Sashe 28
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bangaren sarauniyya mar'atussaliha yana da girma sosai kuma suma bayin dake 6angaren nata wajensu yana da yalwa sosai,bimbii bata samu daki ita kadai ba yadda take a 6angaren prince,hadata akayi da wasu bayi su hudu ita ta zama ta biyar, neman wuri tayi daga can gefen dakin ta ajiye kayanta, yanayin bayin data hadu dasu anan ba kamar su khulood bane ta fahimci akwai tsugumi da baqin ciki a lamarinsu sbd tunda ta aka kawota dakin ba wacce ta mata kallon arziki,ummu nana ta sanar da ita aikinta shine baiwa furannin dake 6angaren gbdy ruwa safe da yamma sannan da tatso nonon raqumi, washegari da sanyin safiya bimbii ta tashi ta bawa furanni ruwa sannan ta dauki kwarya ta tafi tatso nonon raqumi anan suka hadu dasu khulood suna ganinta suka taho da gudu suka rumgumeta, israt tace" bimbii daman arzikinki muke ci jiya kina tfy lenah ta dawo dakin tayi mana korar wulaqanci muka koma dakin hadaka yanzu mu takwas ne a dakin da muke" murmushi bimbii tayi ta janyo hannun israt tace" karki damu komai na duniya dan hkr ne wani lkcin baka cimma kyakykyawar qaddararka kai tsaye har saika qetare'''' manyan qalubale na rayuwa" murmushi sukayi gbdy, khulood tace" wannan hk yake" sunkuyawa sukayi suka soma tsatsar nonon raqumi duk suka cika kwaryoyinsu sannan suka dora bisa kawunansu suna tafe suna hira har suka iso hanyar da zasu rabu su khulood suka wuce 6angarensu itama ta wuce nata 6angaren, prince akbar kuwa ranar kasa runtsawa yyi sai tunani yake dalilin dayasa sarauniyya ta nemi ya bata bimbii har yanzu ya kasa fahimtar manufarta saidai yana da tabbaci tana da manufa nayin hkn don mace ce mai mutuqar hange da fahimtar lamura kuma gata da tarin hikima, kiran ubaid yyi ya shigo ya rissinar dakai a gabansa cike da ladabi,dago dakansa yyi dake jingine bisa wata tattausan kujera ta alfarma ya kalli ubaid dakansa ke sunkuye, yace" kana da wata fahimta kan manufar sarauniyya na amsar wannan baiwa" shiru ubaid yyi na y'an daqiqai yana tunani sannan ya dago dakansa ya kalli babban prince yace" ranka ya dade bani da wata fahimta kan hkn saidai abunda ya bani mamaki shine me yasa sarauniyya ta kira bimbii har gabanta sannan tace ta tafi batare data furta komai ba sannan ta maida dubanta kan idaniyarka, abunda na fahima anan shine akwai wani sirri data gani cikin kwayar idanunka bisa al'muran wannan baiwa taka, ka gafarceni ranka ya dade da wannan hasashe nawa" shiru prince yyi domin amsar ubaid kadai ta haska masa manufar sarauniyya mar'atussaliha,wato ta fahimci sirrin zuciyar prince game da bimbii da take qasqantacciyar baiwarsa, kallon da prince ke yiwa bimbii kawai ya ankarar da sarauniyya cewa d'an nata yana da wani feeling kan wannan baiwa, abunda yasata aikata hkn shine tana gudun faruwar wani babban al'amari zuwa gaba mutuqar bimbii ta cigaba da kasancewa da prince, hkn da tayi na amshe bimbii daga wurinsa tana tunanin shine mafita, cikin kwana biyu kacal prince ya gama jigatuwa da kewar bimbii, hknne yasa ya buqaci ubaid ya kawo masa su israt yana son ganinsu, ubaid yaje ya taho dasu israt da jikinsu har rawa yake sbd tsorota da sukayi na jin wai babban prince nason ganinsu sai sukayi zaton ko wani laifin sukayi, suna shiga bangaren prince suka same shi a zaune kan wata