← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 59

Sashe 36

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screesht na payment ta whatsapp ta wannan layi...07041195806....

Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔

Written By Bintuu Seer

29

*Only one person fill my heart*.....You are the reason of my breathing,I love you so much dear💕💕

Yau bimbii na kwance ita kadai a daki sbd tun safe take jin jikinta wani iri babu dadi amma tana ta daurewa batason ummu farhan ta gane halin da take ciki, ummu farhan ce ta shigo dakin hannunsa riqe da wani qaramin cup da zuma a ciki, bimbii na ganinta tayi saurin miqewa zaune, murmushi ummu farhan tayi ta miqa mata qaramin cup din dake hannunta tace" ki shanye zuma ce tana cike da sirrika na magunguna 2kala musamman wurin mace mai juna biyu" murmushi bimbii tayi tasa hannu ta amshi cup din ta soma shan zumar har ta shanye, da dare lkcin cin abincin dare duk suna zazzaune kan wata qatuwar darduma duk sun harde kafafunsu suna cin abinci, farhan ya kalli mahaifinsa abeed yace" abu itama andal akaita mkrt mn" dago dakai abeed yyi ya kalli 6angaren da bimbii ke zaune yace" andal wai kina son mkrt" murmushi bimbii tayi tace" ehh abu ina so" kallonta farhan yyi ya kalli cikinta daya dan turo sosai ya ta6e baki ya cigaba da cin abincinsa, ummu farhan ta kalli abeed tace" amma dai ba yanzu ba saita haihu tukunna" farhan ya dago ya kalli bimbii yace" nikam ban ta6a ganin yarinya qarama kamar ki da ciki ba" iyayen nasa ne sukayi saurin kallonshi tare da harararsa sai yyi saurin sunkuyar dakansa qasa, shima kawai zancen ne ya kubce masa sbd ya tsani ganin wannan ciki a jikin bimbii da suke kira da andal, bimbii kuwa tsuru tayi tana son tuna wani abu amma kwakwalwarta ta toshe duk wata kafa ta tuna mata abunda ya faru da ita a baya, ummu farhan ce ta dafata da murmushi a saman fuskarta tace" andal ko bacci kkji ne" daga mata kai tayi alamar ehh, kamo hannunta tayi suka miqe suka nufi dakin kwanan bimbii, gyara mata wurin kwanciya tayi tace" ki kwanta saida safe" kallonta bimbii tayi tace" Allah ya bamu alheri" murmushi tayi ta sunkuya ta shafa kan bimbii tace" ameen summa ameen"bimbii cikin dare ta tashi zaune, bayanta taji ya riqe qam ga wani irin ciwo da mararta take mata duk ta hada gumi, hk ta din ga fama har asuba tayi ta soma jin motsin abeed da farhan zasu fita masallaci, tana cikin wannan hali ummu farhan ta shigo dakin, cikin sauri ta qarasa wurin da bimbii ke durqushe riqe da mararta, tace" andal mene ke damunki,kiyimin mgn" bimbii ba bakin mgn sai idanu kawai take bin ummu farhan dashi, ummu farhan kam tasan ba haihuwa bane sbd cikin nata bekai mizanin haihuwa ba saidai idan wani ciwon ne daban, ruwan zaitun da zuma ta bata ta sha, suna cikin hk su abeed suka dawo, farhan ne ya shigo dakin ya tarar da abunda ke faruwa, shigowa yyi cikin dakin a rude yana kiran suna bimbii, tana jinsa amma ba bakin amsawa, juyawa yyi ya fita da sauri ya sanarwa mahaifinsa, abeed ya shigo shima cikin dakin, farhan ya kalli mahaifinsa yace" ina ganin kawai mu wuce da ita asibiti" kada kai abeed yyi alamar hk za'ayi, cikin wannan safiyya farhan da abeed suka fita, suna fita suka tarar da wani tsoho yana jan keken dokinsa, alfarma abeed ya roqeshi kan ya amince ya fitar dasu bakin babban hanya ko zasu samu abun hawa zuwa asibiti,wannan majanyin keken doki kuwa ya amince suka fito da bimbii suka sanyata ciki tare ummu farhan mai keken dokin yaja suka tafi, sunyi tfy mai nisan gaske kafin suka isa bakin hanyar motoci ke wucewa, dakatawa sukayi har su abeed suka qaraso sannan suka tsayar da wata mota suka shige, daidai king faisal specialist hospital motar tasu ta tsaya suka fito dukkaninsu har da bimbii, suna shiga hospital din wadanda ke yawo da gadon daukar marasa lfy suka dauki bimbii suka shige