← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 59

Sashe 41

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*My heart is bursting,my heart is beating more and more*......the time I set eyes on you I was totally confused💕💕

A hnkli take masa tausan tamkar tana tausayin jikinsa, yanayin yadda take masa tausan yasa shi lumshe idanunsa yana tuna wacce take masa irin wannan tausan wato bimbii, ji yake tamkar itace ke masa tausan sbd exactly yadda take masa hk wannan baiwar take masa, so yake ya dago da kansa yaga wannan baiwa saidai izzah irin tasu ta jinin sarauta na yawo a jikinsa, daga mata hannu yyi alamar tausan ya isa hk, gabansa ta dawo ta tsaya tare da rissinar dakanta qasa sannan ta dago dakanta ta dauki tuffa daga cikin qaramin kwandon data shiga dashi na kayan marmari ta sanya wata kyakykyawar qaramar wuqa ta yanka tuffan ta sake rissinar dakanta tana miqa masa slice na tuffan,shi kuwa babbar prince yana tozali da fuskarta numfashinsa ya dauke na wasu sakanni kafin ya dawo hnklinsa, zuciyarsa bugawa ta somayi da qarfi tamkar zata fasa kirjinsa ta fito ya qureta da idanu ko qiftawa baya yi cike da tsantsar mamaki, ita kuwa bimbii kanta na sunkuye tana riqe da tuffan da take miqa masa jin shirun yyi yawa ne yasa ta dago dakanta tana kallonshi, kallon daya qureta dashi ne yasa taji gabanta ya fadi, miqewa yyi a hnkli yasa hannunsa ya dago da ha6arta yana kallon cikin qwayar idonta cike da tarin rudani, gani yake tamkar gixo take masa ko kuma mafarki yake, ita kuwa bimbii rawa jikinta ya soma tamkar mazari sbd daman taji tattaunawar shugaba suwaiba da hamshaqiya ramlatu kan zuwanta tarar wannan dan sarki matsayinta na mai yaron ciki sai take gani kamar ganin cikin dake jikinta ne yasa wannan dan sarki yi mata hk, sauke hannunsa yyi yana cigaba da kallonta, gani yyi a tsorace take dashi hkn ya nuna tamkar bata gane shi bane,gabansa ne yaji ya yanke ya fadi, maida kallonsa yyi kan qaramin cikinta daya turo sosai ya jima yana kallon cikin sannab ya dago da jajayen idanunsa da tashi daya suka sauya launi, idanunsa ne suka sake bata tsoro tayi saurin ja da baya, a hnkli ya soma takawa har ya isa inda take tsaye ya matsa jikinta sosai tamkar ze hade jikinsu, ita kuwa bimbii ji take tamkar ta saki fitsari a wando sbd tsabar tsorata da tayi dashi, cikin wata irin murya mai cike da rudani yace" me kk nufi? baki gane ni ba?" mgn ta soma cike da qinqina tamkar me koyon mgn tace" ni...baiwa..c..e, shu..ga..ba ce ta turon gareka" be kuma furta komai ba saida kallonta dayake tun daga sama har qasa, ja yyi da baya ya koma kujerar dayake ya zauna ya kwantar dakansa jikin kujerar ya rufe idanunsa sbd dokawa da zuciyarshi take 2akai,ita kuma tayi saurin qarasowa gabansa ta durqushe qasa bisa guiwowinta, batare daya bude idanunsa ya kalleta ba yace" me sunanki?" cikin sauri ta amsa masa tace" suna na andal" bude idanunsa yyi ya kalleta sosai sai kuma ya rufe saida ya jima sannan ya sake mgn yace" waye da cikin jikinki?" cikin tsantsar rudu ta dago da fuskarta tana kallonshi taga idanunsa na rufe sai ta sunkuya ta kalli cikin dake tare da ita, cikin sanyin murya tace" nima ban sani ba kawai ganin cikin nayi a jikina" cikin sauri ya bude idanunsa yana kallonta yace" me kkce?" shiru tayi bata sake mgn ba don yanayin yadda yyi yasa taji tsoron sake maimaita abunda ta fada, tashi yyi zaune sosai ya zuba mata idanu sai kuma ya miqe abinsa ya qarasa hadadden gadon dake can gefe ya kwanta sannan ya dago ya kalleta yaga tana inda yabarta bata da niyyar tashi yace" hk shugabar ta koyar dake aikinki" saurin tashi tayi ta qaraso wurin gadon ta tsaya batare data hau kan gadon ba, murmushin yaqe yyi wanda a zahiri ji yake tamkar ya rushe da kuka, ga zuciyarsa ta gaza dena bugawa da qarfi kawai dauriyya yake yace" ina buqatar ki sanya ni bacci" shiru tayi sai kuma ta hau gadon cikin sanyin jiki yana ganin tahau yyi matashi da cinyarta ji yake tamkar ya rumgumeta a jikinsa ko bugawar da zuciyarsa keyi ze ragu, saidai kawai ya daure, ita kuwa sakoko tayi tana kallon gashi kansa,ba zato taji.muryarsa yace" idan ina jin bacci sai an bani labarai masu dadi nk bacci,ki bani labarinki sai nayi bacci sbd kin min kama da wata wacce na sani" kallonshi take da mamaki sai kuma ta kalli gyararren sumar kansa dake kwance a saman kafadarsa, ji tayi gbdy ya birgeta, cikin sanyin murya ta soma bashi lbrinta iyakar wanda ta sani har da lbrin gidansu farhan da zaman a gdn maheer har kawo wannan lkci, kwance yake a saman cinyarta idanunsa a sama yana kallonta ya harde hannayensa saman qirjinsa ya qura mata idanu a hnkli yace" kuma baki da buqatar sanin me wannan cikin na jikinki" yasa hannu saman cikin nata yana dannawa a hnkli, shiru tayi sai kuma tace" in Allah yaso wataran zan tuna lbr na" murmushi yyi yace" kiyi qoqarin tunawa sbd qila mai cikin yana jiran abinshi" shiru tayi tana mamakin wannan dan sarki daya sake yake mgn da ita hk kuma ya bada interest nasa yana sauraren lbrinta, cikinsu babu wanda ya sake mgn, shi babban prince duk cikin lbrin data bashi babu wanda ya 6ata masa rai yaji bala'in kishinsa irin maheer, be sanshi ba amma yaji tsanarsa sosai cikin ranshi, lumshe idanusa yyi yana jinsa tamkar wani sabon mutum yau gashi ga rayuwarsa suna numfashi a muhalli guda abu kamar cikin mafarki, ita kuwa bimbii hannunta na cikin sumar kansa tana son sanyashi bacci, tunda ya rufe idanunsa be kuma budewa ba, idanun nasa na rufe ya daga mata hannu alamar ta tafi, ji tayi sam batasan sauka sbd qamshin dake fita daga jikinsa yana mata dadi sosai amma dole ta sauka ta nufi hanyar fita, tana fita yyi saurin tashi zaune yana kallon hanyar data bi, zumbur yyi ya miqe ya soma zirya, bimbii kuwa tana fita ubaid ya bita da kallo,saidai be samu nasarar ganin fuskarta ba amma ya hangi cikin dake jikinta, hknne ya bashi tabbaci dalilin dayasa babban prince ya koreta kenan, wani hadimi ne ya sanar dashi prince na son ganinshi ya shiga da sauri,batare da bata lkci ba prince ya bashi umarnin abunda ze aikata.....

