← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 59

Sashe 6

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Littafin nan na siyarwa ne ki siya kiyi karatunki cikin yanci,idan kin shirya siye saiki tura naira#300 ta wannan acct no.0100790419,Alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screenshrt na payment dinki ta whatsapp 07041195806, idan kina buqatar wani bayanin kuma saiki kira wannan layin 08080611486

Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

4

Bayan ya gama komai akan idonta yace ta tafi, fitowa tayi daga kitchen d'in ta fito parlourn da niyyar fita, daya daga cikin friends nasa dake parlourn mai suna farid yasa hannu ya damqo hannunta yana murmushin qetai, qoqarin fixgewa take ta kasa maheer ya fito da cups na green tea a hannunsa, tsayawa yyi yana kallon farid da mamaki yace" ta maka wani abun ne koh" yace" No, but u said she is ur cleaner so i want her to clean my body" gbdy sauran abokan nasa suka bushe da dariya, shi kuwa farid murmushi kawai yyi, wani cikinsu mai suna jalil ya kalli farid yace" clean ur body as how,just make it clear" dariya yyi ya miqe ya soma 6alle ma6allan rigarsa ya cireta daga jikinsa ya kalli maheer yace" kace mata ina son tayimin wanka" maheer jin abun yyi wani banbarakwai ya kalleshi yace"wanka?" yace"yes,ko ba baiwa bace?" murmushi maheer yyi ya kalli 6angaren da bimbii ke tsaye don farid yyi blocking hanyar fitar, duk sauran abokan nasa suna daga zaune suna jiran maheer ya bawa bimbii umarnin yiwa farid wanka, shi kuma gashi baya son abokan nasa suyi zaton ko yana siding din bimbii ne don hk ya kalleta fuska a tamke yace" kije ki yiwa abokina wanka" kwalalo idanu waje tayi ta soma ja da baya tace" wanka zan yiwa wannan qatoton billah ban iya yiwa babba wanka ba" mgnr duk tana yine cikin harshenta na fillanci don bata gama kwarewa da larabcin ba, basu jin yaren nata amma yanayin yadda tayi ya tabbatar musu da gardama take baza tayi masa wankan ba, miqewa maheer yyi ya nufo inda take yace" yauma gardama zakiyimin" su kuwa sauran duk suna daga zaune suna dariyar qeta tare da qara zuga maheer wai lalle yyi sake baiwarsa bata bin umarninsa, kafin su ankara bimbii ta bud'e k'ofa ta fice da gudu, binta yyi da niyyar sakar mata kare ita kuwa Allah ya bata sa'a ta fice daga gdn gbdy, yana ganinta ta fita ya bita da gudu, ita kuwa tana fita ta miqe hanya tana ta gudu don wlh tsoro taji sosai gani take idan ta tsaya zasu iya keta mata rigar mutunci tunda har abun yakai ga hk, shi kuwa maheer gani yyi har ta masa nisa, komawa yyi gd ya kira masu tsaron hanyar data nufa kansu dakatar da ita baiwa ce take neman gudu, su kuwa sukace mata basu ganta ba, rikicewa yyi sosai lkcin da suka sanar dashi basu ganta ba, fita yyi da kansa yana ta zagayen neman bimbii amma ko mai kama da ita be gani ba, ita kuwa bimbii ba sanin gari tayi ba,tana cikin gudun tayi wata hanya data nufi outcast wato wajen gari,tsayawa tayi tana kalle kalle taga tabbas wurin da take wajen gari ne don ba mutane sosai, tana cikin waige waige ta jiyo qarar takun dawakai tana juyawa taga wasu mahaya dokuna ne su shida suna gwada tseren sukuwa sun nufo inda take gadan gadan tamkar basu ganin komai a gabansu, mugun firgita tayi ta soma qoqarin juyawa da gudu aikuwa tuni sun cimma inda take kafin kace kwabo daya daga cikinsu ya gwabjeta da gefen dokinsa, duk sukayi wucewarsu batare da sun tsaya ganin halin da take ciki ba don faduwa tayi a wurin, daga bayansu ashe akwai wasu dakarun mahaya dawakan dake take musu baya, shugaban wannan dakarun ne ya tsaya ya bada umarni a dauki bimbii dake kwance tamkar bata numfashi,su kuwa wadannan shidan da suka soma wucewa ya'yan sarakuna ne dake taqama da izzar jinin sarauta don kowannesu ya fito ne daga sananniyar masarauta me fada aji cikin daular larabawa, wannan wuri kuma filin tseren sukuwar dokunansu ne da suke fitowa duk qarshen mako don nishad'intar da kansu, hadimansu kuma na take musu baya tare da al'qalan dake fitar da gwanin daya cinye tseren cikinsu, suna isa madakata suka ja tunkan dawakansu suka tsaya, PRINCE AKBAR....shine ya samu nasarar cinye wasan tseren sukuwar dokin, sakkowa yyi da fuskarsa da babu yabo babu fallasa daga kan dokinsa, hadiminsa na hannun damansa ubaid ya kama masa dokinsa, sanye yake da wasu fararen kaya tamkar pakistan kansa sanye da rawani baki da fari, fari ne sol kallo daya zaka masa kasan cikakken balarabe, sajen daya zagaye fuskarsa baki ne ya taimaka wurin tona asirin kyan d'an sarkin,yanayin tafiyarsa da kallonsa kawai zai haska cikakkakiyar izzarsa, haqoransa a jere suke farare tas dasu duk wata halitta dake jikinsa fara ce idan ka cire gashin dake jikinsa da kuma kansa,gashin kansa dogo ne tamkar na mata har rawa yake idan ba rawani akansa,PRINCE AKBAR shi ya buge bimbii ta bashi haushi sosai daya ganta a hanyar sukuwar tseransu, ubaid ne ya matso kusa dashi yace" Your highness wannan alamunta ya nuna baiwa ce dake neman gudu" kallo d'aya yyiwa keken dokin da suka dauko bimbii yace" ku kaita cikin yan'uwanta bayi" abunda yace kenan ya wuce abinsa ya sake hawa dokinsa suka dau hanyar komawa gdn sarautar burham dake tsakiyar babban birnin kuwait........

