← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 59

Sashe 45

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screenshrt na payment ta whatsapp a wannan layin..07041195806...

Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

38

*I want to be with you even beyond for ever*......you are my destiny💕💕

Sun isa masarautar burham inda kai tsaye wasu hadimai suka wuce da abram inda akayi masa masauki,prince kuwa wucewa yyi 6angaren mahaifinsa ya same shi yadda dai yabar shi, sarauniyya na zaune gefensa, sarki abdallah yana daga kwance idanunsa na kallon prince akbar, tabbas prince yana cike da tausayin mahaifinsa bisa halin dayake ciki, baya iya mgn har yanzu kawai saidai yana bin komai da idanu tamkar ba sarki abdallah bin jabal ma'abocin cikar izzah da qarfin mulki ba, prince ya labarta masa yadda abubuwa suka kasance tsakaninsa da sarki abu ansar da kuma haduwarsa da abram, batare daya iya cewa komai ba sai kawai murmushi daya bayyana a saman fuskarsa, hkn ya nuna yaji dadin bayanin da prince yyi masa, sarauniya ta kalli prince tace" tashi kaje ka huta don kana buqatar hutu" miqewa yyi ya rissinar dakansa alamar girmamawa sannan ya juya ya fice daga turakar mahaifin nasa, 6angarensa ya wuce ubaid na take masa baya, suna shiga suka tadda bayin dake 6angaren sun jeru sunyi layi don tarbar babban prince, suna ganin shigowarsu duk suka rissinar dakansu har ya shigesu ya wuce 6angarensa, ubaid ne ya dawo ya tsaya a saman corridorn dake 6angaren ya sanar dasu babban prince ya dawo lfy kuma yana kowa fatan alheri sannan ya umarcesu kowa ya koma bakin aikinsa,yana zaune sanye da wata farar riga ta shiga wanka lenah ta shigo, sanye take da wata doguwar jar riga, hannunta yasha tsiraran awarwaro ya cika mata hannu,bisa al'adarta qafarta daure da sarqar qafa, qarasowa tayi inda yake ta tsaye tare da rissinar dakanta qasa alamar girmamawa sannan ta dago dakanta ta wuce da sauri ta shige dakin wanka ta hada masa ruwan wanka mai dumi a cikin kwarmin wanka tasa sinadaran wanka sannan ta fito ta sake rissinar dakanta qasa tayi gefe ta tsaya, wuce ta yyi ya shige dakin wankan, washegari, tun safe abram da prince suka bayyana a turakar sarki abdallah bin jabal, abram kallon sarki abdallah kawai yyi yaga yanayin yadda jikin nasa yyi, dago idanu yyi ya kalli sarauniya mar'atussaliha dake tsaye gefe yace" ina buqatar ku bani lkcin nan da kwana uku nayi bincike akan gubar" tace" an baka amma ka tabbata kayi bincike maikyau don mu nan bamu son kuskure" sunkuyar dakansa yyi alamar girmamawa ga wannan sarauniya sannan ya fita, sarauniya ta kalli babban prince tace" kana ganin akwai alamun nasara tattare da wannan bayahude, kasan fa mutane abun tsoro ne bani yarda da kowa ya duba mahaifinka sai cikakken amitacce sbd muna da maqiya dayawa masu neman ganin bayan wannan masarauta" murmushi babban prince yyi yace" ranka ya dade wannan bayahude baida wani niyya mara kyau ki duba kwayar idanunsa zaki tabbatar da hkn" murmushi tayi ta shafa kansa cike da qauna tace" madallah da wannan jarumin d'a nawa mai tsananin kaifin basira tabbas ina alfahari dakai" murmushi shima yyi ya miqe tare da rissinar dakansa ya fice, komawa yyi 6angarensa yana son ziyartar qasarban don duba lfyr bimbii da gudan jininsa saidai yana shakkar hkn don ko qaqa baya son wani ya gano bimbii na raye har ta haife cikin dake jikinta sbd tsaro, ubaid ya buqaci gani ya shigo da sauri ya iso wurinsa tare da rissinar dakansa qasa yana sauraron umarni,kallonsa babban prince yyi yace" meye tunaninka da ziyarar da nkson kaiwa qasarban" shiru