← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 59

Sashe 4

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta gama nome busassun ciyayin dake farfajiyar gdn sannan sauyawa kifin dayake kiwo ruwa ta basu abinci sai gumi take ga yunwa dake neman kayar da ita, wannan rumfar gezevo din daya nuna mata a matsayin wurin kwananta ta nufa ta zauna tana ajiyar numfashi, gyangyadi ne ya soma daukarta ta batare data ankara ba taji saukar ruwa a tsakiyar kanta, bud'e idanunta tayi da sauri ta saukesu akan maheer yana tsaye akanta riqe da tiyon da ake baiwa furanni ruwa yana mata wanka da ruwan, kallon tsana yyi mata yace" daman bawa har yana da sukunin baccin yamma koh kin manta matsayinki ne" bata fahimtar larabcin dayake amma tana fahimtar tsantsar wulaqancinsa, miqewa tayi ya nuna mata wani karensa dake keji yace" ta fito dashi ta masa wanka" yanayin yadda yake mata alama da hannunsa yasa ta fahimci abunda yake nufi, miqa mata makullin kejin da karen yake yyi ta amsa ta nufi kejin da karen yake tana qoqarin bud'e kejin shi kuwa karen sai haushi yake kamar zeci babu tunkan ta bud'eshi aikuwa tana bud'eshi ya rarumota yana qoqarin cizonta ita kuwa sai ihu take tana neman taimako tana tureshi da iyakar k'arfinta, tun abunda ke faruwa maheer na tsaye daga gefe yana kallonsu yana murmushin mugunta, turmusheta karen yyi a qasa duk yaji mata ciwo da faratansa ita kuwa kuka take sosai tana ture karen ta matsawa duk ta cire takalman k'afarta tana jifan karen dashi,kamo rigarta yyi da haqoransa ya shirin cizonta maheer yyi masa mgn da harshen larabci sakinta yyi ya koma gefe yana haushi 2kad'an yana kallonta ita kuwa duk ta jigata hk ta miqe a razane ta soma qoqarin ficewa daga farfajiyar gdn da gudu ta fice waje don ta mugun tsorata da karen, kallonta maheer yyi sannan yyiwa karen nasa alama da idanu,wani irin tsalle karen yyi yasha gabanta ya gurnanin haushi, juyowa tayi da gudu ta koma ciki ta shige wannan rumfar gezevon, karen be biyota ba ya kyaleta ya tsaya wuri guda, maheer matsawa yyi wurin karen ya tsuguna yana shafashi don ya gama birgeshi yau din nan, kallon bimbii yyi dake raku6e tana kuka yace" matsa tashi ki fito kiyi masa wanka" bata ma ji abunda yake fad'i saida ya daka mata tsawa amma duk da hk taqi fitowa daga inda take kawai kallon karen nan take, nuna karen yyi inda take ba shiri ta fito jikinta sai rawa yake, kallonta yyi ya kalli karen sai ya bushe da dariyar mugunta ya nuna mata karen da hannu wai taje ta masa wanka, gaban mugun fad'uwa yake taje ta ciko ruwa a wani kwarmi tazo ta kama karen don taga maheer dab dasu, abun mamaki karen be kuma mata komai ba har ta gama masa wankan, tunda maheer ya shige building d'insa be kuma fitowa ba bare tasa ran ze bata abinci, yunwa takeji sosai ga dare yyi ba wurin kwanciya tana dai raku6e a wannan rumfar gezevon, tsirawa sararin samaniyya idanu tayi hawaye na zarya akan kumatunta, garin da hasken farin wata gashi kuma da yalwar taurari a sararin samaniyya tana takure wuri d'aya cikinta sai qugin yunwa yake,bata ta6a tsammanin a cikin larabawa akwai marasa imani da tausayi irin maheer ba, hk tayi kwanan zaune washegari babu k'arfi