*Masarautar Burham*🔱🔱

Ginin gdn sarautar burham shi kansa abun kallo ne don gini ne da kwararrun magina suka tsarashi cike da basira, gdn gari guda ne dauke da 6angarori daban daban tare da lambuka na shaqatawa da qoramai wanda ruwansu ke kwaranya, masarautar burham tsohuwar masarauta ce a qasar kuwait mai kafaffen tarihi, akwai arziki da tarin izzah ga jinin sarautar burham, sarki abdallah bin jabal shine mahaifi ga PRINCE AKBAR kuma shine riqe da sarautar wannan daular masarautar burham, sarki abdallah bin jabar mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi irinna larabawan farko ga taurin kan bala'i shiyasa har yau suke kan tsoffi al'adunsu a wannan masarauta, suna da tarin bayi da hadimai,rukunin bayin dake wannan gdn sarauta ya kasu kashi uku kuma dukkaninsu da alamominsu, bayin farko sune na qasa qasa masu kula da share share da gyare gyare da yiwa dawakai wanka, sai na biyu masu kula da bangarorin iyalan wannan gd, kaso na uku kuma sune masu kula da lfy da kuma abincin iyalan wannan gd tare da tsaftace komai nasu, prince akbar shine daya d'a ga sarki abdallah bin jabal sai kuma ya'yan wasu sarakunan dake qasan masarautarsu da suka taso cikin wannan gdn sarauta kuma kowanne cikinsu da 6angarensa da hadimansa tare da gayyar bayi, 6angaren prince akbar yafi kowanne 6angare girma da fad'i, akwai bayi na musamman dake hidimtawa 6angaren nasa sai hadiminsa na hannun damansa ubaid, ubaid yafi kowa sanin halin prince akbar kuma yana mutuqar masa biyayya baya sa6awa umarninsa, gdn sarautar burham sun dau bayi tamkar ba rayuka ba don laifi qanqani bawa ze aikata sarki abdallah ya zartar da hukuncin kisa akansa shiyasa bayin gdn kowa yake taka tsantsan da kaffa kaffa, idan har baka daya daga cikin bayin dake hidimtawa 6angaren sarki ko sarauniyya ko ya'yan sarki to kuwa baka isa ka shiga 6angarensu ba, kowanne rukuni na bayi akwai wanda ke shugabantarsu, idan aka kawo sabbin bayi akwai wacce ke nuna musu ayyukansu suna kiranta ummul shukri, bata da wasa ko kadan gashi ta iya horar da bayi yadda ya kamata a hannunta ubaid ya damqa bimbii,akwai doka sosai a wannan gdn sarauta, kafin a za6i bayi su hidimtawa sarauniyya ko sarki ko ya'yan sarki sai an tabbar da asalin bayin da kuma himmarsu, bayi marasa asali yawancinsu basu aiki a bangaren iyalan gdn suna aiki ne kawai a cikin gdn sarautar,fadar sarki abdallah bin jabal an ginata ne da danyen gwal kowacce kusurwa a fadar daukar ido yake, tsarin wannan gd shine bawa ya tsaya iyakar matsayinsa idan kuwa ya nemi ya qetare kai tsaye hukunci mai tsauri ze hau kansa, kafin su dauki bawa ya soma aiki a wannan masarauta sai ummul shukri ta gwadasu ta kowacce siga shiyasa suke kiranta uwar bayi.........
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

5

*Love is the unsoluble equation to a great mathematician and also a heavy weapon to hold for a great legends and heroes*......🔱🔱
Chapter 6 · 0% Book details