← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 59

Sashe 7

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana farfad'owa ta ganta kwance bisa busassun ciyayi a yashe tsakiya wani d'aki mai yalwar teburan katako da tsoffin kwabobi, gefenta wasu y'an mata ne su uku kyawawa dasu jinsin larabawa saidai alamu sun nuna tamkar suma suna da tambarin bauta tattare dasu, suna ganin ta farfado suka matso kusa da ita suna mata sannu cikin harshensu na larabci, dayake tana d'an fuskantar larabcin 2kadan sai ta d'aga musu kai kawai ita dai sai qarewa d'akin kallo take tana tunanin yau kuma ina Allah ya jefota, hannun suwa kuma ta fado, d'ayar da taji suna kira da khulood ta miqe ta fita da sauri ba jimawa sai gata sun shigo da wata tsohuwar balarabiyya, tana tafe tana dogara sandarta, doguwar riga ce ruwa k'wai a jikinta ta yane kanta da mayafi amma hkn be hana gashin kanta dayake fari fat da furfura leqowa ba,wuyanta da wata katuwar sarqa,kunnuwanta kuma da wasu manya yan kunne sai yatsun hannunta kusan dukka da manya zobuna na azurfa, fuskarta a tamke ba alamun fara'a tana shigowa sauran y'an matan bayin nan suka rissinar da dakansu qasa alamar girmamawa ga uwar bayi ummul shukri, bimbii kuwa kallon tsohuwar kawai take,itako uwar bayi ummul shukri sandarta ta sanya ta d'ago da ha6ar bimbii tana qarewa fuskarta kallo musamman cikin idanunta don mafi yawan larabawa suna karantar sirri zucciyar mutum ne ta cikin k'wayar idaniyansa shiyasa uwar bayi ummul shukri ta qure bimbii da idanu tana karantar sirrin zucciyarta ta k'wayar idanunta, bimbii kuwa sai tayi sauri yin qasa da idanunta kamar yadda taga sauran yan matan bayin sun mata, tana ganin bimbii ta rissinar da idanunta qasa sai tayi wani d'an murmushi na gefen baki ta d'auke sandarta daga ha6arta ta kalli khulood tace" ki bata abinci" tana fadar hk ta dogara sandarta ta fice daga dakin bayin,khulood ta tashi da sauri ta fita don kawowa bimbii abinci itama israt ta tashi ta kawo mata ruwan sha cikin wani kofin tasa daidai lkcin khulood itama ta shigo da wani qaramin kwanon tasa da abinci a ciki,duk suka sanya mata a gaba, bimbii kuwa daman da yunwa ta tashi don hk batare da wani kunya ba ta wanke hannunta da ruwan da suka kawo mata, ta soma cin abincin duk da a ido ta raina yawan abinci suna kallonta ta gama cin abinci tasha ruwa tayi hamdala,khulood ta kalleta da murmushi tace ta tashi su fita ummul shukri na son ganinsu, ba musu ta miqe tabi bayansu suka dinga wuce kusurwowi har suka shiga kusurwar da ummul shukri take, zaune take bisa kujera tana riqe da sandarta suka durqusar da guiwowinsu dukka a gabanta tare da rissinar da kawunansu qasa suna jiran umarninta, itama yadda taga sunyi hk tayi, ummul shukri ta kalle bimbii ta soma mata mgn cikin harshen larabci tace" kin san inda kk yanzu?" girgixa kai bimbii tayi alamar aa, tace" kina gdn sarautar burham,kina cikin jerin maqasqatan bayin masarautar burham"nuna mata su khulood tayi da hannu tace"rukunin aiki iri d'aya zasu nuna miki naki aiki ciki" rissinar dakanta tayi alamar ta amsa yadda dai taga sunayi, sallamarsu tayi suka miqe suka fice, bimbii sai bin wannan gdn sarauta take da kallo don tsarin ginin masarautar ya birgeta sosai, gani tayi bayin gdn sai kai kawo suke,matan kusan dukkaninsu da mayafi a saman kansu,mazan kuma yawancinsu da rawani a kansu,ko'ina na gdn zagaye yake da furanni masu kwantar da zucciya, gdn kusurwa kusurwa ne, kowacce kusurwa an mata yanayi kamar kofar masallaci sanda sanda, israt da khulood na gaba, laila da bimbii na biye dasu,fita sukayi daga wannan 6angaren suka wuce wani wuri suka dauki kwanduna, lailah ta dauki kwando daya ta bawa bimbii ta amsa ta riqe suka sake ficewa daga wannan 6angaren sai tfy suke har suka fara fita daga inda gine gine suke suka soma shiga jeji jeji kuma fa duk a cikin gdn suke, bimbii dai sai binsu take, wani lambu mai cike da bishiyoyi na kayan marmari suka shiga, khulood ta hau bishiyar zaitun, israt tahau bishiyar