← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 59

Sashe 12

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani qasaitaccen k'amshi taji yana tashi ya had'e da ni'imatacciyar iskar dake kad'awa cikin wannan lambu, tashi tayi zaune ta leqa qasan bishiyar don ganin abunda ya haddasa wannan qamshi, abunda ta gani ne yyi mugun kad'a y'ay'an hancinta, PRINCE AKBAK!!.ne shida hadiminsa na hannun dama wato ubaid, tun shigowarsu suka ganta bisa bishiya abun yyi mugun basu mamaki, baiwa cikin lambu babban prince, ita kuwa bimbii tsabar tsorata kasa had'iye tuffan dake bakinta tayi ta sake baki tana kallonsu tamkar wata doluwa, prince akbar kuwa ko kallon bishiyar da take be sakeyi ba yyi gaba abinsa cikin qasaitaccen takunsa da yake bayyana tsantsar izzarsa da kuma isar matsayinsa, ubaid ya gama sanin halin babban prince, idan yana son bashi umarni da ido kawai idan ya kalleshi yana sanin me yake nufi take ze aiwatar, shi prince mgnr ce take masa mutuk'ar wahala tamkar d'an kurma hk yake sai tayi masifar kamawa yake bud'e bakinsa yyi mgn, wata irin tsawa ubaid ya doka mata wanda sauran qiris ya rage ta saki fitsari a wando ba shiri ta diro daga saman bishiya ta kife akan guiwowinta, kallonta ubaid yyi cike da qasqanci yace" wace ce ke? yanayinki kawai ya tabbatar min kedin qasqantacciyar baiwa ce amma ki rasa ina ya dace ki sauke raininki sai a lambun babban prince" kuka bimbii ta soma masa tace" don Allah kuyi hkr wallah ni bansan lambunsa bane" ubaid tsayawa yyi kawai yana kallonta don tabbas shi kansa ya yaba da k'arfin halinta, fuskarsa a murtuke yace" kije ki jira a waje" miqewa tayi sum sum tana d'an waiwayen baya musamman qaramar k'ofa dake cikin lambu da taga prince akbar ya shiga ya barsu a wurin,ubaid kuwa yana ganin ta fice yabi bayan prince cikin k'ofar shima sai gashi ya fito wani babban fili, prince ya hango yana gwada saitin harbin mashi, sauri yyi ya qarasa gefensa ya tsaya yana miqa masa masun dake hannunsa shi kuma yana amsa yana harbawa daidai saitin wata bishiya, bimbii kuwa tana wajen lambun tana jiran fitowar ubaid amma shiru shiru babu shi babu alamarsa har gari ya soma lumshewa,rana na dab da faduwa suka fito daga lambun tasha jira har ta gaji bacci ya dauketa a wurin, sai lkcin prince ya kalleta sosai tana baccinta a wurin, tsayar da idanunsa yyi sosai akanta abun har ya bawa ubaid mamaki don be ta6a ganin prince ya qurawa abu idanu hk ba, bud'e idanunta tayi a hnkli taga inuwar mutum tsaye akanta, k'afarsa kawai ta kalla tun kafin ta dago da kanta tasan mutum ne da hutu ya gama ratsashi,k'afarsa sanye take cikin wani farin takalmi half cover shoe, tunda take bata ta6a ganin mutum mai kyawun k'afa irin prince akbar ba, kafar nan tasa luwui luwui tamkar tumatir gata jajir da ita kamar ka matsa jini ya fito, jallabiya ce fara sol a jikinsa sai rawanin daya rufa a kafadarsa dayake ja da fari, gashin kansa baqin qirin ya sauka har kafadarsa yana rawa tamkar na mata,idanunsa tamkar yasa tozali gasu a lumshe kamar yanzu ya tashi daga bacci,sassayan k'amshinsa ne ya cika hancinta,dago da fuskarta tayi suka hada idanu take taji gabanta ya tsananta bugawa, yana ganin ta dago da idanunta yyi saurin dauke kansa akanta ya haye dokinsa shima dokin nasa fari, alamu sun nuna prince din yana qaunar farin