Sashe 32
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Dukkaninsu kowa yyi shiru ya sunkuyar dakansa qasa, sarauniyya ta kuma kallon azeez cike da tsantsar 6acin rai tace" ka koma ka sanyata cikin dakin ukuba har sai ta bayyana wannan ciki dake jikinta na waye? amma kar kuyi sake wannan sirrin ya fita har wani yaji" rissinar dakai azeez yyi da sauri sannan yaja da baya ya fita, miqewa tayi ta soma zarya ta kasa zaune ta kasa tsaya tana mutuqar shakkar wannan zance yakai ga kunnen sarki abdallah bin jabal, ummu nana dake tsaye gefenta ta dago dakanta tace" ranki ya dade ki bani dama na dauki yarinyar nan kawai na damqata ga masu cinikin bayin dake tfy habasha su maisheta nahiyarta" saurin kallonta sarauniyya tayi sannan tayi shiru sai can ta dago dakanta tace" wannan shawarar ba mai amsuwa bace yanzu sai na gama binciken mamallakin cikin dake cikinta bana fatan ta kasance da wani abu mai kama da jininmu a tare da ita"kada kai ummu nana tayi alamar gamsuwa da mgnr sarauniya mar'atussaliha, azeez yana komawa yasa aka dauki bimbii batare da sun duba halin da take ciki ba yyi umarni a shigar da ita dakin azaba, batare da 6ata lkci ba suka shigar da ita wannan baqin daki suka dorata kan wata kujera aka daddaure mata hannuwa da kafafu, wata shafadediyar bulala suka soma tsula mata, saukar bulalar sau daya kawai ya dauke ganinta na wasu daqiqai kafin ta dawo hayyacinta sun sake zabga mata wata, azeez na gefe yana kallonta sannan yace" ki fadamin cikin dake jikinki na waye" kallonsa tayi da idanunta da suka kumbura sannan ta dauke kanta, kunsan bimbii idan ta sanya taurin kai ko za'a kasheta bata mgn, hk tayi musu shiru su kuwa basu fasa tsala mata wannan mugur bulala mai tfy da fatar jikin mutum ba, kallonta azeez yyi yace" wannan itace tmby ta qarshe dazan kuma miki wannan cikin dake jikinki na waye daga ina kk samo shi, idan baki bani amsa ba toh sai mu gwada miki azabarmu ta gaba" wuta taga sun kunna a wasu dindinan ginin qasa suka sanya wasu qarafa su jajir, kallonta yyi ya nuna mata wadannan qarafa yace" yanzu zaki ji saukar su a jikinki hkn yasa ki bude baki kiyi mgn"sunkuyar dakanta tayi qasa tana jiran su soma aiwatarwa ta rantse ko zasu kasheta basu sanin waye mamallakin cikin dake jikinta, 6angaren ubaid kuwa tunda prince akbar ya bashi umarnin bincike kan guduwar bimbii be dire binciken nasa ko'ina ba sai 6angaren sarauniya sbd hk kawai jikinsa yake bashi kamar dasa hannun sarauniya kan wannan lamarin qila hkne ma yasa ta amshi bimbii a matsayin baiwarta, duk yadda yyi saida yyi yasa israt da khulood suka koma 6angaren sarauniya da hidima sbd yana da alfarma shima a matsayinsa na babban hadimi ga babban prince be samu mtsl ba ummu nana ta karbesu ta hannun ummul shukri sam ita batasan dangantakarsu da bimbii ba, ubaid ya umarcesu su sanya idanu sosai kan dukkanin shige da ficen dake wakana a fadar sarauniyya mar'atussaliha, fitowar israt kenan daga babban kitchen taga shigowar azeez ummu nana tayi masa iso ya shiga don ganawa da sarauniyya, saurin ajiye kwandon tayi ta waiga hagu da damanta taga babu wanda ke ganinta ta lalla6a ta nufi wurin kofar shiga fadar sarauniyya ta tsaya da can nesa ta hango kuyangin bayin dake tsaye bakin kofar shiga fada, dakewa tayi ta qarasa wurin ta shiga cikin jerinsu tare da sunkuyar dakanta qasa, dayan dake qarshe ta wurin kofa tana ganin israt sai tayi zaton tana cikin masu zuwan rana waton bayin dake amsar dutynsu da rana, fita tayi daga jeri ta tafi sbd tana da uxiri mai qarfi, hkn yyiwa israt dadi sosai, wayancewa tayi ta mannu da kofa sosai tayi qasa kamar tana gyara doguwar rigar dake jikinta, karaff, ta