← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 59

Sashe 26

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Prince tunda ta kawo masa wannan abun sha yaga yanayin sai yaji gabansa na fad'uwa bayan fitar yasa ubaid ya bibiyar masa lamarin bimbii duk abunda ya gani baqo tattare da ita ya hanzarta sanar dashi, duk 2tsirgarta akan idanun ubaid take, lkcin daya ga fitowa da dare tana sand'a ta fice yyi saurin bin bayanta inda yaga ta nufa ne yasa ya juya da baya ya koma yaje mugun gudu ya sanar da prince akbar,ko rufe baki be bari yyi ba ya miqe da sauri ya fice ya haye dokinsa ya zabure shi da mugun gudu, ubaid ko tsaye yyi yana kallon prince da mutuqar mamaki yadda yaga ya dauki wannan baiwar tashi da muhimmanci hk,tashi guda kuma tsoro ya cikashi ya soma tunani kar abunda ya faru shekaru dari da talatin da suka gabata ya maimata kansa cikin masarautar burham, suma ji sukayi wurin iyaye da kakanni cewa shekaru dari da talatin da suka gabata lkcin zamanin sarki na biyar cikin wannan masarauta ta burham,d'ansa prince ansar ya ta6a fadawa soyayyar wata baiwa mai suna surayya yar qasar lebanon,tunda hkn ya bayyana sarki ashraf ya zartas da hukuncin kisa ga wannan baiwa batare da digon tausayi ba,baqin cikin mutuwar surayya shine yyi ajalin prince ansar sbd a lkcin ya fada mugun tarko na qaunar wannan baiwa tasa,ajiyar zuciya ubaid yyi yana fatan kar wannan tarihi ya maimata kansa cikin masarautarsu,prince akbar kuwa dayake yana bisa doki ne tuni ya kusa cimmata amma kafin ya qarasa har ta yarjewa kanta kawai ta afka cikin ruwan gwara ta mutu kawai da wannan tsautsariyar rayuwar da take a duniyar da bata da kowa, fad'awarta yyi daidai da qarasowar prince akbar wurin, sakkowa yyi daga dokin nasa ya qarasa bakin kogin da sauri batare da wani jira ba shima ya fad'a cikin ruwan, dayake gwani ne a ruwa da gudu yake suuuu cikin ruwan kogin yana lalibe kozai jiyota, miqa hannunsa kawai yake,gani yyi ruwan na janta sosai dayake ruwan mai tfy ne, tana daf da shigewa wani kwari ta qasan wata gada yyi saurin riqo hannunta ya janyota jikinsa, matseta yyi sosai a jikinsa ya soma suuuu da ita da mugun gudu suka soma tasowa saman ruwan kogin har suka kawo ga6a, daukanta yyi chak ya fito da ita bakin kogin ya kwantar da ita a qasa ya soma danna cikinta da hannunsa ta soma fitar da ruwan data sha, tari ta somayi sosai a hnkli ta soma bud'e idanunta, mamaki ne ya cikata lkcin da tayi tozali da kyakykyawar fuskarsa ya qura mata idanun nan nasa, binsa tayi da kallo kawai,yace" meyesa baki sanyamin guba a abun shan da kk bani ba kafin kizo kice zaki kashe kanki" batace masa uffan ba ta dauke kanta yace" ashe kina sona dayawa hk, kin gwammace ni kibarmin duniyar ke ki kashe kanki,toh idan kin tafi kin barni meye amfanin tawa rayuwar kenan" quresa tayi da idanu ko zata iya fahimta kalmomin dake fitowa daga bakinsa, qoqarin miqewa take ta kasa yasa hannunsa ya miqar da ita, tana zama ta ture hannunsa daga jikinta ya kuma dora hannunsa a cinyarta ta kuma sanya hannunta ta ture hannun nasa,murmushi yyi ya kwanta a wurin dayake rairayi ya janyo cinyar tata ya dora kansa, idanunsa suna sama yana kallon fuskarta, hannunta tasa tana qoqarin tureshi kansa daga saman cinyarta,hannayen nata ya riqe qam cikin nasa, tayi tayi ta kwace ta kasa,ganin hk ne yasa ta dauke kanta gefe guda,murmushi yyi ya miqe zaune