a jikinta sbd yunwa amma hk take ta faman 2aikace don tasan dole ne ma tayi ko kuma yana fitowa yaga ba tayi aikinta ba ya had'ata da karensa, maheer tashinsa kenan daga bacci ya kunna sigarinsa yana sha ya fito ya tsaya a barandar gaban building d'insa yana hangawa yaga abunda ba tayi ba ko wanda ya kamata ya qara mata, gani yyi tayi komai tunkan ya tashi ta gyara furanni ta basu ruwa sannan ta baiwa kifi abinci ta share farfajiyar wurin ta wanke masa qaramar motar hawansa tayi fes, komawa yyi ciki ya fito da wani farantin silver ya ajiye a wani wuri ya juye ragowar abincin dayaci ya rage jiya da dare sannan ya kirata ta taso tazo wurin dayake, nuna mata wannan abincin yyi yace ta dauka taje taci ta dawo da farantin wurin ta ajiye, tsugunawa tayi ta dauki farantin abincin ta wuce ta tafi ta soma ci duk da bata saba da cin irin cimmarsu ba amma hk take taci sbd yunwa, tana gamawa ta komar da farantin ta ajiye a wurin, toh tun daga wannan lkcin a wannan farantin yake zuba mata ragowar abincin idan yaci yage ya ajiye mata a wurin tamkar yadda ake zubawa kare ko sauran dabbobi abinci idan sun gani suzo suci hk itama idan taga ya zuba saita zo ta dauka ta tafi taci ta dawo da farantin ta ajiye a wurin wataran ma har abincin ya soma bushewa batasan ya zuba ba sai idan tazo ta duba ta gani ta dauka hkma kuma zataci ko yunwa ta kasheta a banza baida damuwa, yau hadari ne ya had'u sosai a garin ana sanya ran samun ruwan sama a kowanne lkci ita kuwa fargabar sakkowar ruwan take don tasan kwanan tsaye zatayi a wannan rumfar, cikin dare kuwa aka soma sheqa ruwa kamar da bakin kwarya tun ruwan yana feso mata har ya jiqa cikin rumfar gbdy, miqewa tayi ta tsaya a tsaye ta qanqame jikinta don sanyi ne ke shigarta sosai ga kuma ruwan dake fesowa cikin rumfar duk ya jiqa mata jiki,kayan dake jikinta duk ya jiqe shakaf kuma gashi su kadai gareta idan ma jiqewa sukayi hk zasu bushe a jikinta, wani lkcin idan sukayi datti sosai sai ta bari idan dare yyi dare saita tashi ta ciresu ta daura mayafinsu a jikinta ta wankesu ta shanya kafin asuba ta kwashesu ta maida jikinta, hk aketa sharara ruwa har da qanqara bimbii na tsaye qanqame da jikinta tana rawar sanyi sai gab da wayewar gari ruwan ya d'auke, ita kuwa bimbii ruwan daya jiqata ya sanya mata zazza6i sosai, tashi d'aya tana miqewa jiri ze d'ebeta ga tsananin ciwon kai, kuka take tana roqon Allah kar yasa zazza6in nan ya kayar da ita tana fargabar kar maheer ya fito ya tarar bata aiwatar da aikinta ba, jan jikinta ta somayi ta soma bawa furanni ruwa duk da ruwan saman da aka kwana ana sheqawa, jiri ne ya d'ebeta ta fad'i a wurin kanta yana wani irin sarawa, rarrabawa tayi ta koma gefe ta zauna tana maida numfashi tana son taji dama dama kafin ta kuma yunqurin miqewa, maheer ranar be fito da wuri ba sai yana building d'insa yana playing wani game, wanka ya shiga sannan ya shirya ya fito da niyya zuwa gaida mahaifiyarsa, abunda ya bashi mamaki shine yana fitowa ya tarar bimbii batayi ko d'aya daga cikin ayyukanta ba, makwancinta ya nufa ransa a mugun 6ace ya tarar ruwa ya cika wurin bata ciki, fitowa yyi ya duddubawa ya hangota jingine da wata qaramar