← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 59

Sashe 52

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

angaren maheer kuwa jikin nasa babu laifi har sun koma gd amma ba gdnsa ba gdn ennah, 2kwata rayuwarsa ta sauya ya koma wani irin miskili 2shiru baya shiga sabgar kowa, duk lkcin kuwa daya samu ke6ewa shi kadai sai yyi ta zubda da hawaye shi kansa besan wani irin mugun so yake yiwa bimbii ba,tabbas soyayya tayi masa mummunan kamu, idan ya rufe idanu fuskarta kawai yake gani, likita yace a dena barinsa ya ke6e shi daya sbd wannan tunanin dayake yawan yi kan iya haddasa masa bugawar zuciya farat daya tayi ajalinsa hknne yasa ennah fitowa ta taddashi a parlour shi kadai, wurin tv ta nufa ta kunna masa tashar NYA sbd kallon labaran ya debe masa kewa, kitchen ta shiga ta yanka masa fruit a wani bowl ta fito ta jawo wani stool gabansa ta ajiye masa bowl din fruit din ta koma ta zauna ta sanya siririn medical glass nata tana duba wasu documents, maheer yana shan fruit din a hnkli yana kallon labaran da ake a tasha NYA daidai lkcin suka hasko prince akbar sanye yake da alkyabba golden da farar jallabiya ciki sai rawani fari sol, sajen nan nasa yasha gyara fuskarsa dauke da murmushi, 2kalan hotunansa suka cigaba nunawa suna bada lbrin aurensa da kuma kyautar yan uku daya samu daga princess dinsa wacce take baqar fata daga daga africa, hkn shine yasa ennah dago dakanta ta kalli maheer da dukka attention nasa yana kan labaran tace" yanzu duk isa da qasaitar prince akbar a baqar fata ya qare yana jinin sarautar burham,one in history" kallonta maheer yyi yace"ra'ayinsa kenan kuma ai yana sonta ne shi so ba ruwansa da kalar fata" shiru tayi ba tace komai ba ta maida kanta ta cigaba da bin document din dake hannunta shima ya cigaba da kallonsa daidai lkcin suka fara nuna hotunan bimbii da prince, dukkanin hotunan nasu yana bayyana tsantsar soyayyar dake tsakaninsu koda daga yanayin kallon dake kwayar idanunsa suna jifan junansu, ya daga cup din ruwa kenan ze sha idanunsa suka sauka kan hotunan take glass cup din dake hannunsa ya fadi qasa ya tsaida idanunsa akan screen din tv baya ko blinking sai kawai zuciyarsa dake bugawa da qarfi tamkar zata tarwatse,qarar fashewar cup din ne yasa ennah dago dakanta tana kallonshi, gani tayi ya qure tv da idanu sai ta maida kallonta kan tvn, abunda ta gani ne itama yasa ta saurin watsar da takardun dake hannunta ta miqe da sauri ta wuce ta kashe tvn, juyowa ta matso inda yake ta dafashi kawai sai gani tayi ya fadi kan kujerar cikin sauri ta soma girgixa shi baya koh motsi, fashewa tayi da kuka gbdy ta rude ta cigaba da jijjigashi tana kiran sunan shi amma inaaa, tashi ta janyo telephone ta dannawa faisal kira yana dauka yaji kukanta tana tace" kazo gd maheer ya mutu" kalmomin data iya fada kenan ta kife kan telephone din ta koma wurin da maheer yake tana jijjigashi kamar wata mahaukaciya duk ta fice daga hayyacinta don ba qaramin son yara ne da ita ba, ba jimawa faisal ya shigo ya tarar da halin da dan'uwansa ke ciki shima hnklinsa ya tashi sosai hk suka fito dashi suka saka shi cikin mota suka nufi hospital, cikin hanzari aka wuce dashi emergency sbd ya shiga coma sosai, sai dare likitoci sukayi samu zuciyarsa ta soma bugawa a hnkli, likitan daya fito ya fara fada sosai yana cewa meyesa suka bari hk ya faru yace tabbas yaci karo da abunda ya tada hnklinsa ne shine silar bugawar da zuciyarsa tayi yanzu dai yana cikin wani hali wanda saidai kawai addu'a amma abun yyi tsanani, wadannan kalamai su suka qara daga hnklin ennah ta kifa kan a jikin faisal tana kuka kamar ranta ze fita,gani take kamar mutuwa maheer zeyi gashi dai su biyu kawai Allah ya bata kundai san larabawa da shegen son y'ay'an tsiya, faisal mai dan qarfin halin rarrashin mahaifiyar tasu shima dai kaeai shanye kukan nasa yake, tace" tabbas rashin sani yafi dare duhu idan da nasan yariyar nan itace muguwar qaddarar maheer mezai sanya na siyeta da kudi na, gashi yanzu tana son kashemin yaro" hk dai tayi ta maganganu faisal na rarrashinta,6angaren masarautar burham kam gimbiya mariyatul qifdiya ta sato jiki ta taho masarautar burham burinta kawai ta sake tozali da prince akbar bazata iya jure rashinsa ba, sarauniya ta mata tarar girma sosai, sarki abdallah yana kwance har yau jikin nasa qara tsanani yake sbd tarin damuwa dake addabarsa, kullum cikin tunanin hanyar dazai bi ya yakice bimbii daga masarautarsa yake duk kuwa da halin rashin lfyr dayake jiki,lkcin da lbrin zuwan gimbiya mariyatul qifdiya ya kawo gare shi be bata lkci ba yyi umarni a rubuta wasiqa a aika masarautar abu ansar kamar yadda shima ya aiko masa da zafafan kalmomi hk shima ya aika masa batare da sanin sarauniya don itakam bazata so hk ba sbd mariyatu ta sanar mata mahaifinta besan ta taho ba, lkcin da sarki abu ansar ya krt wasiqar nan ransa yyi masifar 6aci don cikin wasiqar sarki abdallah ya fada masa jinin sarautar burham suna da cikakkiyar izzah da basu bibiya saidai a bibiyesu hknne yasa yarsa tayi tattaki har gdn sarautar burham don samun soyayya mafi girma, wannan batu ya 6atawa sarki abu ansari rai yyi Allah wadai da abun da diyarsa ta aikata, sanyawa yyi aka kira masa gimbiya khamriyya ya soma mata fada kan dalilin dayasa ta kyale gimbiya mariyatu ta aikata wannan abun kunya don ta zubar masa da mutunci da tozarta izzar masarautar abu ansar, sunkuyar dakai gimbiya khamriyya tayi tace" Allah ja zamanin sarki mai daraja tabbas mariyatu tana qaunar yarima akbar dayawa wannan shine dalilin dayasa ta kasa jure hukuncin daka yanke ta nufi masarautar burham batare da sanin kowa ba, ina roqon alfarma a gareka sarki mai daraja kar ka sauke fushinka akanta bisa wannan laifi data aikata mafi muni" shiru yyi ya juyar dakansa tare da daga mata hannu ta miqe jiki a sanyaye ta fice.........

Manage this page pls.

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw toh ki biya #300 ta wannan acct...0100790419,Alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon da screenshrt na payment ta whatspp ta wannan layi....07041195806...

Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: 47*****
Chapter 52 · 0% Book details