← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 59

Sashe 5

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

gaban building d'insa yana hangota zaune a gindin bishiyar guiba tana tsefe kalbar dake kanta tana sake kitsa wata,ita kuwa batasan ma ya fito ba tana tsifanta tana rera waqar da take idan ta fita kiwo cikin harshenta na fillanci,juyawa yyi ya koma ciki ya shiga kitchen d'insa ya soma preparing breakfast a cikin kowanne tunaninsa bimbii ce ke fad'o masa ya ayyana mugunta daya dace ya mata,yana gama girkinsa ya zuba a wani plate ya fito wajen inda yake ajiye mata abinci ya juye mata, ita kuwa bimbii daman tun jiya babu abunda taci kuma yanzun ma bakinta babu dandano ko kadan bama ta sha'awar cin komai sai koko da qosai wannan kuwa tasan samunsa wurinta saidai ko a mafarki amma ba'a gaske ba, bata ta6a sanya ran ze zuba mata abinci ganin yadda suka kwashe dashi jiya kawai tana biyowa ta wurin taga ya zuba mata abinci, wucewa tayi bata d'auki abinci ba, shi kuwa duk bayan sakan guda sai ya leqo yaga ko ta dauki abincin daya zuba mata, hk kawai ya samu kansa da son yaga taci abincin amma har dare ya fito yadda ya zuba abinci hk ze gansa, shiru yyi yana tunanin ko fushi tayi sbd abunda ya mata jiya don ya fahimci kamar tana da zucciya, ita kuwa bimbii ta mance ma da batun abinci kawai lalla6a jikinta take don batason ta kuma kwantawa rashin lfy sbd gudun wulaqancin maheer, qunci da tsantsar bauta duk sun sauya bimbii ta koma wata irin miskila bata da fara'a kullum fuskarta a tsuke babu annuri ko kad'an, duk sanda maheer ya fito ze tarar tayi aikinta ta koma gindin bishiya, yauma yana fitowa ya tarar ta gama aikinta, kiranta yyi ta taso tazo juyawa yyi ya shiga cikin building d'insa ita kuwa ta tsaya a inda take don tasan bata da damar shiga wurin, juyowa yyi yaga tana tsaye bata biyoshi ba, saida ya kuma kiranta sannan ta biyo bayansa ta shigo ciki gabanta yana tsananta fad'uwa don batasan me ze mata ba ya kirata cikin wurinsa, parlourn nasa qarami ne amma yana da kyau sosai kuma ya wadatu da kayan more rayuwa, kitchen d'insa babu abunda babu na kayan amfani, kallonta yyi ya soma nuna mata wasu ayyuka da zata din ga masa cikin building din nasa ciki har da girki, itako bimbii binsa kawai take da kallo cike da mamaki toh yaushe ya sauya ra'ayi har ya amince mata ta din ga ta6a abunda zeci har ma da yarje mata ta din ga shigowa bangarensa tana masa 2aikace,tsawan daya mata ne yasa ta dawo cikin hnklinta, saidai itakam bata iya girki irin nasu ba toh me yakeson ta dafa masa ko irin abincinmu na gargajiyar baqar fata, dayake yanzu tana jin larabci sama sama don Allah ya mata kwakwalwa mai kyau da kaifin basirah,cikin harshen nasa ta masa mgn tace"nikam ban iya girki irin naku ba sai irin namu na baqar fata idan kana so kuma sai na mk" harararta yyi ya wuce yabarta a wurin tare da kora mata warning cewa duk aikin daya yanka mata ta tabbatar bata gocewa kowanne ba, washegari tana gama aikin furanni da baiwa kifi abinci ta nufi wurin building nasa, danna masa alarm tayi saida aka dan jima yazo ya bud'e kofar sanye yake cikin kayan bacci da alamu alarm din data danna ne ya tashe shi daga bacci, bece mata komai ba ya matsa gefe ya bata hanya ta shiga, komar da k'ofar