Sashe 2
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Kwanaki sun shud'e anyi dare dayawa duk sun shud'e amma sukam suna doron ruwan teku suna tfy rabonsu da doron qasa sun jima, duk cikin wad'annan bayi babu wanda yasan qasar da suka nufa abunda suka sani kawai an kamosu daga qasashensu an sakosu cikin jirgi a matsayin kamammun bayi,tunda bimbii ta soma zazza6i wannan saurayin d'an kabilar igbo shike kula da ita yana tausayin bimbii sosai sbd gsky tana da qarancin shekaru, sanyi na ratsa dukkanin sassan jikinsu amma saidai su takure wuri d'aya don babu abun rufa, shi kuwa wannan saurayin daga shi sai wata yar qaramar riga don ya cire rigan dake da kauri a jikinsa ya rufawa bimbii, jirgin nasu ne ya soma tangal tangal tamkar ze kifa kowa cikin wannan jirginsa cikinsa ya d'uri ruwa sbd tsoro, riqe hannun bimbii yyi qam don yaga gbdy ta rikice cikin ikon Allah jirgin ya koma yadda yake normal, kowa ya soma ajiyar zuciya, bimbii a hnkli ta janye hannunta, kallonsa tayi taga alamun shima dai yana jin sanyi amma ya gwammace ya rufa mata jacket dinsa, hannu tasa ta cire rigan daya rufa mata ta rufa masa, kallonta yyi yana qoqarin cire rigan tayi saurin dakatar dashi da hannunta cikin harshen fillanci tace" bana jin sanyi ka sanya kawai" be fahimci mai take fad'I ba amma ya fuskanci abunda takeson yyi, murmushi yyi mata yace"nagode" saurin dago da kanta tayi tana qare masa kallo don tabbas idan har ba kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba kamar hausa taji yyi,tana jin hausa itama 2kad'an don tana fita kasuwa tallan nono, tace" kana jin hausa ne" murmushi ya kuma mata a karo na biyu yace" ehh,amma ni igbo ne daga Abia nk" tace" me sunanka" yace" obinnah" yace"ke me sunanki" tace" bimbii" ya qara nanata sunan nata yace" daga ina kk" tace" ruganmu tana kudu da qauyen lamirde cikin garin gombe" kad'a mata kai yyi alamun ya gamsu, daga shi har ita babu wanda hausar tasa ke fita daidai duk tata suke a hausar amma hk suke dan mgn, bimbii bata da yawan zance amma saita samu kanta da sakewa dashi, cikin tsakiyar daren goma sha hudu jirginsu ya samu isa matattarar tsayawar jiragen ruwa wato Brandford port dake Amsterdam,tunda suka fito daga jirgin nan suke 2kalle kana ganinsu kaga k'auyawa, dole kam suyi k'auyanci don kaf nahiyarmu ta africa ba irin wannan port din, turawan dake kai kawo a wannan port kuwa kallonsu suke tamkar kashi sbd tsabar racism, dukkaninsu babu wanda ze iya fad'ar sunan qasar da suke amma yanayin kalar fatar mutanen qasar ya tabbatar musu qasa masu jan kunne ce wato lardin turawa suke, falmata d'aya da cikin yan'uwan bimbii da aka rabasu tun a jirgi ta saci jiki daga cikin tasu tawagar ta shigo cikin tawagar su bimbii, riqo hannun bimbii tayi tana kuka tace" bimbii zamu rabu gbdy kin ga zasu kuma shigar damu wani jirgin bamu san inda zasu kaimu ba, mudai tamu qaddarar kenan sun rabamu da danginmu sun shigo damu duniya,bimbii ki kula da kanki sannan ki saukar da kanki kiyi duk abunda suka sanyaki don basu da imani zasu iya kashe mutum" kuka suke sosai suna qanqame da juna har lkcin da baturan dake jagorantar tawagarsu ya ankara babu mace daya cikin yan matan nan, suna rumgume da juna suna kuka suka ji an finciko falmata batare da 6ata lkci ba ya sauke mata tagwayen mari a fuska sannan ya jata ya koma da ita cikin tawagarsu, had'esu turawan sukayi suka zargesu da igiya sannan suka tasa qeyarsu suka shige wani jirgin dasu,suna tfy suna waiwayen yar'uwarsu itako bimbii kuka take sosai tana kallonsu har suka shige jirgin,obinnah dake kusa da ita ne ya soma rarrashinta, itama