← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 59

Sashe 35

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Littafin nan na kudi ne, idan kin idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct.....0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turomin da screesht ta whatsapp da wannan layin 07041195806......

Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

28

*You are the only one I can hear*.....You are the only one I can feel cox you are are the reason of my living💕💕

Bimbii kuwa tunda ta fada wannan dogon rami bata kuma sanin inda kanta yake, dulmiyewa tayi cikin wannan ruwan dake kwaranya tamkar na 6ul6ula, ruwan zuba yake shaaaa daga jikin wani dutse gashi fari tas dashi, karfin ruwan ne ya janyeta ta fada wani qaton ruwa wanda yyi iyakar yankin burham da yankin dilham, wannan ruwa shi ya raba tsakanin yankunan guda biyu,qananan jiragen ruwa da manyan kwale kwale masu safarar bayin zuwa yankunan qasashen larabawa 2daban suna ratsawa ta wannan dogon kogi, igiyar ruwa ce tayi tfy mai nisan gaske da ita takaita ga6ar wannan kogi cikin izinin ubangiji wani mutuqin kwale kwale mai suna abeed ya hangi gangar jikinta a yashe gefen wannan kogi igiyar ruwa ta watso ta ga6a, cikin sauri ya nufi wurin don tabbatarwa kansa yana zuwa kuwa ya ganta kwance babu alamun ruhi tattare da gangar jikinta, sunkuyawa yyi yakai hannunsa daidai wurin bugawar numfashinta yaji shiru, duk da hk be hkr ba yasa hannu ya dinga dannan cikinta ruwa ya soma fita mata ta hanci ta baki har saidai ruwan data sha ya fita, jikinta yyi sanyi tamkar qanqara hkn ya tabbatar masa cewa ta jima a cikin ruwa, yatsunsa biyu ya kuma pointing kan qahon zuccinta sai lkcin yaji dif dif alamun akwai sauran ruhi tattare da gangar jikin nata, daukanta yyi yasata cikin kwale kwalensa ya shige ya soma tuqa kwale kwalen nasa har suka fita asalin ga6ar da yake da 2hadar jama'a, duk wanda ya gansa sai yyi zaton baiwarsa ce ta kasa har jaje ake masa hk ya samu ya wuce da bimbii, abeed mutumin dilham ne kuma masunci ne yana zaune shi da iyalinsa a wani qaramin gdn katako kusa da wannan kogi, matar shi daya da d'ansa daya dan kimanin shekaru ashirin sunan shi farhan, matar shi saudat ta tausaya mutuqa da taga halin da bimbii ke ciki, hk suka din ga bata taimakon daya dace kasancewarsu masunta, saudat ta dumamawa bimbii jikinta sosai yadda jikin nata ya dauki dumi sosai, kallon daya ta yiwa bimbii ta fahimci tana dauke da juna biyu, hk suka cigaba da bata duk wani taimako kusan sati guda kenan amma bimbii bata ta6a koda motsi ba bare su sanya mata ran samun lfy, dansu farham a lkcin yana high schl ne ajin qarshe, ba wasu mawadata bane talakawa ne saidai sun fi qarfin cikinsu, bimbii saida tayi sati uku chur tana kwance tamkar mutum mutumi amma basu gjy da kula da ita ba, yau da dare saudat tana kasa mata jiki kawai taga yatsun qafarta sun motsa, murza idanunta tayi ta kuma kallon kafarta taga tabbas motsi take da yatsun qafarta, kwalawa danta farhan kira tayi suka shigo cikin dakin da gudu shi da abeed, nuna musu yatsun kafar bimbii tayi su ga tana motsasu, murna sosai suka somayi tamkar wata jininsu,washegari, da sanyin safiyya saudat ta shigo dakin da bimbii ke kwance sai ganinta tayi idanunta bude tana 2kalle dasu, matsowa tayi da gudu ta zauna kusa da ita ta riqo hannayenta tana mata sannu, ita kuwa kawai binta take da idanu tamkar wata kurma,6angaren prince akbar kuwa shikam be dauki wani tsawon lkci ba, kwanan shi biyar kwance abbas yana bashi magungunan da suka tsuge dafin mashin daya soke shi, a kwana na biyar ya bude idanunsa, ubaid da abbas ba qaramin dadi sukaji ba na ganin prince ya farka, suna dai cikin wannan kogon dutsen dashi sbd sarki