yyi ya rufe ya koma bedroom d'insa ya kwanta, ita kuwa ta shiga kitchen d'in nasa ta soma wanke masa kwanuka,gani tayi wasu abubuwan ma dake kitchen din duk sunyi qura, hk ta wanke komai ta fitar da abubuwan da suka lalace a fridge ta gyara komai ta goge floor din yyi tas, tuni wuri yadau haske da annuri, fitowa parlourn tayi ta goge electronics d'in dake parlourn ta kad'e kujeru ta gyarasu sannan ta share ko'ina ta goge, ba tayi gigin girka masa komai ba don itakam bata iya irin girkinsu, har ta gama aikin nata maheer yana baccinsa baida niyyar tashi, bud'e kofa tayi ta fice tunda ta gama aiki nata ta koma gindin bishiyar guiba inda ta saba zama, tunda ta shigo gdn maheer bata ta6a leqa koda k'ofar waje ba kullum tana ciki tana aikatuwa, tana wurin a zaune taga shigowar wata mota qirar mercedez ta shigo farfajiyar gdn, wasu samari ne su wajen biyar dukkaninsu larabawa ne amma suna sanye ne cikin qananan kaya, wurin building maheer suka nufa, shi kuwa tashinsa kenan ya fito parlourn nasa, tsayawa yyi kawai yana bin ko'ina da kallo tamkar ba parlourn nasa ba ganin yadda floor din ke kyalli da d'aukar idanu ga komai a shirye tsaf, shelves na littattafansa a gyare tsaf duk ta kad'e qurar wurin, yana shiga kitchen ya kuma yin turus sbd komai na kitchen tamkar an maidashi sabo hattar oven d'in dake manne da gas d'in girkinsa cikinsa sai sheqi yake, tunda yake masu aikin dake kula da building d'insa be ta6a samun wanda yyi masa wannan aiki mai kyau hk ba, murmushi yyi kawai be damu ba duk da yaga dinning din dake kitchen babu komai wato bata girka masa komai ba amma shi aikin nata kawai ya birgeshi don shi a rayuwarsa yana son tsafta, alarm din dayaji ana danna masa ne yasa ya fito daga kitchen ya nufi wurin k'ofa ya bud'e, friends dinsa ya gani, dariya yyi ya basu hanya suka shigo, duk suka kame akan kujerun dake parlourn shi kuwa ya shiga kitchen ya soma qoqarin had'a musu tea, su kuwa suna parlourn sun kunna waqar Ali bin wasid suna chashewa da ita abinsu,fitowa yyi ya fita, tsayawa yyi a baranda ya kira bimbii dake gindin bishiya, tahowa tayi tazo wurin tana kallonsa, juyawa yyi tabi bayansa, tana shigowa duk suka bita da kallo suna kallon maheer, daya daga cikinsu yace" mah a ina ka samo mai aiki baqar fata kana nufin ita take maka abinci,God forbid" bimbii tana tsaye daga gefensa, murmushi yyi ya kalle friends din nasa yyi yace" oh guys calm down, she is just my cleaner" d'ayan kuwa yana hakimce a kujera tunda suka fara mgn be furta komai ba kawai bin bimbii yake da kallo tun daga sama har qasa,tsayar da idanunsa yyi kan k'ugunta wanda sai mutum ya mugun qura mata idanu ze gano girmansa don doguwar zumbulin rigar dake sanye jikinta ta taimaka wurin asirtashi, sake dire idanunsa yyi kan na shanunta dake tsaye dodar sukam tsinin tsayuwarsu ya fito ta rigar kuma data taka kad'an suke girgixa don ba bra a jikinta, masu yanci suke da arziqin sanya bra,murmushi yyi kawai tare da lumshe idanu ya komar da kansa ya kwantar jikin kujera yasa hannu yana shafa kwantaccen sajen dake gefen fuskarsa,maheer kuwa kallon bimbii yyi yace ta biyoshi kitchen, bin bayansa tayi tana shiga ta tsaya a gefe shi kuma ya soma had'a breafast, duk abunda yake tana kallonsa.......
Chapter 5 · 0% Book details