da ita,wata nurse ta wuce da gudu zuwa office din doctorn dake kula da wannan 6angare ta sanar masa an kawo wata patient mai juna biyu dake buqatar taimakon gaggawa, doctorn be dago kai ya kalleta ba saida ya gama danne dannensa a laptop din dake gabansa sannan ya dago dakansa yace" kije gani nan zuwa" juyawa tayi ta fita sbd idan da sabo duk sun saba da halin DR.MAHEER mugun dan I dnt care akan patients, hknlinsa kwance ya miqe ya fita daga office din nasa, farhan da abeed na ganin fitowarsa suka nufo shi da sauri, be sauraresu ba yyi wucewarsa cikin dakin da bimbii ke kwance,qarasawa yyi bakin gadon da take yana kallon ruwan drift din dake shiga jikinta sannan ya maida dubansa ga saman fuskarta......wani irin bugawa gabansa yyi da karfi ya qurawa fuskar bimbii idanu, tabbas shidai yasan bazai ta6a mance wannan fuskar ba cikin rayuwarsa, fuskar da kullum take masa gixo ba dare babu rana, mamaki yyi mutuqa na ganin ciki a jikinta, juyawa yyi ya kalli nurse din dake gefensa ya nuna cikin dake jikin bimbii yace" meye wannan a jikinta" nurse din kallonsa tayi cike da mamaki sai kuma ta kalli cikin bimbii dayake nunawa da hannu tace" tana da ciki ne doctorn" cikin tsantsar rudewa yace" what!" nurse din sai abun ya soma bata tsoro ta soma kallon Dr.maheer da tarin mamakin wannan action din nasa, yace" waye ya kawota" tace" wadanda suka kawota suna waje" juyawa yyi da sauri ya fita yana fita farhan yyi saurin shan gabansa yace" yy jikin nata" tsayawa yyi yana qarewa farhan kallo tun daga sama har qasa sannan yace" kaine ka kawota?" cikin sauri yace" ehh, nine" Dr.maheer yace" kai waye nata?" kai tsaye yace" mata ta ce" wani irin kallo maheer ya masa sai kuma ya juyar dakai yana wani irin murmushi mai ciwo, cike da axama ya juya ya chakumi kwalar rigar farhan da idanunsa da suka kala sukayi jazir, ummu farhan da abeed dake gefensu sukayi saurin qarasowa wurin suna mamakin abunda ya hada Dr.maheer da farhan, maheer da idanunsa suka juye sbd tsantsar bala'en kishi ya kalli kwayar idanun farhan yace" kasan wacce ita a wuri na kk fadamin wannan iskancin nk" farhan da idanunsa suka firfito sbd tsaurin shaqar da maheer ya masa yace" kaima kasan wacce ita a wuri na" hknne yasa maheer yyi jifa dashi gefe daya, yace" wlh,wlh bazan kyaleka ba saika fuskanci hukunci" wucewa yyi a mugun fusace ya wuce office dinsa yasa key, nurses din dake tsatstsaye da sauran ma'aikatan asibitin kowa ya cika da mamakin wannan abu, Dr.maheer kuwa kifa kansa yyi kawai a saman table din dake gabansa ya fashe da kuka tamkar wani qaramin yaro, meyesa bimbii tayi masa hk, meyesa bimbii ta bawa waninsa dama har ya ratsa gonar da ba tashi ba, shikam ko a ido ya raina shekarun farhan amma wai wannan danyen yaron bimbii ta baiwa kanta yyi mata wannan danyen aiki, tsananin so tare da tsantsar qiyayyar bimbii su sukayi tarayya cikin zuciyarsa, shi kansa ya rasa wanne ne yafi rinjaye, miqewa yyi a hnkli ya dauki handkerchief dinsa ya goge hawayen fuskarsa sannan ya dauki farar rigarsa ta likitoci yasa ya bude office dinsa ya fita, dakin da bimbii take ya shiga ya tarar da nurses sun zagayeta don bleeding take sosai, suna ganin shigowarsa suka bashi wuri, kai tsaye ya soma gudanar da aikinsa akanta batare daya kuma kallon fuskarta ba, cikin izinin Allah ya samu nasarar tsaida jinin dake zuba sannan ya mata allurar bacci mai nauyi, yana gama aikinsa ya fito daga dakin ko kallon inda su farhan suke beyi ba saida abeed ya miqe da sauri yasha gabansa yace" kayi hkr abunda yaro na ya mk don Allah ka dubamin diyata dakyau" kallon mamaki maheer ya masa sai kuma yyi murmushi yace" ka ta6a ganin inda mutum yyi wasa da rayuwarshi?" dukkaninsu kallonsa sukayi don basu fuskanci me yake nufi da hk ba, be sake kallonsu ba ya koma office dinsa, farhan dogarewa yyi daidai bakin dakin da bimbii take