kujerar mai ruwan zinare yana rubuta wata wasiqa,zubewa sukayi bisa guiwowinsu duk suka rissinar da kawunansu, saida ya dauki dogon lkci sannan ya dago da kansa ya kallesu, miqawa khulood wannan takarda yyi yace" gashi ina son ku miqa wannan takardar ga yar'uwarku, idan har kk bari wani yaji ko yaga wannan takarda toh hukunci mai tsauri na tanadar muku" qara sunkuyar dakai sukayi, khulood tasa hannu biyu ta amshi takardar da take nannad'e cikin wani siririn abu tamkar alqalami, yana miqa ya daga musu hannu suka miqe da sauri suka fice, ranar basu hadu da bimbii ba don hk da dare suka fita suka nufi bangaren sarauniyya, masu tsaron 6angaren sarauniyya ba kowanne bawa suke bari ya shiga 6angaren ba saidai idan a wurin kk aiki ko kuma kana hidimtawa daya daga cikin iyalan sarki,hk suka hana su khulood shiga 6angaren, qin tfy sukayi suka koma gefe suna ta tsaye ko zasu gano fitowar bimbii amma shiru, wani wuri suka samu suka tona rami suka binne takardar sbd basu son su koma 6angarensu da ita tsautsayi yasa wani ya gani, su kansu basu san meke rubuce cikin wasiqar ba, washegari da sanyin sfy suka fito suka nufi wurin da suka binne wasiqar suka tono wurin suka dauki wasiqar suka nufi 6angaren sarauniyya suka tsaya bakin kofa suna jiran fitowar bimbii, ita kuwa bimbii tana ciki ta bawa furanni ruwa tana gamawa ta dauki kwaryarta ta fito don tatso nonon raqumi, tana fitowa ta miqe hanya sai kawai ganinsu khulood tayi sun sha gabanta dukkaninsu a dan rikice, kallonsu tayi da mamaki tace"lfy kk kuwa" basu bata amsa ba sai 2waige suke kamar wasu marasa gsky saida suka tabbatar babu kowa wurin sannan israt ta sanya hannu cikin rigarta ta ciro saqon babban prince ta bawa bimbii, sannan suka sanar da ita gargadin daya musu,shiru bimbii tayi tana kallon wasiqar, khulood ta sake waigawa taga ba kowa ta matso kusa da bimbii tace" kiyi sauri ki 6oye ki tabbatar babu wanda yaga wannan saqo wurinki" sauri bimbii tayi ta chusa wasiqar cikin rigarta sannan ta rabu dasu khulood don su ranar qorama suka nufa, ranar bata samu lkcin kanta ba bare ta bud'a wasiqar taga abunda ta qunsa sai da dare data koma dakinsu ta saci jiki ta fito farfajiyar 6angaren ta nemi wurin da babu yalwar kilmawar bayi ta zauna gindin wata bishiyar dabino ta ciro wannan wasiqa ta bud'e, yyi rubutun ne da haruffan larabci, dayake itama tasan baqi hk ta soma karanta wasiqa, gabanta ne ya soma dokawa 2gudu lkcin data soma ganin kalmomin da prince yyi amfani dasu wurin rubutun wasiqar, ba wasu kalmomi bane sai tsantsar yabo da kuma mutunta darensu na farko, yyi mata gdy da kyautar budurcin da tayi masa sannan qarshen wasiqar kalmomi ne dake bayyana kewarta daya yyi cikin wadannan kwanaki sai kuma wasu zafafa kalmomi na soyayya daya soma furta mata karo na farko,bata qarashe karanta wasiqar ba tayi saurin rufe takardar jikinta na rawa ta dafe qirjinta dayake bugawa tamkar ze fashe sbd tsananin tsoro da razana da tayi, kallon takardar take tana tantaman anya prince ne dakansa ya rubuta wannan wasiqa, addu'a ta somayi cikin ranta Allah yasa su israt basu bud'a wannan wasiqar ba, duqunqune takardar tayi ta kutsirtsirata mitsi mitsi ta din ga tfy da nisa tana cillar da kowanne 6angare na takarda wuri daban daban sbd tsantsar tsaro, jiki a sanyaye ta koma dakin nasu ta tarar