abu, kallon ubaid kawai yyi shima ya haye dokinsa suka barta a wurin batare da sun ce mata komai ba, bin sawun dawakansu tayi da kallo har suka qurewa ganinta, tashi tayi tana karkad'e qasar dake jikinta ta soma tfy har ta isa inda ta ajiye tulunta yana nan inda tabarshi ta cika ruwanta ta dora aka ta nufi cikin gd,tunkan ta qarasa ta hango uwar bayi ummul shukri da tsumangiyanta a hannu, tana sauke ruwan ta rufeta da duka tace" tun safe ko aiki guda bakiyi cikin ayyukanki ba sai yanzu kk kawo sawun ruwa daya" shiru tayi batare data kawo wani uziri ba,ummul shukri bata amsar uxiri ko qaqa,fito mata tayi da wasu manyan barguna tace ta kwasa taje ta wankesu gashi dare ya soma shiga sosai don ma garin da hasken farin wata hk ta kwashi barguna ta nufi babbar qorama dasu ta soma tiqar wanki, tana cikin shanyawa ta gano inuwar mutum a bayanta, juyawa tayi da sauri idanunta ya gane mata prince nasaar, murmushi yyi mata da fararen haqoransa yace" wankin dare kuma baki tsoron mura" wani irin murmushi tayi tamkar kuka iyakarsa le6enta tare da rissinar da guiwowinta tana gaishe shi, tsugunawa yyi kusa da ita yace" ina buqatar kwarkwara kuma ke nkso" kalmar taji tayi mugun bugarta ta zaro manyan idanunta waje tare da dafe kirjinta tace" na shiga uku, wlh ni ban iya komai ba" dariya ta bashi yyi har jerarrun haqoransa suka bayyana yace" zaki koya ai, zaki zama baiwar dake kula dani kwanan nan" gabanta ke faduwa sosai tana kallonshi, babban abunda bimbii ke karewa a wannan yanayin data tsinci kanta aciki na bauta shine budurcinta bata qaunar abunda ze iya rabata da budurcinta, zama kwarkwara a gdn sarauta ai dole sai ka rabu da budurci kuma ga hadari na daukar ciki, itakam tafi qaunar ta cigaba da kasancewa a baiwa mara gata idan har budurcin bazai ta6u ba, sanya hannunsa yyi da niyyar riqo hannunta ta daka wani uban tsalle tayi gefe, abunda tayi yyi masifar daure masa kai,tunda yake ba baiwar data ta6a masa hk sai bimbii shi gani yake kamar taimakonta zeyi amma har ta gwada masa wannan cin fuskar a matsayinsa na jinin sarauta yace"bimbii wannan abunda kkyi kuskure ne babba kar ki kuma gwada hkn ga duk wani jinin sarauta" yyi mgnr fuskarsa a sake tamkar beji haushin abunda ta masa, shiru tayi ta sunkuyar dakanta qasa, wani dutse ya nuna mata yace" ta zauna ta tayashi hira" ji tayi kamar ta kurma ihu amma ba yadda ta iya hk ta zauna daga can gefe ta dosana duwawunta akan dutsen, Allah ya sota ta gama wankinta, murmushi yyi don yana lura da rashin sakewarta yace" bani labarin qasashenku na baqar fata tare da al'adunku" shiru tayi ba tace komai ba, shan kunu sannan ta sauka daga kan dutsen ta sauke guiwowinta a qasa tana roqonsa tace" don girman Allah ka rufamin asiri kabarni na koma bakin aiki na"murmushi yyi yace" wannan ce kawai buqatarki?" ta daga masa kai alamar ehh, yace" shikenan jeki saida safe" miqewa tayi da sauri tabar wurin tana qara dubawa don tabbatar da cewa babu wanda ya ganta tare da prince nasaar, shi kuwa yana daga zaune yana kallonta harta 6acewa hangensa, tana shiga 6angarensu taga su israt da khulood sai zaman jiranta suke suci abinci, suna ganinta kuwa suka tarota da murna suka tmbyta abunda ya sanya ta jima bata fada musu komai ba game da abunda ya faru da ita, suna gama cin abinci israt ta kalli bimbii da murmushi a fuskarta