ya matso da fuskarsa saitin nata kamar ze goga dogon hancinsa da nata ya fara mata mgn da rad'a yana fada wasu kalmomi da nikaina ban san me yake fada mata ba sbd mgn yake wanda ita kadai take iya jin abunda yake cewa, gani nayi ta kwalalo idanu waje tana kallonsa cike da mamaki, matsar da fuskarsa yyi tare da jan hancinta ya mayar dakansa saman cinyarta ya kwantar tare da folding hannayensa dukka a saman qirjinsa ya rufe idanunsa, kallonsa tayi tace" wani ze iya ganinka hk fa ka tashi" shiru ya mata yyi kamar beji me take fadi ba,saida ta kuma maimatawa ya bude idonsa yana kallon fuskarta yace" idan kina son na tashi ki gyaramin gashin kaina ya hargitse" kallon gashin nasa tayi taga sai digar ruwa yake dayake kuma gashin nasa dogo ne, tace" toh ka tashi zaune saina gyara mk" miqewa yyi zaune yayi folding kafafunsa ita kuma ta miqe tsaye kafin ya ankara ta arce da gudu tana daga masa hannu alamar bye bye, murmushi kawai yyi ya taho a hnkli yahau dokinsa yabi bayanta, hk suka qarasa 6angaren nasu saida ya tabbatar ta shige dakinsu sannan yasa ubaid ganin wurin,shi kuma ya wuce 6angarensa yyi saurin cire wannan kayan, israt da khulood kuwa har sunyi bacci don su da suka ga basu ganta ba sun dauko tana 6angaren prince ne, washegari, tun prince na jiran bimbii har ya hkr taqi zuwa 6angaren nasa ta wuce tabi su israt debo kayan marmari,tasan lkcin wankansa yyi amma ta share ta cigaba da huldar gabanta, shi kuwa prince sanye yake da wata rigar wanka fara sol, ya zauna yana jiran bimbii,lkci ya qure sosai amma bimbii bata zo ba, kwantar dakansa kawai yyi a jikin kujerar dayake zaune ya lumshe idanu, ita kuwa dawowarsu kenan ta kalli 6angaren prince, kamar zata shige abinta sai kuma ta dawo da baya ta wuce ciki, tana isa masu tsaron wurin suka bata hanya ta shige,tana shiga ta duba ko'ina bata ganshi ba tana shirin fice ta hangoshi tsaye wurin windows din nan ya harde hannunsa dukka a bayansa ya qurawa waje idanu tun dawowarsu dasu israt yake hangenta, yanzun ma yaji motsin shigowarta kawai juyowa ne beyi ba, matsawa tayi kusa dashi ta rissinar dakai,juyowa yyi yana kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa sannan ya qetarata ya wuce ya zauna ya dora kafarsa daya kan daya yana kallonta yace" na miki afuwan gocewa aikinki da kkyi yau amma idan kk sake maimata hkn toh zan dauki akan wadanda suke janyeki daga bakin aikin ki" gabanta ne ya fadi don ba qaramin tausayin su khulood takeyi baza ta6a yarda wani abu mara kyau ya same su silarta ba,durqusawa tayi akan guiwowinta gabansa tace" kayi hkr bazan sake ba amma kar ka cutar da yan uwana" kallonta yyi sai kuma ya dauke kanshi gefe guda yace" idan na dauki mataki akansu daman ai shine daidai tunda suke saki rashin jin mgn, sune silar dayasa kk tura kanki cikin rikici har da zuwa sace gawa a kogi" a mutuqar razane ta dago kanta tana kallonshi cike da mamakin yadda akayi babban prince yasan wannan sirrin nasu, harararta yadanyi daidai lkcin kuma ubaid ya shigo, rissinar dakansa yyi ya ajiyewa prince wani dogon akwati a gabansa, kallonta yyi yace" baki san aikinki bane koh kuma saina krt miki" wata irin zabura tayi da sauri ta miqe ta nufi cikin dakin wankan nan ta soma hada masa ruwan wanka cikin kwarmin wanka, shi kuwa prince da gangan ya mata hk yasan tana son su khulood sosai shiyass yake mata wannan barazanar, ita har yau batasan