jiyo sautin sarauniyya tana fadar wasu zantuttuka masu kama da al'mara,umarnin da saurauniya ta bawa azeez shine kalmar qarshe data iya jiyowa tayi saurin miqewa ta tsaya qam tare da sunkuyar dakanta qasa yadda taga bayin dake kofar sunyi, daidai lkcin taga fitowar azeez, tana tsaye duk ta qagu ta rasa yadda zata fice daga cikin jerin bayin don daman su uku ne kuma idan suka ga ta fita hk zasu zargi wani abu tattare da ita, tana nan tsaye har ummu nana ta fito kallonsu tayi tace" toh kuje yanzu wasu zasu zo" ita sam bata gane israt ba sbd daman su uku ne kuma ukun ta gansu, sauran suka kalli israt amma ganin da sukayi ummu nana batayi mgn game da israt din ba sai suka juya suka soma tfy daya bayan daya kamar yadda al'adar aikin ta nuna musu,israt kuwa qasa tayi da kanta har suka wuce sauran ita kadai saida ta tabbatar sun wuce kuma ummu nana ta koma ciki itama ta janye jiki ta wuce bata tsaya ko'ina ba sai 6angaren prince, hango ubaid tayi dogare a kofar shiga 6angaren prince, tun shigowarta ya ganota be bari ta qaraso ba ya janye jiki yabi ta wata kofa suka hadu, cikin saurin ta damqa masa takardar dake hannunta bata tsaya wata mgn dashi ba sbd tsaro ta juya ta koma bakin aikinta, shima sanya takardar yyi cikin aljihunsa yyi tfyrsa, saida ya samu wuri mafi sirri ya ciro takardar ya duba, abunda ya gani cikin takardar ne yasa shi sake kallon takardar batare da wani 6ata lkci ba ya nufi komawa 6angaren prince, yana shiga lenah ya gani ta sanar dashi prince bazai samu ganinshi ba yana kwance, kallonta yyi yace" kije dai ki fada masa mgnr tana da muhimmaci" kallonsa tayi tare da murmushi tace" ya kk mgn kamar wani baqo ga dokar wannan 6angare, ni kaina bani da daman iya masa ida baida buqatar hkn" shiru ubaid yyi yana sake duba yanayi yaga lkci na neman kwacewa yasan su waye hadiman babban kurku basu da tausayi bare imani tsaf zasu soma gana mata azaba kamar yadda sarauniya ta bada umarni, qara kallon lenah yyi yace" don Allah ki taimaka ki sanar dashi" haushin ya bata ta harareshi tayi juyawarta ta kyaleshi wurin,juyawa yyi da hanxari don yasan komai nacinsa be isa yaga prince yanzu ba, wurin wata bishiyar magarya ya tsaya ya ciro wani uzir ya hura da qarfi, sai ga wata kyakykyawar tsuntsuwa ta taso da gudu daga gabas ta nufo inda yake ta sauka a kafadarsa, saman wannan bishiyar magarya anan shekar wannan tsuntsuwa yake, sautin wannan uzir ne ke kiranta idan har ba tayi nisa ba,wannan tsuntsuwa ta prince akbar ce tana da tarin baiwa da fiqira daya banbanta ta da sauran tsuntsaye ba inda bata shiga a 6angaren prince akbar sannan duk inda ya aikata bata kuskuren isar da saqo, tasan ubaid sosai don shine kawai da prince ke kiranta da qarar uzir, daukanta ubaid yyi ya qulla mata saqon wata qaramar takarda a kafafunta sannan ya dagata sama ya kalli kudu da ita saitin 6angaren prince akbar ya saketa ta tashi firrrrrr, wannan tsuntsuwa bata tsaya ko'ina ba sai 6angaren prince akbar tasauka har tsakiyar gadon kwanansa daga gefensa, idanunsa na rufe hannunsa dafe da saitin zuciyarshi numfashinsa na sauka a hnkli, kansa ne ke tsananta ciwo,kukan wannan tsuntsuwa tasa yaji kusa dashi, bude idanunsa yyi a hnkli ya kalli gefen nasa ya hangota tana kada masa fika fikanta, tashi yyi zaune yana murmushi yasa hannunsa ya dauketa yana shafata, kafarta ya kalla yaga wata qaramar takarda a daure,hannunsa yasa ya cire takarda yana cirewa ta tashi firrrrr ta fice abinta don ta isar da saqonta, warware takardar yyi ya soma karantawa,be qarasa gama karanta abunda ke takardar ba ya sakko daga gadonsa da mugun sauri ya fice, ubaid kuwa na tsaye daga kofa yana