abdallah bin jabal har yau be hkr da nemansu ba, prince akbar ya zamto wanted ga masarautar burham,mtslr shine har yanzu suna cikin yankin masarautar burham basu da hnyr da zasu iya ficewa daga yankin masarautar burham sbd nemansu ake ruwa a jallo, prince akbar ya farfado kuma yana cigaba da amsar magani wurin dattijo abbas saidai tunda ya farfado har yau be tankawa kowa ba, da tunanin bimbii ya farka ita kawai yakeson gani a halin da yake ciki, d'an sarki mai cikakken izzah wanda ya saba kwana bisa tattausa yau shine ya samu kansa cikin wannan kogon dutse amma shi duk ba wannan ne ya dame shi ba,babbar damuwarsa shine shin bimbii tana raye ko tana mace, idan har bimbii bata raye toh shikam be ga amfanin tasa rayuwar ba sbd itace mahadin ruhinsa itace bugawar numfashinsa, wadannan irin tunani su suka zame masa sana'a, ubaid ya fara damuwa da yanayin da yake ganin prince ciki sai yake ganin kodai ya samu wata mtslr ne, dattijo abbas yace ya kyale prince ya kadaice da zuciyarshi, prince akbar ko gama samun sauqi beyi ba ya fito daga wannan kogo, ubaid ya kalleshi ya rissinar dakansa qasa yace" ranka ya dade dakarin masarauta sun bazu ko'ina nemanka kawai suke idan kayi wani wuri yanzu zasu iya ganinka" kallon prince yyi sannan ya dauke kansa ya juya sai can yace" gudu yana ga raggo ne amma namiji baya gudu a fagen fama koda hkn na nufin ajalinsa" yana gama fadar hk ya kama dokin dake daure yahau ya sakar masa linzami yabar wurin, kai tsaye wurin ramin daya tura bimbii ya nufa, yana qarasawa wurin ya sauka daga kan dokin ya nufi wurin ramin ya leqa qasan ramin ya tabbatar da tsayinsa batare da wani shakka ba ya soma shirin afkawa cikin dogon ramin shima ya isa duniyar da bimbii take, murya da yaji bayansa ne yasa shi juyawa, ubaid ne yace" ranka ya dade kafin ka aikata hkn ya kamata kasan halin da sarauniya take ciki tun ranar daka bar masarauta ta kwanta babu lfy kuma jikinta ya tsananta tana da burin sake ganinka kar ka kashe kanka batare daka gana da mahaifiyarka ba" kalaman ubaid sunyi tasiri mutuqa sun sanya ya soma begen ganin mahaifiyarsa duk da laifinta gare shi amma uwa ai uwa ce" jiki a sanyaye ya koma ya haye dokinsa kawai bisa mamakin ubaid sai kawai gani yyi babban prince ya dauki hanyar masarautar burham, tun daga nesa dakarin dake tsaron kofa suka hango shi batare da wani 6ata lkci ba suka bude masa kofar wannan gdn sarauta ya shige da dokinsa, duk wanda yaga prince sai ya cika da mamaki, tuni wannan albishir yakai kunnen sarauniya sannan yakai ga sarki abdallah bin jabal, umarni ya bayar a rufe kowacce kofa ta wannan masarauta sannan ya sake bada umarni a kama prince a miqashi kurkun qasa, prince yana sauka daga dokinsa yaga dakarin tsaron wannan gd sun tsagayeshi ta ko'ina dukkaninsu riqe da makamai, sarauniya bata da masaniyyar wannan umarni da sarki abdallah ya bayar saida ummu nana ta shigo ta shaida mata, prince kuwa fuskar nan tashi tamkar hadari ya kalli wadannan dakaru yace" duk wanda yakeson uwarsa ta haifi wani ya cigaba da tsayuwa anan" dukda sun san jarimtarshi amma basu kauce ba don suna mtuqar shakkar mahaifinsa sarki abdallah bin jabal, prince wata qaramar wuqa ya ciro daga jikin dokin dake gabansa ya nufi shiga cikinsu, kai tsaye yaji muryar mahaifiyarsa daga bayanshi tace" idan har nina haifeka kar ka kuma aikata wannan abu,bani son ka kuma zare takobinka bisa umarnin mahaifinka kabi umarnin shi" juyawa yyi a hnkli ya hango an turota a wheel chair, sauke wuqar dake hannunsa yyi ya qarasa inda take a hnkli ya tsuguna gabanta ya dora kansa bisa cinyarta ya rufe idanunsa, hawaye take sosai tasa hannunta tana shafa kansa, daidai lkcin sarki abdallah bin jabal shi da tawagarsa suka qaraso wurin, fuskarshi