← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 59

Sashe 21

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin nan na siyarwa ne, kan naira #300 kacal, zaki tura ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turo da screesht na payment ta whatsapp ta wannan layi....07041195806....

Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

16

*The more I see you, my heart beat faster than I Imagine*.....so,you are my heart beat....💕

Idanun kowa a wurin yana kanta, lkcin ta soma rero baitocin dake cikin waqenta cikin karyayyen harshenta na diyan fillo dake fitar da luqqa na larabci mai dadin mutuqar dadin sauraro, waqa daya ta dauka cikin waqoqin larabcin da israt ta koya mata har da irin salon rawar waqar, rawan da ciki ake ana karkad'a k'ugu, toh abunku da masu ma'adanan kadawa gaba da baya tuni ta janye hnklin kowa na wurin da salon rawarta, k'ugunta take k'adawa cike da tsantsar k'warewa tana rero baitocinta da muryarta data gama kared'e wurin sbd zaqi, dayawa a wurin sun koma tamkar mutum mutumi sun zuba mata na mujiya, gimbiya hindu ranar ma hk ta din ga cika tana batsewa don ba hk taso ba, ita tunaninta bimbii waqar fillanci zatayi sbd ta toxarta ta a wurin a aibata harshenta tare da kalar fatarta, sai ga bimbii ta bata mamaki tayi waqenta cikin harshen larabci, juyi take sosai skirt din data saka mai batsa ne ta kasa yana hurawa, duk inda ake neman cika na mace toh bimbii ta qetare wurin, tana zuwa qarshen waqar ta sunkuya da qafa daya tare rissinar dakanta qasa ta musu hk da hannuðŸ™wurin ya dauki tafi sosai, shikanshi sarki abdallah murmushi yyi irin nasu na manya, prince akbar kuwa gbdy ransa a dagule yake ji yyi zaman wurin duk ya gundureshi, bimbii koh dawowa tayi bayansa ta tsaya bayan taje ta sauya kayan dake jikinta, prince nasaar shima takaicine ya ishe shi yadda yaga bimbii ta koma bayan prince akbar ta tsaya, wata baiwa ce wacce ke cikin bayin dake rarraba abun sha a wurin ta kawo ruwan inibi ta sunkuya tare da ajiyewa a gaban prince akbar sannan ta dauka ta tsiyaya masa a qaramin cup ta rissinar dakanta qasa tare da miqa masa cup din da hannu biyu, bimbii tayi sauri ta zagayo wurin ta zata amshi cup daga hannun baiwan nan, gani tayi baiwar taqi bata cup din sai miqawa prince take dakanta, kallon baiwar prince akbar yyi yace" ki bata itace keda haqqin bani abu naci" jiki a sanyaye baiwar ta miqawa bimbii cup din dake hannunta bimbii ta dan diga ruwan inibin a farcen dake babban yatsanta, duk suka tsaya suna mata kallon mamaki,yatsan nata ne yyi duhu sosai, juyawa tayi ta miqawa baiwar ruwan inibin data kawo tace" babban prince baya shan ruwa inibi" kallonta prince akbar yyi sannan ya kalli wannan baiwa dake tsaye sai kawai ya miqa mata hannu ta miqo masa cup din data tsiyaya ruwan inibi yakai bakinsa da niyyar sha, bimbii kuwa sai kallonshi take taga tabbas sha zeyi sai tayi saurin sanya hannunta ta amshi cup din daga hannunsa takai bakinta,gimbiya hindu dake kallonsu miqe tayi da sauri cike da tsan tsar mamaki, baiwa ta amshi abu daga hannu prince takai bakinta, hknne ya dauko hnklin mutane, prince akbar kuwa tsayawa yyi kawai yana kallon bimbii data shanye ruwan inibin dake cup din tas, kafin ta sauke cup din, ubaid ya dauketa da