ubaid yyi yana tunani sannan ya dago dakansa yace" yakai ma'abocin hikima tabbas har yanzu duk wani motsinmu akan idanun masarauta yake kuma ko yaya ka fita ziyartar wani wuri a yanzu zasu iya tunanin wani abu wanda hkn zesa su sanya masu binciken sirri su soma gudanar da bincike" jinjina kai yyi alamar gamsuwa, ubaid yace" duk wani kulawa tana samu ita da gudan jinin burham dake tare da ita, kuma nasa cikakken tsaro daya dace" kallonsa prince yyi yace" madallah da wannan amintaccen hadimi" rissinar dakai ubaid yyi saida prince ya daga masa hannu ya ja da baya sannan ya juya ya fice, jinginar dakansa yyi a kujerar dayake zaune yana tunanin qalubalen dazai fuskanta zuwa gaba kan wannan batu don masarautar burham na da tsauri sosai bisa jagoranci mahaifinsa sarki abdallah bin jabal, yana daga cikin tsaurin wannan masarauta basu amfani da maganin bature komai a gargajiyance suke yinsa suna kan al'adun iyaye da kakanni wato larabawan farko, bimbii tana qarqashin kulawar sumayya tana bata cikakken kulawar data dace, gudan jinin burham kuwa yana cike da kuzari sam be dauko bimbii a komai ba yyi gadon larabawa ne, yau suna kwance cikin dare yaro ya soma kuka sosai yaqi yin shiru, daukansa bimbii tayi tana ta jijjigashi ko zeyi shiru amma yaqi yin shiru kuma yaqi karbar nono yasha, kukan shi sumayya taji tayi hanzarin shigowa dakin a rikice tana tmbyr bimbii abunda ya same shi, bimbii tace" nima gani nayi ya fara kuka yaqi yin shiru" hannu tasa ta amshi jaririn tana kallonshi, jikinsa taji yyi zafi alamun sun nuna zazzafi ne a jikinsa, ruwan dumi ta hada ta sanya shi ciki sannan ta bashi mgnin zazzafi, saida ta jima dashi cikin ruwan dumi sannan ta fito dashi ta goge shi ta sanya masa kaya masu taushi,hkn data masa yasa ya tsagaita da kukan har bacci yyi gaba dashi, washegari, kwana ukun da abram ya diba ya cika, sai yamma abram ya iso akayi masa iso ga sarauniya ita kuma ta wuce dashi turakar da sarki abdallah ke kwance, anan suka tarar da babban prince yana tare da mahaifinsa suna sauraron qarasowar abram, batare da 6ata lkci ba abram ya fito da wasu tsinkaye masu kaifin gske ya ajiye gefe, tare da wani farin ruwa, dago dakan sarki abdallah yyi ya bashi wannan ruwan dake cikin wani gora yasha sosai sannan ya sanya wannan tsinken daya a bakinsa ya fito masa da wani abu kamar dan wuya ya ajiye a cikin wani qoqo hk ya cigaba dayi har ya gama, wata qaramar kwalbar ya fito da ita da wani ruwan magani a ciki ya sake bashi yasha sannan ya goga masa wani mai mai kyalli a dukka sasssan jikinsa, prince da sarauniya kuwa suna daga gefe suna kallon abunda wannan bayahude yake, miqewa yyi ya kalli sarauniya tare da rissinar dakansa qasa yace" ranki ya dade na gama sai mu saurara mu ga yadda jikin nasa ze amshi mgnin, gubar dake jikinsa baquwar guba ce wacce ta fito daga nahiya mai nisa wato nahiyar baqar fata, nayi nasarar gano antidote dinta ne sbd na ta6a krt yanayin wannan guba, idan har jikin nasa yyi maraba da wannan antidote toh daga gobe alamar hkn ze soma bayyana" murmushi sarauniya tayi tace" idan har nasara ta tabbata lfyrsa ta dawo kana da kyakykyawar kyauta ta musamman idan kuma muka ga akasin nasarar tabbas fushi na ze tabbata akan ka" murmushi abram yyi ya sake rissinar dakai sannan yaja da baya ya fice,dukkanin wanda ke wannan masarauta kawai tsumaye yake yaji ya lfyr sarki abdallah bin jabal har tsawon kwana daya da yini jikin sarki abdallah be nuna wata alamar na sauyi ba, cikin izinin ubangiji a washegari sai gashi ya soma miqewa zaune dakansa, wannan cigaban da aka samu a lfyr sarki ba