Sashe 16
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
faru lkcin ni kuma wata baqin ciki na zai soma" gbdy kalaman bimbii sun basu mamaki kawai kallonta suke cike da al'ajabi amma sai sukayi shiru, khulood ta kalli israt tace" ki tashi mu koma 6angarenmu kafin ummul shukri ta fahimci ba anan muka kwana ba" saurin miqewa sukayi bimbii ta rakasu har kofar shiga 6angaren nasu sannan ta dawo, baiwar gimbiya hindu zulham kuwa daman a 6angaren ta kwana don daukar rahoto aikuwa tun fitowar bimbii cikin dare daga 6angaren prince akan idanunta har fitowar da sukayi yanzu,murmushi tayi kawai wuce sum sum don isar da saqonnin ga gimbiya hindu, gari na wayewa kuwa bayi suka soma rige rigen fitowa bakin qorama suna jiran ganin bimbii ta fito wankin budurci, ita kuwa bimbii da wannan safiya ta shiga kitchen din da ake shiryawa prince abinci, bayin dake aiki a kitchen duk suka bita da kallon raini don haushinta sukeji, gaishe tayi fuskarta a sake amma cikinsu babu wacce ta amsa sai aikinsu suke, itama bata kuma tanka musu ba ta wuce cikin kitchen ta hada ruwan inibi ta sanya zuma ta dauko wani jug tamkar na zinare ta zuba ciki ta sanya qananan kofuna, duk suna kallon abunda take, bushewa sukayi da dariya, dayan da ake kira zulja ta kalli bimbii tace" yadda kk da duhun fata hk tunaninki yake mai kk dauki babban prince da zaki hada masa wannan shirmen ki kai masa hala baki iya girki bane" bimbii batace musu komai ba ta dauki faratin da jug da kofunan yake ta fice ta nufi 6angaren prince akbar, bata ganshi a ciki ba don hk ta qara gyara komai na 6angaren ta kuma sanya qamshi ta ko'ina ta gyara gadon nasa ta goge ko'ina don ummu sumayya ta fada mata aikin babbar baiwa mai hidima ga prince tana shirin fita ya shigo tare da hadiminsa ubaid, sunkuya tayi ta rissinar dakanta alamar gaisuwa, batare daya kalleta ba ya zauna abinshi ubaid na tsaye a bayansa, tana nan kan guiwowinta bata miqe shi kuwa yama mance da ita a wurin yana nunawa ubaid wasu maps, daga qarshe ya bawa ubaid maps din da batasan ko na meye ya fice dashi, sai lkcin ya kalli 6angaren da take durqushe ya kalli kuma abunda ta ajiye masa, itama sai lkcin ta tuna aikinta ta miqe da hanzari ta qarasa wurin nashi ta soma tsiyaya masa ruwan inibin a kofi, kallon ya kumayi ya kalli abunda take zuba masa yace" meye wannan?" ya nuna mata ruwan inibin da take tsiyaya masa cike da girmamawa ta sanar dashi ruwan inibi ne, yace" abunda kk iya kenan da safe" bata gane nufinsa ba tace" yana qara lfyr zuciya da faranta safiya ranka ya dade" shiru yyi be kuma mgn ba ta miqa masa ruwan inibin ya sanya hannu ya amsa ya ajiye a saman farantin, nuna mata yyi ta dauka ta fita dashi, shiru tayi kamar zatayi kuma hk ta dauka ta fita dashi ta koma kitchen, bayin dake kitchen din kuwa dariya suka soma mata har da tafa hannu,zulja tace" yanzu dai kinsan waye prince koh" fita tayi daga kitchen din don batasan me zata girka masa ba idan dai ba irin cimmarta ta rugarsu,idan kuwa tayi wannan ganganci tasan ba abune mai dadi ze biyo baya ba,kafin komai zancen rashin fitowarta wankin budurci ya karade ko'ina, wannan abu yasa sunan bimbii ya kuma fitowa cikin bayi kowa yasanta, dayawa abu yyi musu dadi musamman nasaar da shima ya sanya yar leqen asiri kuma ta kawo masa kyakykyawan labari daya sanya shi farin ciki,itama gimbiya hindu tayi dariya sosai ranta qal don hk prince akbar yake birgeta, sarauniya kuwa murmushi kawai tayi don tafi kowa sanin halin danta,ita kuwa bimbii sai yanzu take fahimtar yadda suka dauki za6en nata bada wasa ba sbd rashin qaunarsu ga baqar fata.......