wasu kyawawan mari lafiyayyu guda uku,tana matsayin baiwa har ta samu yancin da zata amshi cup a hannun prince takai bakinta, wata irin fizga ubaid yakai mata ya durqusar da ita a qasa bisa guiwowinta, shi kuwa prince bece uffan ba kawai kallon bimbii yake, ita kuwa bimbii abunda yasa tayi hk shine tun tana rawa bisa stage idanunta yakai kan dan sarkin dulham wanda ake kira da prince amir shima ya bayyana a wannan taron, lkcin da baiwar takai masa nasa ta ajiye ta nufo wurin prince da dayan na hannunta ashe ita kanta baiwar bata ankara ba sa'adda prince amir ya musanya mata farantin da jug din da ruwan inibin da zata kaiwa prince akbar yake ya tura mata nashi wanda ta fara ajiyewa, ita kuma bimbii ganin hkn yasa tasan tabbas babu qamshin gsky kan lamarin, diga ruwan inibin da tayi a saman farcenta har yyi duhu shine ya tabbatar mata da akwai guba mai qarfi a cikin wannan abu don tun tana yarinya Allah yyi mata wannan baiwar, idan har akwai abu na cutarwa a abunda zataci idan ta sanya bisa farcenta tana ganewa, idan farcen nata yyi duhu toh abincin da akwai abun cutarwa a cikinsa,wannan dalili ne yasa ta hana prince shan ruwan inibi data ga kuma ya amsa ze sha shine ta amsa ta shanye ita,aikuwa tana wurin a durqushe kan guiwowinta idanunta suka soma gani dishi dishi, tsintsiyar hannunta tashi daya ta soma sauya launi zuwa kalar ja, basu ankara ba sai ganinta sukayi ta zube a wurin, zumbur prince ya miqe daga inda yake zauna ya nufo wurin da bimbii ke kwance ya tsuguna yakai hannunsa ze riqo tsintsiyar hannunta daya ga tayi jajir yana son tantance qarfin gubar dake jikinta, ubaid yyi saurin riqe masa hannu yace" ranka ya dade kar ka ta6a, guba ce mai qarfu zata iya shiga jikinka"sarki abdallah bin jabal kuwa dayake suna da dan tazara tsakaninsa da wurin da ya'yan sarakunan ke jera besan abunda ke faruwa ba saida hadiminsa ya matso kusa dashi ya rada masa abunda ke faruwa, saurin tashi yyi ransa a mutuqar 6ace, baiwar kuwa data kawo wannan ruwan inibi tashi daya jikinta ya soma rawa, ita dai har ga Allah tasan bata zuba komai a ruwan inibin ba toh waye ya mata hk, sarki abdallah bin jabal dakansa ya taso ya iso wurin yana kallon bimbii dake kwance ya kalli hannunta daya suntume tashi daya hkma wurin maqogwaronta, kallon hadimin dake bayansa kawai yyi shi kuma ya sunkuya da hanzari ze dauki bimbii ya fice da ita, prince yyi saurin dakatar dashi shi ya sunkuya da niyyar daukanta, tsawar da mahaifinsa sarki abdallah ya daka masa ne yasa shi janye hannunsa, akan idanunsa wannan hadimi ya sunkuya ya dauki bimbii ya fita da ita, ita kuwa wannan baiwa sarki abdallah ya bada umarnin tfy da ita dakin azabtarwa har saita bayyana wanda ya sanyata aikata wannan gangacin kan magajin masarautar burham, bimbii wani dogon daki aka kaita suna binciken irin gubar don bata magani, 6angaren wurin taro kuwa cigaba sukayi da taronsu batare da nuna kulawa ga abunda ya faru da bimbii ba sbd ita din baiwa ce, sarki abdallah yana da mugun ra'ayin riqau babu wanda ya isa yasa shi janye abunda yyi niyya shiyasa suka cigaba da gudanar da wannan taro tamkar babu abunda ya faru, prince kuwa kasa zama a wurin yyi ya sulale shi da hadiminsa ubaid suka bar wurin taron,suna fita ya kalli ubaid yace" kaje