tana cikin alhinin rabuwa da yan'uwanta wani daga cikin masu kula dasu yazo yace ta biyoshi, batasan meze mata ba ita dai kawai batare da gardama ba ta miqe tabi bayansa, obinnah dake gefenta yyi saurin miqewa ze rakata mutumin ya daka masa tsawa dole ya koma ya zauna ita kuwa tabi bayansa suka qarasa wurin wani tsohon jirgin ruwa dake gefen port din, nuna mata kofar jirgin yyi yace ta shiga, shiga tayi shima yabi bayanta, suna shiga gabanta ya yanke ya fad'I don lura tayi jirgin abandon one ne ba kowa cikinsa sai tarin shirgi, bata qarasa rikicewa ba saida taga ya soma zame wandon dake jikinsa, take jikinta ya soma rawa tamkar mazari ta soma ja da baya cike da tsantsar rudewa, murmushi yyi lkcin daya gama zame dukkanin tufafin dake jikinsa ya kalleta yaga yadda ta rufe idanunta ruf sai makyarkyata jikinta yake ta durqushe a wurin tare da daga hannayenta dukka ta soma masa mgn da harshen fillanci tace" ka yiwa Allah ka yiwa annabinsa ka kyaleni karka ketamin haddi niba kafira bace" cikin kuka take roqonsa duk fuskarta tayi 2sha6e da hawaye, shi kuwa tumuqin arne besan ma abunda take fad'I ba don ba jin yarenta yake ba, shima baqar fata ne amma yyi kala da irin mutanen kenya din nan baqine qirin tamkar gawayi asalin african man, matsowa kusa da ita tana ja da baya har takai qarshen jirgin yana biye da ita da murmushin qeta a fuskarsa, hannu yasa yana shirin kamota aka doko kofar jirgin, wannan asalin balaraben ne daya amsheta daga wurin baturen nan, kallon mutumin yyi ransa a mugun 6ace ya soma zaqinsa cikin harshen turanci yace" kai wawa ne so kk kamin asara, kasan dalilin dayasa na amsheta sbd daka ganinta kasan danyar budurwa ce kuma kudin virgins ko wurin saidawa daban yake, shine dan kai dan iskane kk neman mini asara daman all those africans are bunch of animals,bauta ita tafi dacewa daku" hk balaraben nan ya din ga masifa, shi kuwa sai qoqarin sanya wandonsa yake,bimbii kuwa na daga gefe sai ajiyar zuciya take, qeyarta dan balaraben ya tasa ya komar da ita cikin tawagar sauran bayin, obinnah na ganinta ya soma tmbyrta ko sun mata wani abunne ta kada masa kai alamar basu mata komai ba,suna nan yashe a gefen ruwa tamkar ba mutane ba sanyi sai busasu yake sai wurin asuba suka ga tsayawar wani jirgi, yana sauke fasinjojin cikinsa ya soma deban wasu fasinjojin, hk akazo aka tasa qeyarsu suka shige wannan jirgi,kwanansu biyu suna tfy kafin suka soma shiga lardin larabawa, jirginsu ya tsaya ne qasar KUWAIT..... Abdullah bin faisal International port, tun saukarsu daga jirgi wasu zungura zunguran motoci suka soma dibansu kai tsaye kasuwar cinikin bayi aka wuce dasu, yadda ake cin kasuwa saida tumakai ko dawakai hk ake cin kasuwar saida bayi, manya manya keji akeyi ake zuba bayin ciki, suma hk aka zubasu cikin keji, farashin bayin hawan hawa ne wani kudinsa yafi na wani, manya masu kudi da jinin sarauta da masu mulki sukan siye bayin dayawa sukaisu muhallinsu suna musu kowacce kalar bauta amma yawanci jinin sarauta basu daukan baqar fata sai larabawa kalar fatarsu, masu ma'aikatu da gonaki suke siyen baqar fata sukaisu suna musu aiki amma masu daukar boyi boyin gd ma sunyi son larabawa kalar fatarsu suna mugun kyamar baqar fata musumman na africa,bimbii an hadata keji daya ne da wasu yan'mata amma dukkaninsu larabawa ne sukansu kallonta suke suna mamakin wai daman a qasashen baqar fata ma akwai mata masu kyau kamar bimbii, gani sukayi gashin kanta yafi nasu tsawo gata duk cikinsu ta fisu kyau da cikakken diri irinna mata saidai kawai su nuna mata hasken fata, mutanen sai 2zirga suke suna siyen bayin da