qaramin farin ciki yasanya sarauniyya ba, saidai sarki abdallah da batun auren babban prince da gimbiya qifdiya ya bude baki,hkn yasa prince yyi shiru, cikin kwanaki uku jikin sarki abdallah ya warware ya dawo yadda yake tun farko, sarki abdallah bin jabal yyi farin ciki da wannan lfy daya samu tuni yasa aka kira masa wannan bayahude wato abram har fadarsa, abram na shiga wannan fada ta sarki abdallah bin jabal da aka ginata da danyen gwal ya zube gaban sarki yyi gaisuwa, murmushi sarki abdallah yyi yace" yakai wannan masani ma'abocin kimiyya da tarin sani tabbas nayi farin ciki da wannan ingantaccen magani nk don hk ka fadamin buqatarka gareni kowacce iri ce nayi maka alqawarin cika maka ita batare da wani 6ata lkci ba,zan faranta ranka kamar yadda ka faranta min" fadar sarki abdallah tayi shiru kowa na sauraron jawabin dake fita daga bakin sarki kuma suna sauraron suji buqatar wannan bayahude ga sarki abdallah, prince na tsaye gefen mahaifinsa shima yana sauraro, abram dago dakansa yyi ya kalli sarki abdallah sosai yace" yakai wannan sarki ma'abocin qarfin mulki da magana daya ina da buqata mai qarfi a gareka duk da ina da cikakken sani kan halayyarka ta cika alqawari da tsayawa kan mgn daya amma duk da hkn ina da shakka bansan ko zaka iya cikamin wannan buqata tawa ba don tana da qarfi" wannan zance na abram ya sanyawa kowa tunani shin wanne bayahude kuwa wacce buqata ce dashi hk dayake wannan batu, jikin sarki abdallah yyi sanyi da jin wannan batu na abram don shi tunaninsa wannan bayahude buqatarsa bata wuce dukiya, shi kuwa dukiya kowacce iri yakeso ze iya mallaka mishi batare da yasan yyi wani abu ba don yana da qarfin arziqi, prince shima a nashi 6angare mamakin abram yake yana tmbyr kansa shin wanne bayahude wacce buqata yake da ita a wannan masarauta tasu da har yake fadin tana da qarfi, kallonsa sarki abdallah yyi yace" ka fadi buqatar taka naji kai tsaye" shiru abram yyi yana shakkar fadin wannan buqata tashi kar wannan sarki yasa a masa kisan gilla, daka masa tsawa uxair yyi yace" yakai wannan bayahude ba'a yiwa sarki shiru ka hanxarta fadar buqatarka don sarkinmu ma'abocin alqawari ne da mgn daya kowa ya shaida" ajiyar zuciya abram yyi ya numfasa sosai sannan ya dago dakansa ya kalli sarki abdallah bin jabal dake hakimce a wata kujera ta alfarma mai ruwan zinare yasha alkyabba baqa da rawani mai baqi da fari, duk da sarki abdallah ya cika masa idanu amma hkn ya bude yace" yakai wannan sarki buqatar da nk nema gare ka itace ka yarje auren prince akbar da tsohuwar baiwarsa daka yankewa hukunci kisa sannan kayi aikin gafara a garesu tare da sanya musu albarka su da gudan jininka da yanzu hk wannan baiwa ta zama silar zuwansa duniya".....fadar yanayin rudani da daya bayyana a fuskokin al'ummar dake wannan fada yafi gaban kwatance, prince akbar kuwa mutuwar tsaye yyi, sarki abdallah bin jabal kuwa qurawa abram idanu yyi da fuskarsa da babu alamun annuri, jin zciyarsa yake kamar zata tsago ta fito sbd tsananin 6acin rai, fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta, prince gabansa mugun faduwa yake duk da tarin jarumtarsa yana masifar shakkar mahaifinsa, wannan yanayi da abram ya gani ne yasa tsoro da tarin rudani hade da firgici ya bayyana a fuskarsa,jikinsa rawa ya somayi sosai, miqewa sarki abdallah yyi yayi ya soma takawa a hnkli masu tsarinsa suka take masa baya yabar cikin wannan fada batare daya furta komai ba,sarkin hukunci yaba dakarun dake fadar umarni su kama abram su wuce dashi dakin horo don koyar dashi darasin harshe.......
Chapter 45 · 0% Book details