ka bincika inda suka kaita" rissinar dakai ubaid yyi alamar ya amsa umarni sannan yyiwa prince rakiya har 6angarensa sannan ya koma don binciko wurin da akai kai bimbii,prince kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye saikai komo yake da hannayensa a baya yana tunanin halin da bimbii ke ciki, zama yyi a wata kujera ya bude wani akwati ya fito da wata qaramar kwalba ta antidote na irin gubar dake jikin bimbii ya dora saman table din dake gabansa, bimbii kuwa gubar dake jikinta ba'a son ta jima a jikinta idan ta jima a jikin mutum tana illata dukkanin garkuwar jiki ne,sun bata magani amma har yanzu jikin nata beyi respond ga maganin ba, 6angaren prince kuwa ubaid ya kawo masa labaran dukkanin abunda ke faruwa da bimbii, cikin dare ya fice shima ya nufi sashin da bimbii, masu tsaron wurin suna ganin prince suka rissinar dakai tare da bashi hanya ya shige ciki, bimbii ya gani kwance bisa wani dogon gadon katako an lullu6a mata wani mayafi, hannun nata ya kalla da wuyanta yaga wurin ya qara yin jajir, batare daya sanya wata safar hannu ba ya kamo hannun nata yana kallo, kallon bayin dake kula da ita yyi yace su fita su bashi wuri, cikin sauri suka juya suka fice, handkchief dinsa fari sol yasa ya daure mata hannunta sannan ya fito da wannan qaramar kwalba ta antidote na wannan gubar ya bude bakinta ya tsiyaya mata ya jijjigata sosai har antidote din ya wuce zuwa maqogwaronta, qara riqo hannun nata yyi yana kallon wurin yaga ko mgnin zeyi respond har be ga wata alama data nuna jinkinta ya amshi mgnin ba, qura mata idanu yyi cike da sanyin ciki yasa hannunsa ya cire dukkanin awarwaron dake hannunta yasa a aljihunsa, gumi duk ya jiqa masa fuska sai qare mata kallo yake yana dana sanin gardaman daya mata da hkn be afku ba, 6angaren su israt da khulood kuwa sun sami labarin abunda ya faru da bimbii ranar dukkaninsu kasa bacci sukayi, sunyi kuka sunyi kuka har sun gaji, israt ta kalli khulood tace" shikenan mu kuma hk rayuwarmu zata cigaba da kasance kenan ,dubi abunda ya faru da layla yanzu kuma ga wata masifar ta kuma faruwa da bimbii duk a silar bauta" khulood ta kalleta tace" muma idan har muka cigaba da wanzuwa a wannan masarauta wlh qarshenmu bazai kyau ba, gwara mu cire tsoro kawai mu nemarwa kanmu hanyar gudu" kallonta israt tayi tace" abunda ya kamata kenan amma gwara musan halin da bimbii ke ciki tukun" khulood tace" hknne" prince akbar kuwa be bar dakin da bimbii take ba sai gab da asuba, saidai ya gargadi bayin dake tsaron wurin da wadanda suke aikin cikin wurin kar yaji kar ya gani, wato baya son wani ya fahimci a wurin ya kwana tare da bimbii, sukam mamaki ne ya cikasu na ganin duk girma da cikar izza na prince akbar yazo ya kwana tare da baiwarsa sannan ya nuna damuwa sosai kan halin da take ciki amma duk cikinsu babu wanda yasan ya bata antidote din nan, basu kawo komai ba saidai suna ganin yana nuna kulawar ne gareta don nuna halaccinsa ga sadaukarwar da tayi dominsa, sarki abdallah bin jabal kuwa baida masaniyya cewa prince yaje ganin wannan baiwa dakansa, wannan baiwa kuwa data kawo ruwan inibi tana nan ta azabtuwa amma har yanzu bata furta komai game da gubar da suke zargin ta zubawa prince a ruwan inibi............
Chapter 21 · 0% Book details