← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 59

Sashe 23

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ta jima a wurin tana zaune sannan ta tashi ta qarasa 6angaren nasa, tana zuwa bayin dake tsaron kofar suka bata hanya ta shige, tana shiga ta saki wata ajiyar zuciya sbd qamshin sassayan qamshin daya ratsata hk kullum 6angaren nasa yake, mutum ne shi ma'abocin son qamshi, gani tayi komai a gyare yake babu buqatar ta gyara, bude dakin wankan tayi shima ta gansa a shirye komai a jere tsaf tun daga kan sinadaran wanka da 2towels duk anyi hanging nasu neat, fitowa tayi ta sassauke curtains din da suke a kame sannan ta juya ta fice, komawa tayi dakinsu sbd har yanzu lalla6a jikinta kawai take tana aiki mai tsayi zata soma hakki da fitar da numfashi 2sama, kwanciya tayi don qara bawa jikin nata hutu,tunawa tayi da wannan dan akwatin da prince ya bata, sauka tayi a hnkli daga gadon taje ta bude wata drawer ta fito da qaramin akwatin sai daukar idanu yake ta koma bakin gado ta zauna sannan ta fara qoqarin bude dan akwatin, tana budewa taci karo da wasu kyawawan awarwaro masu mutuqar kyau ko ba'a fada mata ba tasan gold ne, qurawa awarwaron idanu tayi tana kallonsu batasan lkcin da murmushi ya su6uce mata ba zira awarwaron a hannunta, tamkar an gwadata don chas suka mata daidai hannunta, sai kallon hannun nata take tamkar wata y'ar qauye, gani tayi kamar awarwaron sun fi qarfin matsayinta amma prince ya bata kyauta, sanya awarwaron gold ai sai jinin sarauta amma ba ita da take baiwa ba,shiko prince awarwaron data sanya ranar a hannunta ne suka birgeshi shiyasa yyi mata wannan kyautar,motsi ta jiyo alamun dake nuni da wani tunkaro dakin nata, saurin zame awarwaron tayi daga hannunta ta maidasu cikin akwatin tayi saurin tashi ta komar dashi cikin drawer din dayake ta dawo ta haye gado ta kwanta, israt da khulood ne suka shigo, zama sukayi kusa da ita suna sake mata sannu, murmushi ta musu kawai, wajejen yamma suka soma jin hayaniyar bayi a farfajiyan 6angaren prince akbar,bude kofa sukayi suma suka fita suka ga ashe prince ne ya dawo, gbdy bayin dake aiki a 6angaren nasa sun jeru sunyi 2sahu suna masa barka da dawowa lfy shi kuma yana daga tsaye a saman dogon corridorn 6angaren nasa,gefensa daman hadiminsa ubaid ne, kallon bayin yake daya bayan daya sannan ya juya ya soma takawa a hnkli da niyyar ya shige 6angarensa hkn yyi daidai da fitorwa su bimbii daga dakin nasu suka shiga sahun bayin, idanunsa ne suka sauka akanta amma sai yyi saurin shigewa 6angaren nasa duk da idanun nasa yana son qare mata kallo, ubaid ne yyiwa bayin mgn sannan ya sallamesu kowa ya koma bakin aikinsa, bimbii wucewa tayi babban kitchen ta hada masa abun sha na zaitun ta dauka ta nufi 6angaren nasa, tana zuwa kofar ta bude ta shiga, samunsa tayi kishingid'e a jikin wata kujera yana duba wasu maps, ganin shigowarta ne yasa yabar abunda yake ya dago dakansa ya zuba mata lumsassun idanunsa yana kallonta, kallon da prince din ke mata ne yasa ta tsarguwa sosai amma dai ta daure ta tako a hnkli ta rissinar dakanta sannan ta ajiye farantin dake hannunta, sunkuyawa tayi ta soma tsiyaya masa ruwan zaitun din a qaramin cup ta dauke tare da sunkuyar dakanta qasa tasa hannunta dukka ta miqa masa cup din, saida ya jima be amsa ba kawai ya qura mata idanu yana kallonta, dago da kanta tayi ta kalleshi idanunsu suka sarqe da juna, hannunsa ya miqa ya amshi cup din dake hannunta ya qara kwantar dakansa a jikin kujerar yana sipping ruwan zaitun din yana cigaba da kallonta, itace taji kunya ta sunkuyar dakanta qasa tana kallon floor, murmushi yyi yace" ya jikin