babu digon afuwa, dago dakai prince akbar yyi ya juya sukayi ido hudu da mahaifin nasa, dauke kai sarki abdallah yyi ya kalli dakarun dake wurin yace" ku miqashi kurku" kafin ya rufe baki sun matso wurin da prince yake suka kama shi, saurin cire musu hannu yyi daga jikinshi ya kalli mahaifin nasa yace" zan tafi dakai na" wucewa yyi gaba suka bishi a baya, sarauniya ta fashe da kuka ta kalli sarki abdallah tace" don Allah kayi masa aikin gafara" be kalleta ba bare ta sanya ran ze bata amsa ya juya abunshi yan fadansa suka take masa baya, ummu nana ta tura wheel chair din da sarauniya ke kai ta koma da ita 6angarenta tana kuka, ita kanta tasan sarki abdallah ba qaramin kafiya ne dashi da taurin kai ba shima kuma dan nasa hk yake ai gado ba karambani bane, bude masa kofar kurku sukayi ya shige ya zauna abinsa suka maida kofa suka rufe, bimbii kuwa tana samun kulawa yadda ya kamata daga wurin saudat da danta farhan saidai babban tashin hnklin shine bimbii tayi losing memory nata, 2kwata bata iya tuna komai ta manta duk abunda ya faru da ita ta mance ita wace ce,komai koya mata ake hatta mgn da yadda ake cin abinci dama komai, farhan yana mutuqar qoqari wurin kula da bimbii da koya mata abubuwa, shidai abu guda ne ya tsole masa idanu game da bimbii shine wannan jikin dake jikinta ya tsani yaji ance bimbii tana da ciki, sudai sun tsinci bimbii basu san ko tana da aure bane ko bata da aure sudai kawai sun ganta da ciki kuma gashi tayi losing memory nata bata iya tuna komai bare su nemi ta sanar dasu wace ce ita, yau da gobe jikinta ya warware saidai komai nata cikin sanyi take yinsa, bata son mgn shiru shiru, farhan shi kullum mamaki yake wai bimbii yar qarama da ita amma tana da ciki don shi gani yake ya girmi bimbii, tun bimbii bata mgn har ya dage ya soma sanyata mgn, hk yake shiriricewa kullum gabanta yana bata labarai na ban dariya, ya maida bimbii tamkar wata qawarshi itama saita dauke shi aboki kuma dan'uwanta don ita duk zatonta saudat itace ta haifeta, farhan kuma qaninta ne saidai ita mamakinta meyesa ita bata kaisu hasken fata ba, tana yawan yiwa farhan wannan tmbya shi kuma sai ya shashatar da zancen, a kwana a tashi cikin bimbii kullum qara girma yake, tmbyr saudat tayi wai meyesa cikinta ke girma hk, murmushi kawai saudat tayi tace" kar ki damu wataran zaki haifa mn baby ne" shiru tayi bata kuma cewa komai ba,hk rayuwa ta cigaba da tfy, shaquwa sosai ta shiga tsakanin bimbii da farhan sun zama tamkar abokai,wata rana sun je bakin teku kallon ruwa, farhan ya kalli bimbii yace" ki bani wannan zoben na hannunki yana min kyau" kallon zoben bimbii tayi wanda ita bata ce ga yadda akayi zoben ya shiga hannunta ba tace" zoben nan yana min kyau a hannu bani cireshi don ma kaji" dariya yyi yace" toh shikenan ai" prince akbar kuwa tunda sarki abdallah ya sanya shi cikin kurku ya dauke masa kai, kuma yace ayi treating nasa equal da sauran prisoners, babban damuwa prince bimbii ce, shi kansa yana mamakin irin son da yake yiwa bimbii, duk daren duniya sai yyi mafarkinta, hali yake ciki na quncin zuciya da damuwa, tun yana daurewa har abu ya soma cin qarfinsa sai wayar gari akayi prince na aman jini, sarauniya kam kullum tana hanyar wannan kurku kuma kusan duk ranar duniya saita neman wa prince gafara wurin mahaifinsa amma ya kafe kai da fata sai prince ya gane kurensa kafin ya fito dashi kuma sai ya fito duniya ya qaryata soyayyarsa ga wannan baiwa sannan ya nesanta kansa da cikin dake jikinta idan yyi hk kawai shine ze iya yafe masa, wannan abu kuwa shine abu mafi tsauri ga prince akbar, bazai ta6a qaryata soyayyar bimbii ba hkma cikin dake jikinta duk kuwa da cewa besan ko tana raye ko bata raye ba........
Chapter 35 · 0% Book details