da abokan zaman dakin nata suna hirarsu ko kallonta ba wacce tayi itama bata sanya musu baki ba sbd akwai abu mafi girma dake dawainiyya da ruhi hade da gangar jikinta don hk bata da lkcinsu, samun wuri tayi ta kwanta, tana rufe idanunta kyakykyawar fuskar prince akbar zata soma mata gizo, miqewa tayi da sauri ta soma mutsitstsike idanunta,kunnuwanta taji tamkar muryarsa yana furta mata wadannan zafafan kalmomi da suka rudata suka gigita tunaninta baki daya,hannu tasa ta soma toshe kunnuwanta, duk bayin dake dakin suka soma kallonta suna tunanin ko ta samu matsalar kwakwalwa ne,6angaren prince kuwa ya rasa kansa sosai, be ta6a tunanin tarkon son wata diya mace zeyi masa irin wannan kamun ba amma sai gashi dare daya ya fada soyayyar qasqantacciya baiwa baqar fata da sun bambamta a komai, tun daga kan nahiya, asali,tushe har ma da kalar fata,riqe kansa yyi kawai ya rasa meke faruwa dashi, jin zuciyarsa yake tamkar zata zage sbd wani irin bugawa da take da qarfi, ga kewar bimbii dake azabtar da gangar jikinsa har ma da ruhinsa,miqewa yyi da sauri ya kira ubaid, kallon ubaid yyi yace" ina son ganin bimbii a wannan dare kasan duk yadda kayi ka kawo min ita" kallonsa ubaid yyi a nutse cike da girmamawa yace"an gama ranka ya dade" fita yyi da sauri, israt ya samu cikin sirri ya buqaci taje 6angaren sarauniyya ta fito da bimbii, sanar dashi tayi bata da damar shiga yankin sarauniya matsayinta na qasqantacciyar baiwa, wani qaramin gate pass ya ciro daga aljihunsa ya bata yace"ki nunawa bayin dake tsaron kofar wannan zasu bude miki kofa ki shiga" amsar gate pass din israt tayi ta tafi da sauri ta nufi yankin sarauniya tana zuwa ta nunawa masu tsaron kofa wannan gate pass suka bata hanya ta shige, bata sha wahala ba ta gane dakin da bimbii take, tana shiga dakin taga kusan dukkanin bayin dake dakin sunyi bacci sai bimbii kawai dake zaune ita kadai kamar wata mara gata, bimbii kamar ance ta kalli kofa taga israt tsaye tana kallonta,tasowa tayi da sauri tazo wurin israt, jan hannunta israt tayi suka fice daga dakin, israt ta kalleta tace" meke damunki hk bimbii yanayinki ya nuna kina tattare da damuwa" bimbii tayi shiru sai kuma ta kalli israt tace" babu komai" kallonta israt tayi kadan sannan ta kawar da waccar mgnr tace" babban hadimin babban prince ubaid shike son ganinki yanzu" dafe kirji bimbii tayi ta kalli israt tace" israt me kk zaton zemin" israt tace" gsky ban da sani kan hkn amma ga dukkanin alamu prince ne dakansa ke buqatar ganinki" take gaban bimbii ya yanke ya fadi, ta soma ja da baya, israt tsayawa tayi tana kallonta cike da mamaki,hannunta tasa ta riqo hannunta tace" akwai abunda ke faruwa ne tsakaninki da prince" girgixa kai tayi da sauri alamar aa, jan hannunta israt tayi suka soma tfy har suka fice daga yankin sarauniyya suka din ga wuce kusurwa kusurwa har suka qarasa inda ubaid ke jiransu, yana ganinsu yyi murmushi yace israt ta tafi sannan ya kalli bimbii yace" babban prince nada buqatar ganinki" juyawa yyi ita kuma ta soma bin bayansa cike da sanyin ciki kamar kaxar da kwai ya fashewa a ciki, gabanta kuma sai cigaba da faduwa yake har suka qarasa 6angaren prince, suna shiga suka tarar dashi zaune lenah na tsiyaya masa green tea, shigowarsu ne yasa shi dago da lumsassun idanunsa ya saukesu kan bimbii,lenah