta muku baqin cikin dake qunshe a zuciyar sarki abdallah ba, hk ya din ga sauke fushinsa akan bayi yana aikasu kurku koma ya yanke musu hukuncin kisa, sati daya da isar saqon haihuwar sarki abdallah ya soma ciwo 2sama abu kamar wasa dare daya ya gamu da bugun zuciya sakamakon baqin ciki da takaici daya masa yawa,wannan shine silar dayasa sarauniya ta aikawa prince saqo ya dawo gd mahaifinsa babu lfy, shi kadai yyi niyyar komawa masarauta amma sarauniya tace dole ya taho da bimbii da yaran don su gansu, ba don ya so ba suka soma shirin komawa, ranar alhamis jirginsu ya hau saman ruwa suka nufi komawa nahiyarsu, safiyar laraba suka isa yankin burham, hadimai ne ta ko'ina suka zo tararsu, hk suka qarasa gdn sarautar burham kai tsaye prince yyi umarni sumayya ta wuce da bimbii 6angarenta, hkn shine ya kawo tarnaqi cikin gdn don 6angaren sarauniya yakamata a wuce da maijego da yaranta amma mirtsitsi prince ya take wannan al'adar yaqi bari a wuce da bimbii da jariranta sashin sarauniya, wannan abu ya hasala sarauniya sosai kuma ga ummu nana sai qara rura wutar lamarin take tana sake tunzura sarauniya mar'atussali, yanzu kam sarauniya ta soma zargin bimbii kan tana son mallake komai na gdn sarautar burham tunda gashi ta haifi yara uku kuma ta mallake zuciyar ubansu,wannan dalilin ne yasa ita ta koma bayan mijinta,babban prince tsoro yake kar maqiya su sake masa yankan baya shiyasa ya rufe idanunsa yyi hkn kuma yasa tsauri sosai a 6angaren bimbii, tsaurin dake 6angaren nata ma babu a nashi 6angaren, ita kanta bimbiin jariran nata na mata qamshin dan goma............

Littafin nan na kudi ne,idan kina da buqatar krtw biya #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,ki tura screenshrt na payment naki ta wannan layin....0704119580

Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

44

*If God destinied no one can say no*...........💕💕
Chapter 50 · 0% Book details