har lkcin da nurse ta basu damar shiga su ganta, cikin sauri duk suka miqe suka shige dakin, samunta sukayi tana bacci, farhan ya zauna gefenta yana kallon fuskarta yana hararar cikin dake jikinta don gani yake duk wannan cikin ne ke wahal da ita,ummu farhan riqo hannun bimbii tayi tana mata addu'ar samun lfy, ranar Dr.maheer a asibiti ya kwana ya kasa tfy gida, bini bini ze leqa dakin da bimbii ke kwance, idanunsa kuwa sunyi jajir sbd kukan daya sha, kishi ne kawai ke wahal dashi mutuqar ya bude idanu yaga bimbii dauke da jikin waninsa sai zuciyarsa tayi daci,6angaren masarautar burham kuwa har yanzu sarki abdallah bin jabal na nan kan bakansa, wannan abu dake faruwa shine ya bawa prince nasaar damar samun shiga sosai wurin sarki abdallah, prince nasaar ya samu cikakken iko da fada aji cikin wannan masarauta ta burham, hkn shine ya bashi damar fito da abunda ya jima a qasan ruhinsa wato daukar fansa kan sarki abdallah bin jabal, prince nasaar da ne ga sarki hamxa mai sarautar birnin al' bait, sarki abdallah bin jabal shine silar rusa wannan kyakykawan birni ya dawo dashi qarqashin mulkinsa, qarfi da shahara da masarautar burham ke dashi idanun duniya yasa batare da wani jayayya ba sarki hamxa ya miqa wuya ga sarki abdallah bin jabal inda birninsa ya dawo qarqashin inuwar masarautar burham, sarki abdallah dakansa ya nemi sarki hamxa ya bashi riqon prince nasaar tun yana qarami sbd yana son masarautarsa ta qulla zumunta ta musamman da masarautar al'bait, wannan shahara da daukaka da masarautar burham ta samu ya mugun tsolewa masarautu da dama idanu burinsu su durqusar da wannan izzah ta sarki abdallah bin jabal, prince nasaar babban burinsa shine masarautar burham ta dawo qarqashin izzah da sarautar birnin mahaifinsa, wannan kudiri nasa yasa shi cigaba son cigaba da kasancewa cikin wannan masarauta yana aikawa da sirrin wannan masarauta birnin al'bait saidai har wayau masarautarsu batayi tsayin da zata iya hada kafada da masarautar burham ba, prince akbar ya kasance babbar garkuwa ga wannan masarauta ta burham sbd tsantsar jarimtarsa hadi da sharp intelligency nasa, rufe prince akbar da sarki abdallah yyi ya baiwa tarin maqiyansa na ruguza masarautar burham ne batare daya fahimci hkn ba,prince nasaar ya samu yarda da amincewar sarki abdallah sosai, prince akbar yasa bimbii cikin qalbinsa, zuciya da gangar jikinsa bimbii suke buqata, yau tsawon watanni hudu kenan yana rufe amma bimbii bata ta6a 6acewa cikin tunaninsa ba,yau da dare yana zaune ya kalmashe kafafunsa ya jingina da jikin qarfen kurkun, idanunsa a lumshe suke yana tuna duk wani kyakykyawan memory nasa da bimbii,muryar mahaifiyarsa yaji tana masa mgn tace" ina son kayi yadda mahaifinka keso ka mance da wannan baiwar, cikin jikinta ba nk bane daman ai, ka furta hkn gaban kowa, mahaifinka yana yin hkne duk don ya kare muhibba da daraja na wannan masarauta, ina son ka bashi hadin kai" shiru prince akbar yyi sai kuma ya bude idanunsa ya kalli mahaifiyarsa dake hawaye tana kallonsa yace" ranki ya dade idan har na furta hkn nayi qarya, cikin dake jikin wannan baiwa nawa ne bana wani bane sbd me zan qaryata hkn,kar ki damu dani ko halin da nk ciki a yanzu koda na fita daga nan ba lalle rayuwa tayi tsawo ba nima, nafi son nima na tafi na bar wannan duniya mai cike da rudani" kuka sosai sarauniya take tace" kafi fifita soyayyar mace fiye da soyayyar mahaifiyarka yarima" kallonta yyi sosai yace" soyayyarki ta daban ce cikin ruhina baki da mahadi nan duniya ranki ya dade" murmushi tayi hade da kuka a hade ta zauna dakanta take bashi abinci a baki cike da qauna,hmmm,uwa uwace Allah kabarmu da iyayenmu ka bamu ikon faranta musu, soyayyar uwa soyayya ce da babu alqus so ne na haqiqatan, idan mutanen duniya dukka sun gujeka uwarka tana nan tare dakai.............
Chapter 36 · 0% Book details