tace"albishirinki!" bimbii ta kalleta tace"goro" israt tace" babban prince ya fitar da ranar za6en sabuwar baiwa dake kula da 6angarensa, nida khulood muna son shiga gasar saidai bamu da chanchata sbd rukunin bayin da muke ciki basu shiga za6en" murmushi bimbii tayi tace" tab, amma kuna da karfin hali waye ya aikeni nikam bani so" khulood tace" wlh nima bawai don ina da sha'awar hkn nakeson shiga ba saidai hkn shine nake ganin ze taimakamin wurin jeton lailah daga wannan hukunci kinsan har an kaita kurkun qasa fa" bimbii tace" kamar ya kenan" khulood tace" idan kina wannan matsayi zaki samu dama sosai wurin neman alfarma wurin babban prince don shine na biyun sarki a wannan masarauta" shiru bimbii tayi sai kuma ta dago da kanta tace" kuna ganin hkn bazai ta6a budurcinku ba" dariya sukayi gbdynsu, israt tace" tab, ai nikam idan prince akbar ya buqaceni da gudu zan miqa wuya don burina ya cika" bimbii sakin baki tayi kurum tana kallon israt da mamaki shimfide kan fuskarta, khulood tace" kaf cikin bayin da suka ta6a kula da 6angaren prince babu wacce ya ta6a nema duk kuwa wacce yau babban prince ya amshi budurcinta dole ta burge kuma dole tayi alfahari dakanta don ta isa mace" bimbii kallon khulood take da tsantsar mamakin kalamanta,gyara zama tayi tana fuskantarsu tace" toh ya akayi kksan baya nemansu" murmushi sukayi israt tace"ai al'adar wannan masarauta shine babban prince dakansa yake za6en baiwar da zata kula dashi duk wacce ta samu nasara za'a sanar a wurin za6en amma matakin qarshe na za6en idan har prince ya samu baiwar a matsayin disvirgin wato ba danyar budurwa ba toh hukunci mai tsauri ze hau kan baiwar shiyasa duk wadanda suke shiga gasar sai sun yarda da kansu, abu na gaba kuma idan ya sameki a cikakkiyar budurwa toh washegarin ranar baiwar zata fito da zanin gadon daya 6aci zuwa babbar qorama ta wankesu dakanta cike da alfahari, hkn shine shaidar dake nuni prince shine ya fara saninta diya mace kuma zata cigaba da kasancewa a matsayin baiwarsa koda ya sake sabuwa kuma sarauniyya zata mata kyautar girma sbd ta faranta ran d'anta ta bashi babbar kyauta,toh shi prince akbar har yau duk bayin da yake za6e babu wacce ta taba fitowa da wannan shaida balle sarauniyya tayi mata kyauta sannan ba'a ta6a samun wacce hukuncin rashin budurci yahau kanta ba hkn na nuni da cewa prince akbar be ta6a kusantar ko daya daga cikin bayinsa ba, kinji dalilinmu" ajiyar zuciya bimbii tayi tana al'ajabin wannan al'ada tasu tamkar ta larabawan farko, khulood tace"idan kk kasance baiwar prince kin tsira kenan don babu dan iskan dazai nemi keta miki haddi kina matsayin baiwa ga prince akbar" shiru bimbii tayi tana tunani, tabbas idan hkne gwara ta shiga gasar don tana tunanin abunda prince nasaar yace da ita yau, wai zata zama kwarkwararsa, kallon khulood bimbii tayi tace" toh su kuma sauran princes din fa suna kwatar budurcin bayin nasu" khulood tace" sukam kowacce baiwa suka za6e washegari take fitowa wankin zanin gadon daya 6aci" shiru tayi sai kuma ta dago da kanta tace"tabbas nima idan zan samu dama zan shiga gasar prince akbar kodan lailah" rumgumeta sukayi suna dariya, saidai tunaninsu yanzu shine rashin cancanta musamman bimbii da take ba balarabiyar usul ba shikansa wannan naqasu ne gareta...........
Chapter 12 · 0% Book details