tuffa suna tsinkowa suna jefo musu su kuma suna tattarawa suna zubawa a kwandunansu, saida suka cika kowanne kwando sannan su khulood da israt suka sakko kowacce ta dauki kwandonta ta dora a saman kanta suka fice daga lambun suka nufi cikin gd, suna cikin tfy wasu samari suma bayi ne suka tare musu hanya,abunda ya baiwa bimbii mamaki shine ashe kowacce cikinsu tana tafe da qaramar wuqarta a cikin jikinta sai gani tayi duk sun sauke kwandunansu sun sanya hannu cikin fatarinsu sun fito da qananan wuqaqensu sun tsatstsaya suna sauraron su ga me zasuyi musu su soma yankarsu, bimbii kuwa ta qame a tsaye da kwandonta a saman kanta cike da mamaki, su kuwa suna ganin yan matan sun fito da wuqa sai suka wuce abinsu saida suka ga sunyi nisa suka maida wuqaqensu cikin jikinsu suka sunkuya suka dau kwandunansu suka cigaba da tfy,su mazan larabawan wannan yankin Allah ya zuba musu son jikin mace ba wuya suke yiwa yan mata fyade shiyasa yan matansu ke yawo da wuqa sbd tsaro, bimbii dai tana ganin abun mamaki cikin wannan gd sbd ita daman tunda ta shigo qasar kuwait tana qunshe ne a wuri daya batasan al'adunsu ba sai yanzu da Allah ya jefota gdn sarautar burham, wani qaton kitchen suka shiga, kitchen bayi ne ciki keta hidima, shugabar bayin dake wannan babban kitchen din mai suna jahan ita ta amshi kwandunan nasu ta jujjuye kayan marmarin a cikin wasu manyan kwanduna dake kitchen din ta basu kwandunansu, duk bayin dake hidima cikin kitchen din sai bin bimbii suke da kallo tamkar sun ga wata sabuwar halitta,lallah ce taja hannun bimbii suka fice daga kitchen din,maida kwandunan sukayi suka koma wani 6angaren suka fito da wasu manyan barguna suka nufi wata qatuwar qorama dake dake tsakiyar gdn suka dauko wasu manyan abubuwan wanki da akayisu da katako suka soma dirzar wankin wannan manyar barguna sai yamma liqis suka kammala ayyukansu suka koma 6angarensu,su hud'u ne a dakin nasu,khulood,lailah, israt sai yanzu da aka kawo musu bimbii, dukkaninsu akan wannan busassun ciyayin suke kwana tamkar shine suka maida katifarsu saidai su shimfida mayafansu akan ciyayin su kwanta, ita bimbii ranar kam bacci tayi mai dadi don kuwa gani take ta samu cigaba tunda har ta samu damar kwanciya cikin daki ba'a rumfa ba kuma har ta samu albarkar kwanciya a ciyawa ba'a dandamalin k'asa ba wannan kadai cigaba ne a wurinta bata damu da tiqar aikin da suke ba don daman tasan ta ita baiwa ce kuma tana cikin qangin bauta,kwanan farin ciki tayi ga qawaye ta samu da basu nuna mata zangwama ko kadan sun dau kansu tamkar yan'uwa hk suke rayuwarsu tamkar jini daya kuma kusan dukkaninsu sun fito ne daga qasashe mabambanta saidai su duk daga qasashen larabawa suke masu makwabtaka da qasar kuwait ita kadai ce baqar fata daga africa, washegari da sanyin safiya duk suka tashi, tunkan su fita ummul shukri ta shigo ta kama tsintsiyar qafar bimbii ta sanya mata wata qaramar sarka irin wacce wasu matan ke sanyawa a qafa sbd ado su kuma wannan sarqar qafan itace alamar dake nuni da rukunin bayin da suke shiyasa taga suma su khulood kowacce da wannan sarqar a qafarta ita da ta dauka sbd ado suka sanya ashe shine tambarin rukunin bayin da suke,kallon qafar tayi taga sarqar ta mata kyau, miqewa tayi suka fice, ranar kwaryoyi suka dauka suka tafi tatsar nonon raqumi,kowacce saida ta cika kwaryarta da nonon sannan suka dauko suka taho kai tsaye wannan babban kitchen suka kai nonon aka juye a charkoki, daga nan suka wuce kowacce ta dauki tulunta suka tafi babbar qorama don debo ruwa, saida suka ciccika duk wasu abubuwan tara ruwa na 6angarori 2daban sai yamma liqis ranar ma suka koma 6angarensu, bayan sun gama cin abinci suna shirin kwanciya lailah ta fito da wata sabuwar wuqa yar qarama ta miqawa bimbii tace" ki riqe wannan kema sbd akwai hadari ki din ga yawo babu abun kare kai kin ga kema budurwa ce saiki sanya budurcinki cikin hadari" amsar wuqar bimbii tayi mata gdy sannan ta sanya wuqar qasan wurin kwananta......

***
Chapter 7 · 0% Book details