shine dakansa ya cecesu lkcin da suka tafi kogi ganin gawar layla ba,shine dakansa ya dauke hnklin bayin da suke shirin kamasu ya basu damar gudu shiyasa ya rufe fuskarsa da baqin kyalle, gani yyi taurin kan bimbii yyi yawa gata da kafiya kamar shi,dawowa da kallonsa yyi kan ubaid suka soma tattaunawa game da sabuwar takobin da mahaifinsa ya aiko masa dashi, bude masa akwatin ubaid yyi shi kuma ya fito da takobin sai sheqi take da walwali,murmushi yyi sosai sannan ya mayar da ita cikin akwatin,dagawa ubaid hannu yyi shi kuma ya sunkuyar dakanshi qasa sannan ya fice,komar da kallonsa yyi wurin dakin wankan yana jiran fitowarta, fitows tazo gabansa ta rissinar dakanta qasa alamar komai ya kammala, batayi saurin dagowa dakanta ba don tasan tunda bataji motsin miiqewarsa ba toh tabbas ita yake kallo,a zucci tace" haba mutum sai kallon tsiya kamar wani maye" tashi yyi yaxo ya wuceta ya shige dakin wankan, ranar dai kam ta jima tana masa tausa cikin dakin wankan kafin ya kammala wanka ya fito, kwanciya yyi kan gadonsa ya lumshe idanu,tasan sarai tausa yakeso kafin yyi bacci don shi baya iya bacci hk sai an masa dabara, bimbii kam ita yanzu kam tana tsayuwa ne tare da bata da yalwatacciyar tazara tsakaninta da royal bed na prince, tana mugun shakkar hawa gadon nan yanxu, jin taqi hayowa sai abun ya bashi dariya har ya murmusa sbd ya fahimci abunda take tsoro, daga mata hannu yyi tayi saurin sake masa curtains din data rufe kusurwar da gadonsa ke ciki ta wuce ta fice,shi kuma yabita da kallo yasan abunda tafi so kenan shiyasa ya bata umarnin tfy, washegari bimbii tayi masa rakiya wani taro da sarauniiya dakanta ta shirya a 6angarenta na yanta wasu bayi, prince baya taba sake bimbii ta 6acewa ganinsa duk inda tayi yana binta da kallo a sace, sarauniyya mar'atussaliha kuwa uwace wacce tasan halayyar dan nata ciki da waje, ta lura da kallon dayake bin bimbii dashi a sace, kiran bimbii tayi tazo gabanta ta rissinar dakai sannan ta maida dubanta kan kwayar idanun prince dake kallon bimbii nan take ta warware kanta komai tace" bimbii ta tafi, bimbii ta dawo inda take ta tsaya,sarauniyya mar'atussaliha ta kalli prince da murmushi a fuskarta sosai tace" idan na nemi alfarma a wurinka zakamin kai tsaye" kallonta mahaifiyar tasa yyi cike da mamaki yace" umarninki kawai nk jira na aiwatar" fadada murmushinta tayi tace" toh ina son ka bani wannan baiwar taka" saurin dago da idanunsa yyi yana kallonta, murmushi tayi masa sannan tace" kar damu saika maida tsohuwar baiwarka lenah ko ka sake za6en wata cikin bayi na" qaqalo murmushi yyi ya kalleta yace" meyesa kkson wannan baiwar kawai" itama murmushi tayi tace"kallonta kawai nayi naji ta kwantamin daka ganin tana da zuciya mai kyau" shiru yyi ssnnan ya dago dakansa yace" shikenan ranki ya dade na baki ita saidai......." sai kuma yyi shiru tace" kayi magana dana, fadi abunda kkson fada" murmushi yyi yace" aa, babu komai"ranar dai bimbii ta tattara ta koma 6angaren sarauniyya tabar 6angaren babban prince, wannan abu yyiwa mutane da dama dadi ban dasu israt da basu ji dadin hkn ba,itako bimbii abu yyi mata dadi sosai don hkn yafi nono fari a wurinta, wasu bayin har mamaki suke da suka ga bimbii na nuna farin ciki, lenah itama 6angaren abu yyi mata haske ta koma hidimtawa prince akbar, 6angaren prince kuwa abun babu kyau..........
Chapter 26 · 0% Book details