bishiyar guiba dake qarshen gdn tana yashe a zaune tayi zaman dirshan, qarasowa yyi wurin batare da la'akari da yanayin da take ciki ba yasa hannunsa ya kamo gashin kanta ya watstsaketa da wasu lafiyayyun mari har uku sannan ya jefar da ita kanta ya bugu da bishiyar guiban sannan ya soma zazzage mata ruwan bala'i batare da digon tausayawa ga yanayinta daya ganta ciki ba ya umarceta data tashi ta kama aikinta, shiru ta masa taqi motsawa daga inda take bare yasa ran zatayi abunda ya umatceta, ranta yyi mugun 6aci take taji zuciyarta ta kangare koda kasheta zeyi ta sadaqar bata yin abunda yace, shi kuwa kallonta yake kawai da mugun mamaki don ya saba duk abunda yasata ba musu bare gardama zatayi amma yau dubi taurin kan da take gwada masa, hannu yasa ya cire belt din dake d'aure a k'ugunsa ya soma dukanta dashi tamkar Allah yyi masa wahayi, duk ya farfasa mata jiki amma be fasa dukanta ba ita kuma bata motsa daga inda take ba kuma ba tsillin hawaye ko qiris a idanunta, yana cikin dukan nata yayansa zayeed ya shigo gdn, wurin ya qarasa da sauri don shi kansa yasan zuciyar maheer idan har ransa ya 6aci zai iya aikata komai, jansa ya somayi yana qoqarin fizge belt d'in hannunsa shi kuma yana tirjewa, dakyar ya iya lalla6ashi ya shigar dashi cikin building d'insa yana cika yana batsewa yana kuma huci don ransa ya 6aci sosai gani yake bimbii bata chanchanci ta masa wannan taurin kan ba a matsayinta na qasqatacciyar baiwa kuma baqar fata shiyasa cikin zaqin dayake mata har yana ce mata gorilla family wai duk baqar fata dake africa daga family na gwagwggon biri suke she never deserve to behave like this cox she is nothing but gorilla family......zagi na uwa na uba hk ya dinga sauke mata kwando kwando yyi da larabci yyi da turanci, tun shigarsu ciki tana wurin bata motsa ba don batajin idan ta miqe tsaye k'afafunta zasu iya d'aukar gangar jikinta, sai lkcin taji saukar wasu hawaye masu d'umi a saman quncinta, kallon jikinta tayi taga yadda ya farfashe da duka sai kuma tayi murmushi wanda yafi kuka ciwo,zayeed ne ya fito ya kalleta shima cike yake da fushi amma yana kallonta ya fahimci bata da lafiya shima dai ba wani daraja bayi baqar fata ke dashi a idanunsa ba amma dai yaji tausayinta kad'an, samo mata magani yyi ya bata ta amsa da godiya shiko batare daya saurari abunda take fad'i ba ya fice daga gdn yyi tafiyarsa, maheer kuwa ranar bak'in ciki kamar ya kasheshi hk ya kwana cike da qunci, washegari kuwa ya fito da sanyin safiya yaga ko batayi aikin nata ba don qiris yake jira da ita ya mata dukan da zata kusa ziyartar lahira sai kuma yyi rashi sa'a don ta gama kowanne da cikin aikin nata duk da rashi jin dad'in jikinta da take amma ba kamar jiya ba don maganin da tasha yyi mata amfani yau taji dama dama ba kamar jiya shiyasa tun safe ta lalla6a ta gama komai ta koma gindin bishiyar guiwa ta zauna, cike da haushi ya koma ciki ya kwanta akan doguwar kujerar dake qaramin parlourn nasa yana fitar da hayaqin sigarin dayake busawa,hoton bimbii ne ke dawo masa lkcin dayake dukanta, idanunta qamas suke babu alamun kuka, zumbur yyi ya miqe ya kuma fita ya tsaya a barandar dake
Chapter 4 · 0% Book details