naki" dago da kanta tayi suka sake hada idanu dashi sai kuma duk ta duburbuce sbd idanunsa dake neman kayar da ita, tace" d...a..sauqi" be kuma cewa komai ba ya miqe yabar wurin hkn ya ankarar da ita lkcin wankansa yyi, wucewa tayi saurin yi cikin dakin wankan ta soma hada ruwan wanka yadda ta saba sannan ta fito, ganinsa tayi sanye da wata rigar wanka fara qal yana zaune, tana fitowa ta rissinar dakanta a gabansa, bece mata komai ba ya miqe ya shige, ita kuma ta tsaya daga bakin kofa, tana nan tsaye taji alarm alamar dan sarkin na buqatarta cikin dakin wankan, shiga tayi da sauri ta tarar dashi a cikin kwarmin wanka cikin ruwan dake turiri, saman ruwan duk kumfa, hannunta tasa a kafadunsa ta soma masa tausa a hnkli, shi kuwa idanunsa a lumshe suke yana amsar saqon dake shiga jikinsa ta wata siga daban dashi kadai yabarwa kansa sani,daga mata hannu yyi tabar tausan ta soma masa wankin gashi tana gamawa ta fice ta kyaleshi yyi wankan, tadan jima sannan ta kuma jin alarm ta koma ciki, ruwa ta debo a wani qaramin bahun tazo gabansa ta ajiye ta kuma miqewa taje ta dauko sinadaran wankin qafa ta zuba a ruwan qaramin bahun, sannan ta riqo kafafunsa da suke sanye cikin takalmin wanka ta cire takalmin wankan ta sanya kafafun nasa cikin ruwa, kallon kafafun nasa take da suke jajir dasu tamkar tumatir ga laushi da santsi tamkar ta jarirai sai ka rantse baya taka qasa dasu, itakam bata ga abun wankewa a wadannan kafafu ba idan badai kawai izzah da hutu ba, riqo kafar tasa tayi tamkar wacce ta riqo gold cike da taka tsantsan ta soma wanke masa, duk abunda shi kuwa idanunsa a rufe ma suke tamkar mai bacci har ta gama masa wankin kafar, fita tayi tana jiran fitowarsa, ta jima da fita kafin ya fito sanye da wasu kaya masu kalar ruwan kwai, jikinsu tamkar na mage, gashin kansa kuwa walwali kawai yake da sheqi, takalmin kafarsa ma mai jikin mage, kai tsaye royal bed nasa ya haye ya kwanta, ita kuwa dayake ba wata cikakkiyar lafiyar jiki ne da ita ba tuni ta soma dan jin jiri sbd dan aikin da tayi, so kawai take ya bata izinin tfy taga yyi mata shiru hkn ya tabbatar mata bata gama aikinta ba so yake ta sanyashi yyi bacci, a hnkli ta qarasa kusurwar da royal bed nasa yake itama tahau gadon, yana jin ta hawo gadon ya dago da kansa ya daga mata hannu, alamar baya buqatar tausa, dadi taji har hkn ya bayyana a fuskarta ta soma qoqarin sauka da sauri, saurin riqo hannunta yyi ya kalli tsakiyar idanunta yace"kimin rawa ita nakeso" kallonsa tayi tamkar kuka, sakinta hannunta yyi ya tashi ya sauka daga kan gadon ya koma kan wata kujera,ita kuwa bimbii bata da karfin jiki tayaya zatayi rawa, tsayawa tayi sai kuma ta fara rawar 2kadan, shi kuma yabita da kallo tana cikin rawar kawai jiri ya debeta ta tafi luuuu, sai ganinsa tayi kawai ya tareta da hannu guda ta fada jikinsa, kallon fuskarsa take 2dishi shima yana kallonta, dagata yyi chak ya kwantar da ita kan royal bed dinsa shima ya kwanta daga gefenta,kunsan kowanne qabila suna da techniques nasu a gargajiyance, idanunta ya kalla kawai yasan jiri ne ya kwasheta, ba zato bimbii taji kyakykyawan bakin dan sarkin bisa nata, duk da halin da take ciki amma zuciyarta ta soma dokawa 2uku ta qwalalo manyan idanunta waje cike da razana..........kundai son halin bimbii taku😉....

Littafin nan na siyarwa ne, idan kina da buqata ki tura #300 ta wannan acct....0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screesht na payment ta whasapp through wannan layin....07041195806......

Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

19

*Forbidden love*.....the beginnig of my story.....
Chapter 23 · 0% Book details