suka musu,kowanne bawa so yake a siyesa ko Allah zesa yyi dace da mutanen kwarai su masa riqon arziqi,wata balarabiya itama tazo duba bayi kallon daya zaka mata kasan ba daga gdn talauci take ba, balaraben dake dasu bimbii ne yyi saurin tararta ya kawota wurin kejin dasu bimbii suke wai ta duba koda wacce tayi mata, kallonsu take daya bayan daya tana duddubasu tamkar wacce zata siyi akuya, idanunta ne ya tsaya kan bimbii ta nuna bimbii da hannu tace" wannan baqar fata ce koh" balaraben yace" ehh,amma tana da cikakken lfy ba zaki samu mtsl da ita ba" sake kallon bimbii tayi tace masa ya fito da bimbii aikuwa ya bude kejin ya fito da bimbii, batare da bata lokaci ba tayi cinikinta ta biya suka bata certificates of ownership na bimbii har wurin motarta balaraben ya rakata ya budewa bimbii boot din mota ta shiga aka rufeta sannan matar ta shige gdn baya drivernta yaja motar suka wuce, bimbii na bayan boot din motar tamkar akuya tana rakube har suka iso gdnsu sannan aka budeta ta fito, gdn qaramin bungalor ne mai kyau da tsari ga furanni ta ko'ina kunsan larabawa da son hutawa, tsagaya matar ta somayi da bimbii tana nuna mata ayyukan da yake nata ciki har da baiwa wadannan furannin ruwa da kula dasu, duk aikin nata na wajene be danganci cikin bedroms,kitchen ko cikin parlourn ba don wannan aiki daya shafi cimmarsu ko kula da wurin kwanansu basu amincewa da baqi yyi musu ba suna da kyankyamin baqin mutum sosai duk wannan ayyukan na cikin gd balarabiya yar'uwarsu suke dauka, wani qaramin daki aka baiwa bimbii, kullum bimbii tunkan kowa ya tashi take tashi tayi dukkanin aikin da matar nan ta yanka mata, batasan sunan wannan balarabiya ba amma taji ma'aikatan gdn na kiranta ennah, tana da tsauri sosai batason wasa ko sakaci da aiki, tana yara biyu dukkaninsu maza ne amma kowanne da gdnsa basu zaune tare da ita, bawai iyali ne dasu ba amma kowa yana zaune shi kadai a gdnsa saidai duk weekend suzo su gaishe su yini sai dare suke tfy, ennah tana son wadannan yaran nata sosai da zayeed da maheer, maheer shine qarami atleast bazai gaza shekaru ashirin da uku ba sai zayeed mai shekaru ashirin da shida, yau weekend tun sanyin safiya bimbii ta gama aikinta, zuwan bimbii gdn yasa furanni dake gdn suka soma kyau da fitar da kyawawan furanni masu kala sannan tana yankesu tana saitasu tana cire ciyayin dake fitowa qasansu suna hanasu girma, kullum ennah na kallon yadda bimbii ke gyaran furannin ta windown dakinta, ita kanta ta yaba da aikin bimbii, kullum tana aikinta tana waqarta cikin harshen fillanci,tun tazo gdn bata taba shiga cikin wannan bungalor na masu gdn ba, ranar wata asabar maheer ya shigo gdn, tsayawa yyi yana kallon yadda bimbii ke gyaran furanni fuskarsa sam babu annuri don shi be ta6a tsammani ennah zata kawo musu baqar fata gd ba, qarasa yyi inda bimbii ke aikinta yasa hannu ya janyo mayafin dake rufe da gashin kanta ya janyo dogon gashin kanta, cike da tsoro ta dago a idanunta tana kallonshi tace" malam lfy me na mk" cikin harshen fillanci take masa mgn aikuwa ya watsa mata mari saida shatar hannunsa suka fito a fuskarta ya bala'i cikin harshen larabci wai uban waye ya kawo musu baqar fata gdnsu, muryarsa ennah taji tayi saurin fitowa ta qaraso wurin,kamashi tayi suka shige bungalor ita kuwa bimbii hawayene ya cika mata idanu kawai ganin yadda ake wulaqanta bil'adama toh shi baqar fata ba Allah ne ya halicceshi ba, itama bimbii indai a kalar fata ne tana da haske idan anan africa ne zamu iya kiranta da fara amma su kallo daya suke mata suke gane ba balarabiya bace duk da tsantsar kyawun halittarta.....