← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 59

Sashe 29

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

kuwa tana gama zuba masa tea din ta sunkuyar dakanta qasa sannan taja baya tana jira umarninsa,daga mata hannu yyi alamar ta tafi,rissinar dakanta ta sakeyi sannan ta juya da niyyar fita, mamki. tayi sosai na ganin bimbii tsaye a gefe,wata uwar harara ta aika mata sannan ta fita ranta a mugun 6ace, ubaid yana shigo da bimbii shima ya rissinar dakai,prince ya daga masa hannu ya fice, suna fita dukka ya rage sai bimbii kawai, yana daga zaune idanunsa na kanta ya kasa dauke kai,ita kuma ta kasa gaba ta kasa baya tana tsaye kawai wuri daya, sun dade a hk kanta na qasa ya taso a hnkli ya tako har inda take, matsowa yyi sosai tamkar zasu manne, ita kuwa take zuciyarta ta tsananta dokawa ta soma neman matsawa amma sai yyi saurin take mata kafa, zafi taji sosai ta dago dakanta tana kallonshi, dage mata gira daya yyi, cikin tsantsar dabara da hikima yyi mata jan bazata ta afko kirjinsa ya hannunsa duka ya mata daurin kazar kuku ta yadda bata da damar raba jikinta da nashi, kallonsa take cike da tsoro saita fara masa kuka, murmushi yyi ya dora fuskarsa saman nata ya rufe idanu itama ta rufe idanu suna sauraron bugawar zuciyoyinsu dake bugawa a tare kuma da qarfi, hannunsa ya dora kan kirjinta sannan ya kamo hannunta ya dora kan nashi qirjin, yace" wannan kawai ya tabbatar miki prince bazai iya rayuwa babu ke kusa dashi hkma kema bazaki rayuwa babu ni ba sbd bugawar zuciyarmu daya" shiru tayi tana jinsa amma taqi bude idanu gashi jikinta ya mutu murus bata da qarfin aiwatar da komai, sunkuyawa yyi yasa hannu ya cire mata wannan tsohon zoben dake yatsan hannunta na dama ya sanya mata wani na danyar azurfa daidai hannunta, jin jikinsa yake wani iri ya tabbatar idan har ya cigaba da kasance da bimbii toh ze sake tabargaza, janye jikinsa yyi a hnkli ya juya mata baya, daga mata hannu yyi ya bata izinin tfy batare daya juyo ya kalleta ba don baya son ta fahimci halin dayake ciki, juyawa tayi ta soma tafiya zata fita sai kuma ta jiyo ta dawo da baya, muryarta kawai yaji tace" idan za'a fara soyayya dole sai zuciyoyi biyu sun aminta da juna don cikin soyayya babu izzah bare nuna fin qarfi, idan daka shawarceni ko ka nemi amincewa ta zan fada mk cewa akwai wanda nkso, na bashi zuciyata tunkan yanzu kuma har gobe shi nk so, ka huta lfy" jin maganganunta yyi tamkar saukar ruwan dalma don prince mutum ne mai tsananin kishi musamman ga abunda yakeso, juyawa tayi zata tafi kawai taji ya damqo hannunta, idanunsa jajir dasu yace" soyayyata tana da tsada sosai nikaina na rasa yadda akayi qasqantacciyar baiwa kamarki ta samu zuciyata a araha da rahusa dare daya, toh ki sani duk wanda zaki so a baya na yake ko kin manta nina amshi budurcinki ba wani ba, ki sani soyayyarki itace babban kuskuren dana aikata ga dukkanin wani jini na sarautar burham, wannan irin soyayya ita ake kira haramtacciya a ilahirin wannan masarauta......ki amshi soyayyata ko karki amsa wannan za6in ya rage naki amma ina qara tuna miki ki kwana kullum cikin tuna matsayinki gareni ba kowa bace illah qasqantacciya baiwa mai mini hidima, ina da cikakken iko akanki" kallonsa bimbii tayi sannan tayi murmushi tace" idan da zaka zare kalmar so kabarni matsayin qasqantacciyar baiwa hkn shine farin ciki na" tana gama fadar hk ta juya ta fice daga sashin nasa tabarshi zaune ya dafe kansa dake juya masa, gani yake idan har bimbii taqi aminta da soyayyarshi zuciyarshi zata iya tarwatsewa........babbar baiwa ga sarauniya mar'atussaliha kuwa ummu nana tuni ta miqa zancen zuwan bimbii ga babban prince wurin sarauniya, shiru sauraniya tayi sannan ta dago dakanta ta kalli ummu nana dakanta ke sunkuye tace" ina son ganin azeez" jikin ummu nana har rawa yake ta fita don kiran azeez....azeez shine sarkin hukuncin dauri...............
Chapter 29 · 0% Book details