**

6angaren maheer kuwa hauka tuburan ya gwada musu lkcin daya dawo gida ya tarar ba bimbii ba alamunta cikin gdn, a guje ya fito tamkar mahaukaci yahau motarsa yyi gdn ennah, tana zaune tana krt wata jarida taji shigowarsa ya afko ciki kamar an jefo shi kallonta yyi yace" ina kk kaita ina kk kaimin ita?" kallonshi tayi cike da rashin fahimta tace" me kk fada" kallonta yyi a tsorace yace" ban ganta ba ina kk kaita nasa kece kk dauke min ita" miqewa tayi tana kallonsa tace" au taji gargadin da na mata kenan ta nemi hanyarta hkn yyi kyau" kallonta ya tsaya yi yace" ina take?" tace" wannan kai zan tmby" kallonshi tayi kawai sai taga yana hawaye yace" do you want me to live?" kallonshi ta tsaya tanayi cike da mamaki don batayi zaton abun nashi yyi tsananin hk ba tace" what do you mean maheer" wani murmushi yyi ya kuma kallonta batare data ankara ba yyi saurin daukar qaramar wuqar yanka lemo dake gefenta ya soma ja da baya yace" I told you my life is useless without her, do you know how much I suffered when I lost her? a rikice take kallon wuqar dake hannunsa tace" no, maheer dnt do this u are a muslim" murmushi yyi be sake cewa komai ba ya chaka wuqar a qirjinsa, wani irin ihu ta kurma a guje tayi kansa tana kiran sunan shi, shi kuwa sulalewa yyi qasa cikin jini...........

pls manage it pls....

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir, union bank saiki turo da screenshrt na payment naki a whatsapp ta wannan layi...07041195806....

Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

35

*To me you are the princess*........you are my queen,you build a perfect kingdom in my heart.....so, you are the star💕💕
Chapter 41 · 0% Book details