ganin fitowarsa ya rufa masa baya, dokinsa ya hau ransa baqinqirin tamkar garwashin wuta, a wani irin sukawane ya dauki hanyar wannan babban kurku ubaid shima yana yana take masa baya, hk suka din ga qetawa ta cikin duwatsu da shuri har suka fara hango ganuwar kurkun, a cikin kurku kuwa azeez jira yake qarafan nan suyi jajir ya soma manna mata a jiki har saita magantu, ita kuwa fuskar nan nata tayi jajir saboda kwanciyar jini, idanunta sun kumbura har sun soma hadewa kamar zasu rufe, jikinta kuwa duk ya farfashe ko a hk suka kyaleta sai tayi jinya maikyan gaske, azeez tsugunawa yyi gabanta ya ciro daya daga cikin qarafan dake wutan yyi jajir tamkar zuga zugi yasa hannunsa yaye mata doguwar rigar dake jikinta yana shirin yin sama da ita ya manna mata qarfe a tsakanin cinyoyinta, tana ganin hk ta rufe idanunta rufe tana shirin taji saukar qarfe amma sai taji akasin hk don kunnenta ne ya jiyo mata sautim muryar da har yau bata mancewa, hancinta kuma ya jiyo mata qamshinsa,wata irin tsawa mai tsananin rikitarwa ya kwasawa azeez dake shirin sauke wannan jan qarfen wutan a tsakanin cinyoyin bimbii, hkn ne ya dakatar da azeez ya jiyo yyi ido hudu da prince, mamakine ya cikashi ya tsaya kawai yana kallon prince akbar, takowa yyi har tsakiyar dakin yasa hannu daya daya shaqo wuyan azeez take rawanin dake kime a kansa ya fadi qasa, duk da tsantsar jarimtar azeez amma kasa kwacewa yyi a hannun prince akbar, dagashi yyi sama da hannu daya, hannunshi daya harde a bayansa fuskar nan tasa tamau ya cillar dashi gefe guda take ya fadi kan wannan qarfen wutan dake yashe gefe yyi wata qara sbd zafin wannan qarfe daya janye fatar jikinsa sauran hadiman kurkun dake wannan daki kuwa duk sunyi 2tsuru suna kallon prince daya dawo musu tamkar wani namijin zaki, ita kanta bimbii duk da halin da take ciki be hanata mamakin yanayi na tsantsar fushi data ga prince ciki ba, qarasawa yyi inda take ya tsuguna 2kwata be dago da kansa ya kalleta ba sbd bayason ganin halin da fuskarta ke ciki, kunce mata hannayenta yyi da qafafunta ya dauketa chak ya juya ya fice da ita hk suka din ga bi ta wadannan dogayen corridorn sbd shi kanshi wannan kurku a jikin dutse aka ginashi, hk suka din ga ratsawa har suka fito wajen kurkun wurin da dawakansu ke daure ya fara dorata saman dokin sannan shima yahau suka zabiri dawakan nasu suka bar wurin da gudu, sosai suke gudu bisa dawakansa cikin jeji ubaid na biye da dokinsu har suka iso wani kyakykyawan kauye, kai tsaye kofar wani gida suka tsaya,prince ya rufe kusan rabin fuskarsa da rawanin dake kansa sbd baya son wani ya shaida shi don wannnan qauye shima mai suna jandun yana cikin yankin masarautarsu ne, wani tsoho ne ya fito sanye da wata akyabba da qaton rawani yana dogara sandarsa a rankwafe yake tfy sbd da tsufa, gemunsa fari ne gashi dogo sosai, dakatawa yyi yana kallonsu, prince dauke yake da bimbii a hannunsa, murmushi yyi wannan tsoho don sai yanzu ya gane prince daya kalli idanunsa sosai sbd fuskarsa rabi rufe take,nuna musu hanya yyi suka shige cikin gdn,ginin gdn dai gini ne irin nasu na larabawa na zamanin baya, ginin jajir irin na jar qasa, cikin wani daki suka shiga mai yalwa sosai ya nunawa princewa wata shimfida ya kwantar da bimbii data jima da shiga coma, wata dattijuwa ta shigo riqe da faranti da qananan cups ta ajiye gaban prince, itace naiha matar wannan tsoho, shi wannan tsoho ya fito ne daga yankin dilham, Allah yyi masa baiwa ta sanin magani sosai, prince akbar shine ya taba ceto rayuwar wannan dattijo mai suna abbas daga tarkon sarkin yankin dilham sarki najash ya bashi mafaka shi da matarsa cikin wannnan dan qauye.....